30/08/2026
HASSAN MAGAJI YA KARA KAFA SABON TARIHI A BICA
Shugaban kungiyar Bica Alh. Hassan magaji ya gabatar da Sabon Kofi ga sauran Shugabannin kungiyar
Hakan na zuwa ne a cikin fara shirye shiryen fara gasar Bica premier leagues 2026-2027
Wannan Cup shine irin sa na farko wadda kungiyar ta taba gabatar wa a tarihin kungiyar
Hakika Hassan magaji ya yi fice wajen Sanarwa Tareda kawowa wannan kungiya cigaba ta fannoni daban daban
Muna Maka Fatan Alkhari, Allah ya karawa rayuwa Albarka