Doctor zulaihart room
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Doctor zulaihart room, Chiromawa garin-malam, Kano.
20/05/2026
CIWON MARA LOKACIN AL'ADA.
Ciwon mara yana faruwa ne sbd mahaifa tana matsewa domin fitar da jinin Al'ada wanda hakan ne yake jawo ciwon mara.
Ciwon al’ada shi ne zafin da mace ke ji a ƙasan ciki, bayanta ko cinyoyinta yayin da jinin al’ada ke zuwa. Wasu matan zafin yana zama kaɗan, amma ga wasu kuma yana iya zama mai tsanani har ya hana su yin ayyukansu na yau da kullum.
Me yake kawo shi?
Yawanci ciwon al’ada yana faruwa ne saboda mahaifa tana matsewa domin fitar da jinin al’ada. A lokacin, jiki yana sakin wasu sinadarai (prostaglandins) da ke ƙara tsokanar zafi.
Haka kuma, abubuwa kamar:
A) rashin motsa jiki,
B) damuwa (stress),
C) sanyi,
D) ko wasu matsaloli a mahaifa (kamar E) infection ko fibroid)
na iya ƙara tsananta ciwon.
ME YAKAMATA MACE TAYI DOMIN RAGE TSAFIN?
1. Ki dinga shan ruwan zafi ko shayi mai dumi.
2. Ki saka abu mai dumi a ƙasan ciki (hot water bottle).
3. Kihuta sosai, ta guji gajiya.
4. Motsa jiki mai sauƙi kamar tafiya ko -- shimfiɗa jiki yana taimakawa.
5. Cin abinci mai gina jiki, musamman kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa.
Idan zafin ya yi yawa, ana iya amfani da maganin rage zafi da likita ya amince da shi.
⚠️Idan ciwon al’ada ya wuce kima, ko yana zuwa da zubar jini mai yawa, to yana da kyau mace ta ga likita domin a bincika lafiyarta.
Allah Yasa mudace
Doctor zulaihart room 👈
20/05/2026
Kula da lafiya yafi kula da kudi akiyaye 👌
Doctor zulaihart room
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Website
Address
Chiromawa Garin-malam
Kano