BURIN Masoyi

BURIN Masoyi

Share

Love story

13/02/2024

Wasu Kurakuren Da Maza Magidanta Suke Tafkawa Kuma Ko Ajikinsu:

SHARE 🔔

Bama dabi'a ba, sun ma maidasu tamkar abune na wajibi su aikata hakan.

Wadannan dabi'un suna da matukar wahala a samu wani namijin da bai da wasu daga cikinsu. Dabi'un nan sune kamar haka:


1: Kula mata da sunan da sunan namiji mijin mata hudu ne. Wannan bai zama dalilin da Kaine can kaine nan ba. Amma kana da mace ko mata ba aure kake da niyar yi ba amma ana ganinka da wasu matan. Wannan kuskure ne.

2: Ka kashe kudi a waje amma a gidanka matsolo kake.
Idan kana tare da abokanka ko 'yan matanka baka shakkar kashe kudi, amma kanada shiga gida ka dawo babu.

Kaje kana ciyar da wasu da basu da hakki a kanka abubuwa masu dadi. Amma gidan ka suna cin abinci ko nama babu. Wannan kuskure ne.

3: Murtuke fuska shima yana cikin genden kuskuren da wasu maza magidanta suke yi.
Idan suna waje dariya da shewa babu kaukautawa, da sun shigo gida sai su hada fuska ko kada mace ta raina su. Wannan bayaga kuskure ne babba, har ila yau jahilci ne da gabanci ga duk namiji mai irin wannan halin.

4: Wasu mazan ba zaka taba ganinsu sun fita sun jera da matansu, ko sun shiga mota tare ba domin yin wani ziyara, dubiya ko shakatawa. Gani suke agansu da matansu tare faduwan ajine. Amma yana barin gidansa zai iya zuwa wajen wata da zai sa a gaban mota su tafi shan 🍨. Kuskure ne babba.

5: Akwai wani kuskuren da wasu mazan ke yi na kin wadata matansu da iyalansu da suturan sawa daga Sallah sai Sallah.

Babu wani abun burgewa da zaka hana matarka tayi maka kwalliya mai kyau, amma zaka kalli wasu matan na waje da s**a yi shiga mai kyau kana sha'awar su.

Wadata iyalinka da sutura da kayan kwalliya ba asaran kudi bane, domin haka Allah (SWT) Ya umurta maza suyiwa matansu. Shiyasa ma Ya haramta wasu mazan su kalli kwalliyar da matarka zata maka.

Idan kana cikin irin mazan nan 'yan gargajiya daga Sallah sai Sallah to ka daina saboda kuskure ne.

6: Rashin yin wasu shawarwari da matarka nan

03/11/2023

__❤💐❤ALAMOMIN DA❤❤❤_
ZAKI GANE NAMIJI YANA SONKI
___💜💐💜 >. >>

14/09/2023

IDAN KA GA MA'AURATA SUNA SON JUNAN SU... 🥰😘

🖤🥀 Idan ka ga mata da miji suna son junan su cikin farin ciki da annashuwa da kyakkyawar fahimtar juna,kada ka ce lallai waɗannan sun ci sa'a!..

🖤🥀 A cikin rayuwar aure babu wani abu da ake kira da suna "sa'a"..

🖤🥀 Ba ka san irin yadda kowane ɗaya daga cikin su ya sauka daga ra'ayin sa domin rayuwa ta yi kyau ba..

🖤🥀 Ba ka san yawan aibobin juna da s**a kawar da ido ga barin su ba saboda rayuwa tare da samun sulhu a tsakanin su ba..

🖤🥀 Ba ka san yawan kura-kuran da s**a yafewa junan su ba..

🖤🥀 Kai ba ma za ka taɓa iya hararo matsalolin da s**a samu a tsakanin su sannan s**a kuma haɗiye su saboda suna matuƙar son su kammala rayuwar su tare da juna ba..

