Dandalin kwallo

Call Website Contact the business

Dandalin kwallo “⚽ Labaran Kwallo na Gaskiya + Zafafan Ra’ayoyi 🔥
📊 Real Madrid | Arsenal | EPL |fc Barcelona
👉 Follow don kada ka rasa updates!”

🚨📰 Sababbin labarai: Lamine Yamal, Raphinha, Argentina da Cristiano Ronaldo ⚽🔥🔥 Lamine Yamal ya mayar da martani ga masu...
30/09/2026

🚨📰 Sababbin labarai: Lamine Yamal, Raphinha, Argentina da Cristiano Ronaldo ⚽🔥

🔥 Lamine Yamal ya mayar da martani ga masu s**ar sa:

Ya ce “Wata ɗaya da ta wuce kuna cewa bana taka leda yadda ya kamata. Yanzu hankalina kwance yake, ina jin daɗin wasan. Na san cewa ko yaushe za ku iya sake dawowa da irin wannan maganar.”

🎙️ Anthony Gordon, bayan an tambaye shi kan Ballon d’Or:
“Abu ne mai wahala, amma a ganina Lamine Yamal ne mafi kyawun ɗan wasa a duniya.”

🗣️ Fermín López:
“A ganina, Lamine Yamal ya cancanci lashe Ballon d’Or.”

🗣️ Nico Williams:
“Ina fatan Lamine Yamal zai lashe Ballon d’Or a bana. Idan kana fahimtar ƙwallon ƙafa kuma kana jin daɗinta, za ka san cewa Lamine ne mafi kyau.”

🇦🇷 Lionel Scaloni ya tabbatar da sabbin shugabannin Argentina: Cuti Romero zai zama kyaftin, Dibu Martínez na biyu, sannan Lautaro Martínez na uku.

🇧🇷 Raphinha ba zai buga sauran wasan Brazil a wannan hutun wasannin ƙasashe ba. Gwajin da aka yi masa ya nuna ɗan kumburi a tsokar cinyarsa ta dama, amma matsalar ba mai tsanani ba ce, kuma an bar shi ya koma Barcelona domin kariya.

🇵🇹 A Portugal kuma, ana ci gaba da magana kan rashin jituwa tsakanin Cristiano Ronaldo da koci Jorge Jesus. Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ya je Copenhagen domin tattaunawa kan lamarin. Cristiano bai halarci atisayen ƙungiyar ba, amma rahotanni sun ce ya koma otal ne domin yin atisaye na musamman a ɗakin motsa jiki.

Dandalin kwallo

Yana da shekaru 19 da kwanaki 75, Lamine Yamal ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya zura kwallo a ragar kasar In...
26/09/2026

Yana da shekaru 19 da kwanaki 75, Lamine Yamal ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya zura kwallo a ragar kasar Ingila a wata gasa a Wembley a cikin shekaru 20 da s**a gabata.

Ƙwallon da ya ci bayan daƙiƙa 104 ita ce ƙwallon da ta fi kowacce ƙwallo sauri da ƙungiyar da ta ziyarci Wembley ta zura tun 1957.

Spain ba ta zura kwallo mafi sauri ba a wasan da ba na sada zumunci ba tun 12 ga Oktoba, 2005, lokacin da Antonio López ya ci kwallo bayan daƙiƙa 53 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

Dandalin kwallo

🚨 Ferran Torres na ƙoƙarin shawo kan tsohon abokin wasansa a Barcelona, Pedri, domin yabi sahun sabi zuwa PSG. 🇪🇸An bayy...
25/09/2026

🚨 Ferran Torres na ƙoƙarin shawo kan tsohon abokin wasansa a Barcelona, Pedri, domin yabi sahun sabi zuwa PSG. 🇪🇸

An bayyana cewa Torres, wanda ya bar Barçalona zuwa Psg a farkon wannan kakar, yana ƙoƙarin lallashi tare da shawo kan ɗan wasan tsakiyar Pedri domin ya koma PSG

Su biyun abokan juna ne na kut-da-kut a wajen filin wasa kamar yadda aka tabbatar

Dandalin kwallo

‼️💥 Marc Cucurella: “Abin mamaki ne a gare ni cewa Real Madrid ce ƙungiyar da ke yin mafi ƙarancin gudu a La Liga, domin...
23/09/2026

‼️💥 Marc Cucurella: “Abin mamaki ne a gare ni cewa Real Madrid ce ƙungiyar da ke yin mafi ƙarancin gudu a La Liga, domin mu muna yawan gudu sosai.

