19/03/2026
LABARIN DUNIYAR TARIHI YANA MAIMAITA KANSA, YARBAWA DA IYAMURAI SUNE S**A KOYAR DA TA ADDANCI ANAJERIA.
Lawrence Nomanyagbon (Anini)
Lawrence Nomanyagbon Anini wanda aka fi sani da "The Law," sanannen ɗan fashi da makami ne na Najeriya wanda ya addabi birnin Benin ta tsohuwar jihar Bendel a tsakiyar shekarun 1980.
Duk da cewa ya takaita ta'asarsa ga Jihar Bendel (jihohin Edo da Delta na yanzu) da kewaye, Anini ya kasance babban batun tsaron ƙasa kuma wanda ya janyo abin kunya ga Rundunar 'Yan sandan Najeriya. Yana jagorantar gungun yan ta'adda wanda ya kai ga wani mummunan matsayi tsakanin watan Agusta da Disamba na 1986, ya kashe mutane yadda ya ga dama, ya yi fashi, ya yi wa mata fyade, sannan ya yi garkuwa da su, inda ya ƙarfafa kai hari ga manyan jami'an 'yan sanda, kai har ta kai ga kai hari kan ayarin kwamishina da mataimakin babban sufeton 'yan sanda. Ayyukansa na ta'addanci ya tilasta wa jaridar Guardian Nigeria ta yi tambaya a ɗaya daga cikin rubuce-rubucenta - "Shin za a iya k**a Anini?"
Ta'addancin sa ya kara yaɗuwa a faɗin ƙasar a lokacin da Anini ya addabi jihohi uku - Ondo, Anambra, da Bendel.
Asali
An haifi Lawrence Nomayagbon Anini a shekarar 1960, kuma ya fito ne daga ƙauyen Orogho (Ƙaramar Hukumar Orhionmwon) kimanin kilomita 100 daga birnin Benin. Daga baya aka gano cewa mahaifinsa Oghadomwangbe ya mutu a shekarar 1980.
Lokacin da Anini ya yi ƙaura zuwa birnin Benin, burinsa shi ne ya zama direba. Ya koyi tuƙi kuma ya fara tuƙa Taxi a cikin birni. Duk da cewa yana ƙarami, a wurin ajiye motoci, duk abinda ya fada ta zauna. Kuma ya shahara wajen warware matsalolin wurin ajiye motoci.
Zama mai aikata laifi
Ba da daɗewa ba ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen tuƙi, zuwa aikata laifuka, inda ya zama direban 'yan fashi a Benin. Bayan ya koyi dabaru, ya kafa ƙungiyarsa ta kansa wacce ta ƙunshi Monday Osunbor (a matsayin kwamandansa), Solomon Osemwenkhae, Johnbull Ahuwan, Moses Idahosa, Philip Iwebelua, Bernard Obi, da Friday Ukponwan. Sun ƙware a satar motoci da fashin banki. A cikin mutanensa akwai wani jami'in 'yan sanda, DSP George Iyamu, wanda ya taimaka wa ayyukan ƙungiyar da mak**ai da bayanan tsaro.
Charles Enonchong, marubucin littafin 'The Rise and Fall of Anini', ya bayyana Anini a matsayin mai son kyawawan tufafi kuma mai shan taba sigari.
Aikata laifuka Anini ya fara ne a farkon shekarun 1980, kuma ya kai wani matsayi tsakanin watan Agusta da Disamba na 1986 lokacin da ya haɗa gangan yan fashi. Mazauna Bendel da jihohin da ke makwabtaka da shi sun rayu cikin tsoro da firgici yayin da Anini da mutanensa s**a sami 'yancin aikata abin da ransu yake so. Kafafen watsa labarai sun sanya masa suna "Sarkin Benin Mai Zaman Kansa". (“Outlaw King of Benin”).
A watan Agusta na shekarar 1986, Anini da gungun mutanensa sun kai hari a Bankin First Bank, Sabongida-Ora, a Jihar Edo. Sun sace dala 2,000. Dala ɗaya a 1986 ana canja ta a Naira 5.