🖤🥀 Ba ka kuma san tsawon lokacin da s**a ɗauka a tsakanin su domin samun fahimtar juna ba.

🖤🥀 Ita soyayya ba ta taɓa zama "sa'a" ba..

🖤🥀 Soyayya wata kyauta ce da baiwa da masoya suke yi wa junan su,imani ne daga zuci,abu ne da ɓangarori biyun suke raji tare da nuna bajinta ne da tausayi tare da haƙuri da juna..

🖤🥀 Idan har babu waɗannan siffofi a cikin alaƙar ka ta aure,to ka yi ƙoƙarin samar da su; saboda ka samu jin daɗi a karan kan ka,ka kuma sanya abokin zaman ka cikin jin daɗi.

🖤🥀 Jama'a ba a zaman aure da karya,zargi,munafunci,yaudara da cin amana,duka wadannan siffofi suna lalata zamantakewar aure komai hakurin ka.

29/07/2023

Hanyoyi 8 na Sace Zuciyar Budurwa:

Kasan cuwar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu.

Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa.

🌹 TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.

🌹 KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.

🌹 KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.

🌹 KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya. Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.

🌹 KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yi

29/07/2023

MATUQAR masu dukiya zasu sayi kayan masarufi suboye alokacin da al'umma suke buqata. Idan Allah yarike ruwan sama karkayi mamaki.

MATUQAR zubda jini da fyade da madigo da luwadi yayi yawa acikin aluma idan Allah yahanamu ruwan sama karkayi mamaki.

Matuqar cin amana,Da saba alqawari da tauye hakkin marayu Zaicigaba da yaduwa acikin aluma idan Allah ya hanamu ruwan sama karkayi mamaki.

Matuqar zamurike istigifari da hailala da salatin annabi s a w. Munatare da samun damuna me albarka. Da samun 'ya'ya nagari da zaman lafiya acikin al'umma.

Allah ka gafarta mana zunubanmu kabamu damuna me albarka,ALFARMAR SHUGABA S A W.

08/07/2023

Kano ta dabo tunbin barayin wayoyi koda vivo kazo sai an sace🤣🤣🤸🤸

30/05/2023

SHAGWABA 🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈
Shagwaba :ki bude kunneki 👂idan kuna kwance zai Tashi kifara kuka shagwaba uhmmm uhmmm, idan yace lfy? Kice ba kaineba zaice me nayi? Zaka ciremin bargon da na rufe kuma sanyi nakeji zaice ai ban cireba kice ai dumin jikinka ne bargon niba wannan ba kawai kadawo 🙈
*kuna zaune kice baby zan sha ice cream idan yace ina zansamu ice cream yanzu saiki kalleshi cikin ido kice ba gashinanba inyace aina? Kice a bakinka sai kiyi masa french kiss🙈kice ai yawun bakinka yafi ice cream dadi
* idan kin shiga toilet kina wanka saiki leko kiyi kara kice wayyo baby zai taho yace lfy 🙈 kice soson da zafi, zaice to ya za'ayi kice ka goge sabulu a hannunka kayimin dashi zaifi soson bazanji zafiba🙈
*
Idan yana zaune a palour yana kallo 🙈saiki taso daga inda k**e ki fada jikinsa ki fara kuka idan ya tmby ki, uhmm uhmmm dear ni kallo zanyi saiki yi kwanciyanki a jikinsa🙈🙈🙈🙈🙈🙈

Zan ci gaba amma sainaga ana following Dina kada ku manta burin masoyi nakune 🧐💃💃💃💃💃💃💃💃

16/05/2023

Ina Shiga ALJANNAH Zanyi Kabbara in cire Riga inyi jifa da ita🥴Ince HURUL'EN Kuna Ina s**e HABIBI gamu ince BAKWAI SU TAHO😋💪

16/05/2023

BATUNA NA YAU AKAN YANMATA MASU LALURAR KWARJINI NE.

