SALLAR ASUBAH
Sallar Asubah haske ne ga ma'abota yin ta a kan lokaci masu fita a cikin duhu domin halartar sallarta, hakanan kuma bushara ce kamar yadda yazo a hadith.
Burayd Al-aslamy (RA) Ya ruwaito daga Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ka yi albishir da cikakken haske ranar al-ƙiyamah ga masu fita zuwa masallaci domin sallar Asubah a cikin duhu.” [Abu-dawud da Tirmidhi s**a ruwaito, Albany ya inganta shi]
Wannan albishir ce ga masu sallar Asubah cikin jam'i masu halartar masallaci a cikin duhun asubah, duk wanda kuma yake son shiga cikin wannan bushara da Manzon ALLAH (ﷺ) yayi to sai ya jajirce wajen yin sallar Asubah a kan lokaci tare da halartar masallaci domin yin sallar acikin jam'i.
Allah bamu ikon kiyayewa
Sabiu Alhassan Maigado
Struggle for Justice
Idan ka barwa ALLAH zaɓi, toh ka roƙe shi mafi Alkhairi daga gare Shi, Idan ya kasance baka samu abunda kake buƙata ba, toh ka yarda da abunda ya kasance a gareka, Kuma ka godewa ALLAH Bisa Hakan...
Yaa Rabb Munbar Komai Gareka, Allah Ubangiji Ka Mana Zaɓi Mafi Alheri 🙏🙏🙏
Duk Mai Neman Arziki, Aure, Gida, Mota, Aikin Hajji, Umra, Makaranta, Haihuwa, Aiki.
Ya Allah Kabashi Alfarmar Annabi Muhammad❣️
Babu Gaggawa.
ASSALAMUALAIKUM,
ZANCE MAI CIKE DA HIKIMA..!
Idan ka shuka salak yau zaka girbe shi bayan sati uku, amma saidai ka cinye shi a ranar ko ya lalace.
Idan ka shuka shinkafa zaka girbeta bayan wata uku, kuma zaka iya ajiyeta har fiye da shekara biyu.
Idan ka shuka mangoro zaka fara tsinkarsa bayan shekara uku ne, amma duk shekara sai ka cika kwanduna ba tare da ka sake shukashi ba.
Idan ka shuka dabino, watakil ka tsinke shi bayan shekara goma sha uku. Amma hatta jikan ka sai ya tsinki ɗansa yaci, matukar ba sare shi akayi ba.
Ita duniya tana bukatar hangen nesa da hakuri, idan kayi shiri mai kyau kayi hakuri, Sai amfani mai dorewa yazo maka. Idan kayi mata gaggawa, Sai karamin amfani yazo maka.
Iya tsawon hakurin da Kayi, iya amfaninsa gareka, kuma hakane ake shiryawa ranar gobe kiyama.
Kayi Aiki, Kayi Hakuri, Kayi Addu'a!
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU DA YAN UWAN MU YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA. AMEEN
Muyi Zabe Cikin Lumana Mu zauna Lafiya da Junanmu Kar Siyasa Tasa Mu Tada Husuma a Tsakankaninmu, da Yan Uwanmu da Abokanmu.
Za6e dai Saura Kwana Bakwai (7)
Sabiu Alhassan P. A
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Address
Jigawa