Amran Farm And Poultry

Amran Farm And Poultry

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Amran Farm And Poultry, Kaduna.

Amran Farm And Poultry, The First Hausa Poultry Training Class in Nigeria That Teach And Highlight Poultry Farmers From Destruction, And Selling Good& Quality Day Old Birds From Different Companies

07/07/2024

Ku Fada Mana Matsalar Da Kuke Fuskanta Game Da Kiwon Kaji, Mu Kuma Zamuyi Muku Bayanin Yadda Zaku Warwareta Tare Da Baku Shawarar Yadda Zaku Kauce Mata A Nan Gaba.

Note: Zamu Fara Bayanin Kan Matsalar Da Muka Ga Anfi Korafi A Kanta.

Like Ande Share๐Ÿ™๐Ÿ™

13/12/2023

Yadda Zaka Kare Kajinka Daga Kamuwa Da Ciwon Sanyi Hunhu Wato Mura Mycoplasmosis(CRD)

Amran Farm And Poultry

Chronic Respiratory Disease Ko Kuma Mycoplasmosis Wata Cuta Ce Wato Murar Kaji Dake Darsuwa Da Sanyi Ko Dafa Wasu Kwayoyin Cuta Dake Cikin Iska.

Ita Dai Wannan Cuta Ta Murar Kaji Mai Tsanani (CRD) Cuta Ce Dake Samuwa Ga Kaji Tun Daga Gurin kyankyasa Da Kuma Iska Mai Dauke Cuta Ko Kuma Tsakanin Kaza Da Kaza Ko Sanyi.

Don Haka Ita Murar Kaji Tana K**a Kaji Ne Tun Suna Kananan Kuma Matukar Mai Kiwo Bai Dauki Mataki Da Sauri Ba Na Iya Haifar Masa Da Asara Na Mutuwar Kajin,

Ya Za'a Kaji Sun Fara Kamuwa Da Murar Nufashi Mai Tsanani?

1) Tari
2)Atshawa
3)Numfashi Da Kyar
4)Yoyon Baki
5)Rufa
6) Kashi Mai Ruwa
Da Zarar Ka Fara Ganin Daya Daga Cikin Wadan Alamomi Kayi Maza Ka Fara Daukan Matakin Kariya Tun Kafin Abun Yayi Karfi.

Yadda zaka Kare Kajin Daga Wannan Cuta Ta Murar Numfashi:

1)Ka Tabbatar Da Ka Siyo Kaji Daga Gurin Da Kake Dabbacin Suna Kaji Mai Kyau
2) Ka Samar Da Cikakkiyar Kulawa Ga Kaji A Kwanaki Sha Hudun Farko (Good Brooding)
3) Ka Kiyaye Amfani Da Kowani Magani Idan Kajinka Sunan Kanana
4) Tsfta
5) Kada Ka Hada Kajin Kwai Dan Nama Ko Kuma Kanana Da Manya Guri Guda

Yadda Zaka Magance Murar Da Zarar Anji Alamunta:

Da Zarar Anji Alamar Daya Daga Cikin Alamominta Toh Ayi Maza Anemo Maganin Mura Mai Dauke Da Sinadarin Tylan Ko kuma Gallimycin.

Domin Neman Shawara Game Da Kiwon Kaji Ko Siyan Kaji Zaku Iya Tuntubarmu A 07033951040.

Don Allah A Dunga Share๐Ÿ™

20/03/2022

"Mun Bude WhatsApp Group Game Da Yadda Ake Kiwon Kaji Kula Dasu Magance Cututtukan, Rigafi Da Dai Sauransu

Ga Masu Bukatar Shiga Naira 1000 Kacal Sai ku Tuntubemu Ta Wannan Number 07033951040 ko Kuyi Mana Magana Ta WhatsApp

20/03/2022

"Ku Fada Mana Matsalolin Da Kuke Fuskanta Game Da Kiwon Kaji Adaidai Wannan Lokacin"

Photos from Amran Farm And Poultry's post 28/11/2021
16/01/2021

"Ko Kuna Son Sanin Yadda Zakuyi Amfani Da Magungunan Mutane A Kiwon Kaji ?