Ya yan'uwana maza masu son yin aure ko ƙari, akwai yanmata dayawa da sunka kasa auruwa saboda lalurar kwarjini, maza tsoron tunkarar irinsu suke sai kaji ance “wace ai girman kai gareta” ko kuma “wace ta raina maza” ko kuma “wace zaɓe take yi” ko kuma “ai wace matar manyace ba irin mu ba”. Amma wallahi su matan ba haka suke ba kamar yadda ake ganinsu, hasalima lafiyarsu sarai kuma sumul basa da girman kai b***e massu.

Wata wallahi har kuka take yi saboda wannan lalura ta kwarjini, kullum addu'ar suke Allah ya kawo musu miji, kuma kullum tunani suke yaushe maza zasu daina musu ganin masu raini ko zaɓe ko fin ƙarfi. Ai mata masu zaɓe da girman kai daban suke, kana ganinsu da shegen azarɓaɓin tsiya da feleƙe suke, da rawan kai kamar fanka.

Irin waɗannan mata masu lalurar kwarjini sun fi yawa a GRA da unguwannin quarters-quaters da barikin Soja da Police. Dan Allah yan'uwana maza a dinga jarraba irinsu, wallahi dayawa daga cikin yaran masu kuɗi ko masu lalurar kwarjini sauƙin kai garesu, kuma ga nutsuwa da tarbiyya.

Amma kaga yan kalen dangi dake zuwa su tare a gidan yan'uwa masu kuɗi, su kam sai a hankali wata ma har wuce makaɗi da rawa take, kai kace babanta ne mai kuɗin ashe kawunta ne ko mijin yayarta ko aunty.

Masu iya magana s**a ce a rashin tayi ake barin araha. Mata masu lalurar kwarjini, ina roƙa maku Allah ya kawo muku mafita ya yaye maku wannan matsalar kuma Allah ya baku maza masu sonku da tausayinku, masu massu kuma Allah ya baku lfy.

©️ Öpphìçhìàl Ràbèèù Èàsèr 🖌️🖌️ ✍️

02/05/2023

HANYOYI 10 DA ZAKA GANE KA CI KAI👇😂

1. Yayinda Kaine kake aiki cikin wahala da jurewa Rana Amma Budurwarka ce ke lashe Albashin. TO KA CI KAI 😂😂

2. Ka siyowa Budurwarka Suya Amma sai kake cin Albasa ba Naman ba. TO KA CI KAI 😂🤣

3. Ka siyo IPhone8 ga Budurwarka Amma wani saurayin na daban acan gefe yana browsing da ita. TO KA CI KAI 🤣😂

4. Kun shafe shekara 3 Kuna soyayya Amma aduk Lokacin da zata gabatar da kai ga kawayenta saita gabatar da kai a matsayin Aboki. TO KA CI KAI 🤣😂

5. Kace da ita Ina Sonki ta Mayar maka da Nima haka ka koma gefe kana ta washe Baki. TO KA CI KAI 🤣😂

6. Ka siya Mata katin waya na 500 Amma sai kace da ita idan ta saka katin tayi maka Flashing. TO KA CI KAI 😂🤣

7. Ka shafe tsawon Lokaci kana yi Mata Shopping Amma ko sau Daya Bata taba hada maka Abinci na Musamman kazo ka ci ba Koda da Azumi. TO KA CI KAI 😂🤣🤣

8. Ka siyo Mata sabbin Dinki Amma Bata taba saka su ba idan kazo zance sai zataje Unguwa. TO KA CI KAI 😂🤣

9. Kunje Restauranta ta lashe Abincin sama da 3500 Amma har kuka rabu batare data Furta maka kalmar I Love You ba. TO KA CI KAI 😂🤣

10. Ka karanta Post din Kuma ka nishadantu Amma ka tafi batare da kayi Comment ko Like ba. TO ARADU KA CI KAI 🤣😂🤣

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Ikara
Kaduna
IKARA