28/08/2026
🔥⚽ FUNTUA, KUN SHIRYA?! ⚽🔥
Lokaci ya yi! FUFCO PREMIER LEAGUE 2026/2027 na dab da komawa filin wasa! 🏆🔥
Sabuwar kakar, sabbin buri, sabbin jarumai! 💪⚽
Kowanne wasa na da labarinsa, kowacce ƙwallo na da farin cikinta, kuma kowanne maki na da muhimmanci!
🔥 Waye zai Zama sarki? Wa zai ɗaga kofin? Wa zai zama zakaran FUFCO Premier League? 🏆👑
🎙️ Mintuna 90 na ƙwallo… amma abubuwan tunawa ba su ƙarewa!
✍️ Sketch
20/08/2026
💰🔥✍️Fatan Alheri GA Adamu Vardy
Yanzu haka Adamu Vardy yana gudanar da gwajin lafiya (medical) a wani babban kulob na Jandarmomin Nijar. ⚽🔥
Wannan wata babbar dama ce a tafiyar sa ta ƙwallon ƙafa!
Muna masa fatan nasara a gwajin lafiyar, kammala komai lafiya, da samun kyakkyawan sabon babi a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Allah Ya bude masa ƙofofin nasara, Ya kuma sa wannan dama ta zama matakin samun manyan nasarori.
Adamu Vardy! 🇳🇬🇳🇪⚽💪
✍️ Sketch
14/08/2026
🔥🏆 YAU NE BABBAR RANA! 🏆🔥
Filin Aya zai dauki zafi yayin da Funtua Pillars FC da Tiger Boys Academy za su kara a wasan ƙarshe na Tukur Tama Charity Competition!
⚽ Pillars ko Tiger Boys — wa zai lashe kofin?
🔥 Kowa ya shirya, 'yan wasa sun shirya, magoya baya sun shirya!
13/08/2026
🔥⚽ Once again, the talented footballer from Funtua, Abba amfani, has made us proud by scoring an incredible 5 goals in the Malumfashi Premier League! 👏🏽🔥
What are your best wishes for Abba amfani as he continues his football journey?
🙏🏽⚽🏆 May he keep shining and achieving greater success! 🌟💪🏽
04/08/2026
FAGEN WASA KWAKWALWA 🙄
Shin waye Zan Fadi mana wace kungiya ce wannan kuma a wace shekara ne aka yi yanzzu wannan hoton
03/08/2026
FULL TIME ⚽ WASAN SADA ZUMUNTA
⚽ Funtua Sharks 1️⃣ 🆚 1️⃣ Katsina United
An busa kararrawar karshe! Kowa ya yi iya kokarinsa, amma wasan ya kare da kunnen doki — ƙwallo ɗaya da ɗaya!
🔥 Funtua Sharks sun nuna jarumta da ƙwazo, haka ma Katsina United sun tabbatar da ƙwarewarsu. Masoya ƙwallon ƙafa sun sha kallo mai daɗi daga farkon wasa har zuwa ƙarshe.
👏 Allah ya ƙara haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin biyu, kuma muna godiya ga ɗaukacin magoya baya da s**a cika filin wasa domin ƙarfafa gwiwar 'yan wasan.
✍️ Sketch
03/08/2026
🎙️🔥 RANAR WASA 🔥🎙️
Masoya ƙwallon ƙafa, lokaci ya yi! Yau ne ranar da za a gwabza wasan sada zumunci mai cike da armashi tsakanin manyan ƙungiyoyi biyu.
⚽ Funtua Sharks FC 🆚 Katsina United FC ⚽
Yau ba kalar wasan yau da kullum ba ne! Rana ce ta nuna ƙwazo, jajircewa da neman nasara. Funtua sharks za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin faranta ran magoya bayanta.
🕑 Lokaci: Karfe 12:30 na rana due to security issue
📍 Wuri: Filin Wasan Funtua Stadium
📅 Rana: Monday, 3 ga Agusta, 2026
Ku fito da ɗumbin yawa domin mara wa ƙungiyarku baya. Ku zo mu cika filin wasa da sowa, tafi da ƙarar goyon baya!
Allah Yasa ayi wasa lafiya a tashi lafiya
✍️ Sketch
01/08/2026
🔥WASAN SADA ZUMUNCI 🔥
🎙️⚽ Ku zo ku shaida wasan da zai ɗauki hankali!
Ba kowace rana ake samun irin wannan haɗuwa ba.
Funtua Sharks 🆚 Katsina United
'Yan kallo, ku cika filin wasa! Mu nuna cewa Funtua gida ce ta ƙwallon ƙafa!
Kar a bari a ba ka labari... ka zo ka shaida da idonka! 🔥⚽💚💛
✍️ Sketch