Ana magana ne kan wannan ne saboda mun yi rashin nasara a wasan derby da kuma a karawar da muka yi da Betis. Da ba mu yi rashin nasarar waɗannan wasannin ba, da babu wanda zai ce ba ma gudu yadda ya kamata.”

🐐 Leo Messi ya zura kwallo ta 75 a tarihin rayuwarsa da bugun Tazara [freekick]50 🇪🇸 Barça12 🇦🇷 Argentina11 🇺🇸 Inter Mia...
21/09/2026

🐐 Leo Messi ya zura kwallo ta 75 a tarihin rayuwarsa da bugun Tazara [freekick]

50 🇪🇸 Barça
12 🇦🇷 Argentina
11 🇺🇸 Inter Miami
2 🇫🇷 PSG

Dandalin kwallo

Diego Simeone ya mayar da martani kan maganar Mourinho:Ya ce lallai akwai iyaka da bai kamata a ketare ba duk maganar da...
20/09/2026

Diego Simeone ya mayar da martani kan maganar Mourinho:

Ya ce lallai akwai iyaka da bai kamata a ketare ba duk maganar da za kayi. ❌

Ya ce ko waye kai - kai ne Mourinho, Flick, Pellegrini, ko ni kaina, ko wani daban - ya kamata mu yi hankali da abin da muke fada a baki.

Ba za ka taba rasa mutuncin da alkalin wasa ke da shi a gare ka ba. Dole ne ka kiyaye mutuncinsa. ⚠️

Ya kamata mu zama masu mutunta juna. Wani lokaci abubuwa kan yi maka daidai, wani lokacin kuma sai akasin haka.

YANZU-YANZU: REAL MADRID SUN FITAR DA SANARWA A HUKUMANCE, BAYAN WASANSU DA ATLÉTICO:“Real Madrid ta sha kashi a wasan h...
20/09/2026

YANZU-YANZU: REAL MADRID SUN FITAR DA SANARWA A HUKUMANCE, BAYAN WASANSU DA ATLÉTICO:

“Real Madrid ta sha kashi a wasan hamayyar da aka buga a Metropolitano, a wasan da alƙalancin Ortiz Arias ya kasance mai matuƙar muni.

“Ya kasa korar Cuti Romero daga fili a farkon rabin wasan bayan ya taka gwiwar Bellingham, duk da cewa ya je na’urar VAR domin duba lamarin. Haka kuma, bai kori Kang-In Lee ba bayan ya taka ƙafar hagu ta Valverde.

“Dukkan waɗannan hukuncin sun yi tasiri a wasan, wanda daga ƙarshe Atlético ta samu nasara a rabi na biyu.”

Dandalin kwallo

Cristian Romero ga Bude Bellingham. "Kai jariri ne mai kuka, Je ka yi kukan ka."Dandalin kwallo
20/09/2026

Cristian Romero ga Bude Bellingham. "Kai jariri ne mai kuka, Je ka yi kukan ka."

Dandalin kwallo

Kwanaki 𝟒,  𝐇𝐀𝐓-𝐓𝐑𝐈𝐂𝐊𝐒 𝟐. Ƙwallaye 𝟑𝟔 cikin wasanni 𝟖. Wannan tawagar ta 𝐁𝐀𝐑𝐂𝐄𝐋𝐎𝐍𝐀 ta wuce misali. 🤯Wasanni 𝟴, Nasara 𝟴....
19/09/2026

Kwanaki 𝟒, 𝐇𝐀𝐓-𝐓𝐑𝐈𝐂𝐊𝐒 𝟐. Ƙwallaye 𝟑𝟔 cikin wasanni 𝟖. Wannan tawagar ta 𝐁𝐀𝐑𝐂𝐄𝐋𝐎𝐍𝐀 ta wuce misali. 🤯

Wasanni 𝟴, Nasara 𝟴. Su waye zasu iya dakatar da 𝗕𝗔𝗥𝗖𝗘𝗟𝗢𝗡𝗔?!

Dandalin kwallo

🚨⚔️ Lamine Yamal kan El Clásico:“Ina son fuskantar Real Madrid a El Clásico. Gaskiya ina matuƙar son irin wannan wasa.”“...
18/09/2026

🚨⚔️ Lamine Yamal kan El Clásico:

“Ina son fuskantar Real Madrid a El Clásico. Gaskiya ina matuƙar son irin wannan wasa.”

“Idan ka taso daga La Masia, ka san cewa El Clásico tamkar yaƙi ne a gare mu.” — Movistar

Address

Kaduna
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandalin kwallo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dandalin kwallo:

Shortcuts

Share

Category