Gaskiyar Zance

Gaskiyar Zance

Share

Gaskiya itace tushen cin nasara

28/11/2025

Unguwannin kano da Sana,o,in su
1 Fagge - Dinki
2 Ɗorayi - waƙa
3 Brigade - make-make
4 Jakara - Gurasa
5 Goron Dutse- Furniture
6 Kurna - ƙwallo
7 Rijiyar lemo - garuwa
8 Rijiyar Zaki - gwanjo
9 Hotoro - dillanci
10 Yakasai - shadda atamfa yadi
12 Gadon qaya - kayan masarufi
13 Kofar mata -Dako
14 Tsamiyar Boka- Harkar siyarda waya
15 Yan Kaba- Gwari (Kayan Miya)
16 sharada - Kanikanci
17 Marmara -Faskare
18 Kabuga - Cima zaune
19 Unguwa Uku - black Market (bimburutu)
20 Kofar Mazugal - wankin mota
21 Dan Agundi - Malaman makaranta
22 Shagari Quarters - Aikin gwamnati
23 Bacirawa - gwangwan
24 Zoo Road - Daukar hoto (Photography)
25 Sani Mai Nagge Buge-buge
26 Gwale - miyagun Kwayoyi
28 Unguwar Rimi - Kame-kame
29 Chiranchi - Gyaran waya
30 Gayawa - Sana,ar Gini
31 Rimin kebe -adaidaita sahu
32 Jan bulo -sh**ha
33 Sheka - Sa ido
34 Jaen -wanki da guga
32 Gwammaja - ?

24/09/2025
24/09/2025

Kuna son Tinubu ya zarce ko dai ya yi wa'adi daya ya huta?

A Najeriya, Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta maida martani ga Fadar Shugaban Kasa dangane da ikirarin da ta yi cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da niyyar tsawaita wa’adin mulkinsa bayan shekarar 2031.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC, ta bayyana wannan ikirari a matsayin mai cike da girman kai da rashin bin ka’idojin dimokuraɗiyya. Jam’iyyar ta jaddada cewa wa’adin Shugaba Tinubu zai ƙare a shekarar 2027, kuma ta bayyana cikakken tabbacin cewa 'yan Najeriya ba za su yarda a ƙara masa ko da kwana ɗaya ba.

24/09/2025

An gudanar da shari’ar ne a karkashin jagorancin Birgediya Janar Ugochukwu Unachukwu a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.

Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, shugaban kotun sojin ne ya bayyana hukuncin daurin Rai-da-rai ga Raphael Ameh, Ejiga Musa, da kuma Patrick Ocheje, biyo bayan samunsu da laifin aikata zargin da aka yi musu.

23/09/2025

Wani yaro dan shekara 13 daga Kunduz a kasar Afganistan ya makale a tayar wani jirgin sama zuwa birnin Delhi na kasar Indiya, a ranar Lahadi, 21 ga Satumba, 2025.. Jami'ai sunce ya tsira da ransa a matsayin "abin al'ajabi" saboda tsananin hatsarin da ya jefa kansa.

Bayan da jirgin ya sauka a filin jirgin saman Indira Gandhi International (IGI), ma'aikatan jirgin sun same shi yana tafiya a kusa da tayar jirgin.

An bayar da rahoton cewa yaron ya gaya wa hukumomi cewa ya yi hakan ne da sani sa" kuma yana tunanin jirgin zai je Iran ne.

Hadarin da yaron ya tsallake yana da wuyar gaske. Masana sun ba da misalin adadin mace-mace sama da kashi 75 bisa 100 a irin wannan yunƙurin. A lokacin tafiya mai tsayi ƙafa 30,000 zuwa 40,000 daga ƙasa samun iskar oxygen yana da wahalar gaske wanda ke haifar da mutuwa.

Wannan labarin sun buga suma sun buga

Don neman karin bayani rubuta . Here's why, and how, akan shafin Google. ✍️

23/09/2025
23/09/2025

Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar Ɗangote.

23/09/2025

Ƴansanda sun jefa wa magoya bayan Natasha barkono mai sa hawaye

NatashaAsalin hoton,others
Ƴansanda sun tarwatsa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, waɗanda s**a raka ta zuwa Majalisar Dattawa daga babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda s**a watsa musu barkono ma isa hawaye domin tarwatsa su.

Magoya bayan sun yi tattaki ne domin raka sanatar zuwa majalisar domin komawa bakin aikinta.

Tun da farko, majalisar ta buɗe ofishin sanatar da ke cikin ginin Majalisar ta Dattawa.

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa Majalisar Dattawa mako guda da ya wuce domin sanar da niyyarta ta komawa aiki bayan dakatarwa na tsawon wata shida, amma majalisar ta ce ta ɗan jira tukuna.

A watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawa tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da Sanata Natasha al'amarin dai ya kai ga har Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da ita daga zauren majalisar lamarin da ya kai ga dakatar da ita na tsawon wata shida.

23/09/2025

Assalam alaikum, muna muku barka da zuwa wannan gida mai Albarka.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Mark Okoye Cl, Asokoro, Aso 900110, Federal Capital Territory, Nigeria
Abuja