26/09/2026
🚨BUGUN FENARITI YA MAMAYE ZAGAYEN 32, WASANNI BIYAR SUN KARE DA KUNNE-DOKI🤝🔥
Gasar Maiden Edition of Hon Tukur Yusuf Daddy Football Competition 2026 ta ci gaba da daukar hankalin masoya kwallon kafa, yayin da wasannin Round of 32 ke kara shiga wani yanayi mai tsananin zafi da fafatawa.
A cikin wasanni takwas da aka buga daga ranar 24 zuwa 26 ga Satumba, wasanni biyar sun kare ne da kunnen doki kafin a yanke hukunci ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida. 🔥
Wannan alkaluma na nuna irin yadda kungiyoyin s**a yi kunnen doki da juna, inda babu wata kungiya da ta shirya bai wa abokiyar karawarta damar samun tikitin zuwa zagaye na gaba cikin sauki.
Sakamakon wasanni yau
Super Star 2–2 Dourtmound Makera
An buɗe wasannin ranar ne da fafatawa mai cike da ɗaukar hankali tsakanin Super Star da Dourtmound Makera.
Ƙungiyoyin biyu sun fafata tsawon mintuna 90, amma kowannensu ya zura ƙwallaye biyu, lamarin da ya sa aka tashi 2–2.
Daga nan aka koma bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Dourtmound Makera ta yi nasara da ci 5–4, ta samu tikitin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.
Sai Kuma Golden Star T/Wada 1–2 Dourtmound
Dourtmound ta samu babbar nasara a kan Golden Star T/Wada, bayan da ta yi nasarar zura ƙwallaye biyu, yayin da Golden Star T/Wada ta samu guda ɗaya.
Daga ƙarshe Dourtmound ta yi nasara da 2–1, ta samu damar ci gaba da fafatawa a gasar.
Jabiri United 1–1 Majesty NaBukka
Wannan ma ya kasance wasa mai matuƙar zafi, inda Jabiri United da Majesty NaBukka s**a yi kunnen-doki da ci 1–1.
Bayan kasa samun wanda zai raba gardama cikin mintuna 90, aka koma bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A nan ne Jabiri United ta yi nasara da ci 4–3, inda ta samu tikitin zuwa zagaye na gaba.
Liverpool FC 0–0 Real Academy
A wasan ƙarshe na yau, Liverpool FC da Real Academy sun fafata a wasa mai tsauri, amma babu ɗaya daga cikin ƙungiyoyin biyu da ta samu damar zura ƙwallo.
An tashi 0–0, kafin a koma bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A ƙarshe, Real Academy ta yi nasara da ci 4–2, inda ta samu tikitin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.
Mr Sky ✍️