16/01/2021

"Tsaftace Ruwan Sha Da Wanke Mazubin Ruwa A Kowace Rana Na Taimakawa Da Kashi 90% Gurin Bawa Kaji Kariya Daga Kamuwa Daga Cututtuka Masu Yaduwa"

Shere It ๐Ÿ™๐Ÿ™

Photos from Amran Farm And Poultry's post 26/12/2020

Ku Fada Mana Matsalar Da Kuke Fuskanta Game Da Kiwon Kaji, Mu Kuma Zamuyi Muku Bayanin Yadda Zaku Warwareta Tare Da Baku Shawarar Yadda Zaku Kauce Mata A Nan Gaba.

Note: Zamu Fara Bayanin Kan Matsalar Da Muka Ga Anfi Korafi A Kanta.

Like Ande Share๐Ÿ™๐Ÿ™

Photos from Amran Farm And Poultry's post 24/12/2020

Muhimmanci Ruwa Da Kuma Nagartatcen Abinci Ga Kaji.

Bayan Tsafta Da Kuma Samun Kaji Daga Makyankyasa Mai Kyau Da Kuma Inganci (Good Hatcherie) Abu Mai Muhimmanci Shine Yadda Za'a Kula Da Ruwan "Sha Da Abinci Kajin.

Kaji Na Bukatar Tsaftatatcen Ruwa Da Kuma Ingantatcen Abinci A Tun Ranar Farko Har Izuwa Ranar Ciresu, Hakan Shi Zai Basu Karfin Gwaiwa Gurin Girma Tare Da Samun Walwala Da Kuma Koshin Lafiya,

Don Haka Wajibi Ne Ga Duk Wani Dake Kiwon Kaji Yayi Matukar Taka Tsantsan Gurin Kula Da Wadan Nan Muhimman Abu Guda Biyu Wato Ruwa Da Kuma Abinci.

โ€ข Yadda Za'a Ciyar Da Kaji Tun Ranar Farko Da Ka kawosu Gona Ko Inda Za'a Kiwatasu
โ€ข Tunda Daga Ranar Farko Har Zuwa Kwanaki Goma Sha Hudu Anaso A Ciyar Da Kaji Abinci Mai Inganci Dake Dauke Da Protein A Kalla 18-22% Sannan A Cigaba Da Basu Wanda 18% Har Su Girma ( Amma Idan Masu Kwai Ne Za'a Cigaba Da Basu Protein 16% Ne)
โ€ข Kada A Bari Abinci Yana Yankewa Domin Hakan Na Haifar Da Asara Da Kuma Takure Kajin Gurin Rashin Girma Da Wuri
โ€ข Sanya Wadtatcen Gurin Zuba Abinci (Feeder) A Ko Ina Domin Bawa Kowani Dan Kaza Damar Cin Abincin, Saboda Idan Wasu Basu Samun Damar Cin Abinci Zai Kasance Basu Girma K**ar Masu Cin Abinci Akoda Yaushe Wanda Hakan Ke Haifar Da Nau'i Biyu A Cikin Kaji Kanana Da Kuma Manya
โ€ข Sanya Ido A Tabbatar Da Kowni Dan Kaza Nacin Abinci Idan An Lura Wani Baya Ci A Ko Rashin Lafiya Na Damunshi A Cireshi Cikin Masu Lafiya.

Ruwa Sha:

Ya Kasance A Koda Yaushe An Samar Da Ruwa Tsaftatace Ga Kaji

Kullum A Wannke Abunda Ake Zuba Musu Ruwa Domin Kashi 75% Na Cututtukan Dake K**a Kaji Suna Sha Ne A Ruwa Don Haka Wajibi A Wanke Abun Zuba Musu Ruwa A Kullum.

Rashin Samar Da Wadatatcen Ruwa Yana Haifar Da Iloli Ciki Kuwa Har Mutuwar Kaji Na Babu Zato Babu Tsammani.

Don Haka Yana Da Matukar Muhimmanci A Kiyaye Waddan Nan Abubu Wato Ruwa Da Kuma Abinci Don Kaucewa Asara Da Kuma Habbaka Riba.
Ga Mai Bukatar Karin Bayani Kan Wani Abu Daya Shige Duhu Game Da Kiwon Kaji Saiya Tuntubi 07033951040

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kaduna