08/11/2025
🚨🗞️ El País | Tasirin wariyar launin fata ga Lamine da ahalinsa!
Makusantan Lamine sun ce matashin yana ɗaukar zagin da mutane ke masa da sanyi, Kamar basu dame shi ba sosai — Wani lokacin ma har yana yin barkwanci da su don rage nauyin abin. Amma ahalinsa sukan fi shi shiga damuwa akan hakan, Musamman bayan kalaman da Mono Burgos ya faɗa a TV kai tsaye, Inda ya ce:
> “Idan bai yi nasara a ƙwallon ƙafa ba, Zai ƙare rayuwarsa yana bara akan titi.”
Wannan magana ta taɓa mahaifinsa sosai yaji zafinta — Har saida ya yi kuka ya kuma kira shugaban kulob ɗin Joan Laporta, Yana neman a fito da wata matsaya kan hakan. Mahaifiyarsa kuwa itama ta nemi a yi magana a fili don kare ɗansu.
Daga baya, Lamine ya ce:
> “Ina ganin yana son ya yaba min ne, Amma bai iya faɗa da kyau ba.”