HausaLink Media

HausaLink Media

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from HausaLink Media, Abuja Nigeria, Abuja.

29/04/2026

Ƙasar China ta miƙawa ƙungiyar ECOWAS sabuwar shalkwatar da ta gina a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da adadin kuɗi sama da dala miliyan 56.5.

29/04/2026

Hikimar Iran Cikin bakinta da Amurka da Isra'ila

29/04/2026

A Najeriya, jami’an tsaro sun hana manema labarai shiga ɗakin shari’ar mutanen da ake zargi da juyin mulki, shari’ar da ke gudana a babbar kotun ƙasar da ke Abuja, hanin da jami’an s**a ce umarni ne daga alƙalin da ke sauraron shari’ar.

Akwai Alamun Gaskiya kuwa?

28/04/2026

Amurka ta ce Iran ta gabatar mata da wani sabon shiri dangane da tsare-tsaren sake buɗe mashigin Hormuz, tare da kawo ƙarshen yaƙin dake tsakaninsu da kuma lamuran da s**a shafi ɗage tattaunawar makamin nukiliya zuwa wani lokaci.

28/04/2026

Wasu majiyoyi daga gwamnatin Amurka sun ce shugaban ƙasar Donald Trump ya fusata matuƙa da sabon tayin da Iran ta gabatar a ƙoƙarin warware rikicin ɓangarorin biyu wanda ƙasashe da dama ke shiga tsakani don sulhuntawa, a wani yanayi da har kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan lokacin da ɓangarorin biyu zasu ci gaba da tattaunawarsu a Islamabad.

28/04/2026

🔊 'Suna gudu ne a kan wani dandali na ƙoƙarin warkar da rarrabuwar kawuna a cikin Isra'ila, suna ƙoƙarin warkar da ƙasa mai rauni bayan 7 ga Oktoba.' A cikin shirin Reuters World News na yau - tsoffin firayim ministan Isra'ila biyu

28/04/2026

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce Amurka ta ji kunya a yakin da take yi da Iran, yana mai gargadin cewa borin kunya ya hana Washington janyewa daga yaƙin, yayin da Tehran ke samun gabalaba.

28/04/2026

An yi baje kolin wasu sabbin mak**ai da manhajar tattara bayanin sirri a Najeriya

Mak**ai da na’urorin da aka baje kolinsu a ranar Litinin 27 ga watan Afirilu da muke ciki waɗanda Kamfanin tsaro a Najeriya mai suna Terra Industries s**a samar sun haɗa da mak**ai masu sarrafa kansu da na’urorin gano ababen fashewa da manhajar tattara bayanan sirri.

Shin kunaga hakan zai karfafa tsaro a Najeriya?

21/04/2026

Bayan shafe kwanaki 129 a tsare, an wanke Sheikh Sani Khalifa Zariya ranar 20 ga wata daga zargin juyin mulki da aka dora masa. Sai dai abin mamaki, kasa da sa’o’i 24, yau 21 ga wata an sake k**a shi da sabon salon wai sunansa yana cikin wasu mutane 7 da ake zargi.

Tambayoyina Ga Gwamnati

Wace sabuwar shaida aka samu a cikin kasa da sa'o'i 24 da ta soke hukuncin wanke shi da aka yi jiya?

Shin sake k**a mutum nan take bayan an wanke shi ba zagon kasa ba ne ga mutuncin tsarin shari'ar Najeriya?

Idan har zargin juyin mulki ne, me ya sa aka kasa gabatar da gamsassun shaidu tun farko har aka kai ga sallamarsa?

Shin an yi la'akari da shekarun Sheikh da kuma yanayin lafiyarsa kafin a fara wannan wasan k**a sakin?

Tambayoyina Ga Al'ummar kasa

Idan aka bari ana cin mutuncin malamanmu da dattawanmu ba tare da bin ka'ida ba, wa kuke tunanin shi ne na gaba?

Shin mun gamsu cewa wannan tuhuma ta gaskiya ce, ko kuwa wata makirci ce ta rage karfin fada aji na wasu mutane a cikin al'umma?

Shin yaushe ne za mu hada kai don tabbatar da cewa ba a amfani da doka wajen kuntata wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba?

Adalci shi ne ginshikin zaman lafiya. Idan har Sheikh Sani Khalifa bashi da laifi k**ar yadda aka bayyana a jiya, to sake k**a shi tamkar kiran fitina ne da rashin amincewa da tsarin doka. Sharri ba ya taba dorewa a kan gaskiya.

Allah ya tabbatar da adalci, ya kuma kare na kwarai daga sharrin masu sharri.

Kuyi sharing wannan saƙon zuwa kowane lungu da saƙo domin ya isa ga waɗanda ya k**ata ya taras🙏🏻

21/04/2026

Ga Dukkan Alamu Jamhuriyar Musulunci Ta Juyin juya halin Iran Ta Zama Kadan garen bakin Tulu.

Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran har sai sun kammala tattaunawa.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da yarjejeniyar dakatar da yaki ta makwanni biyu da bangarorin s**a cimma ke dab da kawo karshe.

21/04/2026

Aƙalla dakarun Sojin Chadi 400 sun isa Haiti don aikin samar da tsaro a ƙasar ta kudancin Amurka ƙarƙashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar ɗinkin duniya, wanda ke matsayin wani ɓangare na dakaru dubu 1 da 500 da ƙasar ta alƙawarta bayarwa.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address


Abuja Nigeria
Abuja