25/07/2026
💣〽️‼️ 𝐒𝐀𝐁𝐎𝐍 𝐋𝐀𝐁𝐀𝐑𝐈: A cewar rahotanni, shugaban Real Madrid, Florentino Pérez, ya yanke shawarar cewa dole ne kulob ɗin ya yi babban saye a wannan bazarar.
📌 Burinsa na farko shi ne ya ɗauki Michael Olise, amma bayan ya fahimci cewa cinikin ba zai yiwu ba, sai ya karkata hankalinsa kan Yan Diomande.
🤝 An ce Juni Calafat ne ya taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan Yan Diomande ya zaɓi Real Madrid, duk da cewa an riga an shirya komawarsa zuwa Paris Saint-Germain.
16/07/2026
💣‼️ Cristiano Ronaldo: Ban buƙatan komai na rayuwa:
Allah yabani abin da ban taɓa tsammani ba, musamman tare da ƙungiyar ƙasa da matakin kaina.Shi ya sa nake son jin daɗin kowane lokaci. Ba zan zama mafi kyawun Cristiano ba idan na lashe World Cup, kuma ba zan zama ƙaramin Cristiano ba idan ban lashe shi ba.👍🏿🎖
Mk Abdul Futboll
14/07/2026
‼️🇲🇽 NISHADI: Magoya bayan Jude Bellingham suna ƙara yada jita-jita game da yiwuwar soyayya tsakanin Jude da Miss Universe na yanzu, yar Ƙasar Mexico Fátima Bosch. 🇬🇧❤️🇲🇽
Yawancin masu amfani da kafofin sada zumunta suna fatan ganin su a matsayin ma’aurata.
Fátima ta bada amsa da cewa:
🗣️Na ga yawancin post a Instagram inda mutane ke haɗa mu. Shi ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne mai ban mamaki, amma dole ne in san shi da kyau tukuna. Ina ganin Shine mafi muhimmanci,
shi mutum ne mai kyau da kuma kyawawan dabi’u.❤️
Mk Abdul Futboll
14/07/2026
✂️ A waje filin wasa, Cristiano Ronaldo Jr. yana koyon fasahar Aski!💇♂️
10/07/2026
💣 Jose Mourinho:
Na zo ne don taimakawa kowa ya zama mafi kyau. Ƙirƙirar al’adar aiki, alhaki, buri da kuma wani abu da na san shi da kyau, wato mutuncin aiki wa Real Madrid. Ina matuƙar son wannan ra’ayi. Ba aiki a Real Madrid ba ne, aiki NE GA Real Madrid.
Fara preseason ba tare da manyan yan wasa ba? Mu kalli al’amarin a hanya mai kyau, kuma dama ce ta sanin matasan yan wasa da zan yi aiki tare da su, suma za su sami dama su san ni.
A cikin kakar wasa, yawancin waɗannan matasan yan wasa za su kasance a cikin ƙungiyar Castilla.
Ina kuma son shiga ciki da taimakawa wajen haɓaka da bunkasa wannan sashin.
Muna aiki tuƙuru. Bawai a yau nazo ba. Mun kasance muna aiki tuƙuru na ɗan lokaci tare da tsarin kulob ɗin a matakai daban-daban. A yau za ka iya aiki ba tare da kasancewa a wurin ba saboda fasaha tana taimaka mana sosai, a yau ya kasance game da zuwa da duba duk abin da aka yi da abin da har yanzu ya rage mu yi.
Magana ba ta isa ba. Muna cikin aiki na musamman.
10/07/2026
‼️Ma’aikatan horon José Mourinho tare a Madrid yau:
🇩🇪 Sami Khedira: Mataimaki
🇵🇹 Pedro Machado: Mataimaki/Mai horon jiki
🇵🇹 João Tralhão: Mataimaki
🇵🇹 Nuno Santos: Mai horor da masu tsaron raga
🇮🇹 Roberto Merella: Mai nazari
🇵🇹 António Dias: Mai horon jiki
Real Madrid sun shirya wasanni huɗu na preseason. Duk huɗun za su kasance a Turai. Ƙungiyar za ta yi tafiya zuwa Austria a ranar 1 ga Agusta don wani wasa na sada zumunci.
ℹ️ diarioas / elchiringuitotv
Mk Abdul Futboll