A ranar 21 ga Oktoba, 1986, bayan ya saci Naira 46,000 daga reshen Agbor na African Continental Bank, Anini ya shiga wata kasuwa da ke kusa ya rinka watsar da wani ɓangare na kudin daga cikin motarsa ga talakawa masu wucewa. Wannan lamarin ya sa aka yi masa lakabi da 'Robin Hood', sunan wani mutum ɗan Birtaniya wanda ya yi wa masu kuɗi fashi kuma ya raba kuɗi ga talakawa.
Anini mutum ne azzalumi kuma 'yan sanda ne s**a fi shan wahala a hannusa. An ruwaito cewa Anini da gungun yaransa sun kashe jimillar mutane 20 - 'yan sanda 11 da fararen hula tara.
Wasikun Anini
Anini ya yi ƙarfi sosai har ya fara rubuta wasiƙu ga waɗanda zai farmaka don sanar da shirin ziyararsa. Kuma bai taɓa kasa cika maganarsa ba, a lokacin da ya ambata zai ziyarci waje don yin fashi.
A watan Agusta na shekarar 1986, Anini ya rubuta wa manajan Bankin New Nigeria, reshen Ring Road, da ke Benin City wasiƙa, yana sanar da bankin cewa yana da niyyar zuwa a kowane lokaci, "ya k**ata a ware masa Naira 10,000," Charles Enonchong ya rubuta a cikin littafin 'The Rise and Fall of Anini'. "Anini ya bayar da adireshinsa a matsayin Lamba 1,000,000 Anywhere Street Within the City, Benin, Bendel State."
Maimakon kai rahoto ga 'Yan Sanda, bankin ya yi gaggawar zuwa wurin Oba na Benin don ya ba da rahoton wasikar Anini ga hukumomin gargajiya.
Akwai mutane da yawa da s**a yi imani da cewa ba za a iya amincewa da yan sanda ba. Mutane da yawa daga cikin mazauna birnin waɗanda s**a taimaka wa 'yan sanda da bayanai da za su iya taimaka wa a k**a Anini sun yi zargin cewa ana iya zarginsu da kasancewa masu hannu a cikin lamarin ko kuma 'yan sanda za su iya aika sunayensu ga Anini. Wasu ma suna jin tsoron cewa za a iya kashe su.
A lokacin ta'addanci Anini ya kara kasaita, Shugaban ƙasa na wancan lokacin Janar Ibrahim Babangida ya ƙalubalanci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Etim Inyang, kuma ya nemi ya san inda Anini yake bayan wani taro na Majalisar Mulkin Soja a watan Oktoban 1986.
"Abokina, ina Anini yake?" Babangida ya tambayi IGP.
A cikin wata wasika da aka ruwaito ya aika wa Shugaban Ƙasa a watan Oktoban 1986, Anini ya rubuta "Ku gaya wa Shugabanmu, muna son sa amma ba mu ji daɗin mulkin sa a nan Bendel. Kudin komai ya karu. Shi ya sa yanzu nake raba duk wani kuɗi da na samu ga jama'a."
Mujallar Newswatch a cikin shafinta na ranar 27 ga Oktoba, 1986 ta lissafa sharuɗɗa shida da Anini ya bayar don zaman lafiya ya dawo birnin Benin.
"Ba za a sake gurfanar da 'yan fashi da makami a gaban kotu ba; dakatar da hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda da kungiyar ma'aikatan sufuri ta Najeriya, da kuma membobin kungiyar asiri ta Ogboni; babu sauran cin zarafin mata 'yan kasuwa da s**a dawo daga wajen sana'arsu; 'dakatar sintiri da karbar 50k-N5 a manyan hanyoyi da kuma dole ne yansanda suyiwa direbobin adalci a kan hanyoyi.
Abin da ke cikin wasiƙar, bai zama abin kunya ba a ce ya sanya kansa a matsayin mai kare ƙungiyar NURTW (tsohuwar ƙungiyar ƙwadago) da kuma mata yan kasuwa, kuma bai kasa yin magana a madadin sauran masu laifi waɗanda ya bayyana su a matsayin 'yan fashi da makami marasa laifi' ba.
K**a shi
A watan Disamba na shekarar 1986, wata wata tawagar 'yan sanda 10 karkashin jagorancin Sufeto Janar Kayode Omonaro ta kawo karshen ta'asar da ya ke aikatawa a ranar 3 ga Disamba, 1986.
Anini yana ciki sharholiyar da ya saba tare da mata a lamba ta 26, t**in Oyemwosa, gaban makarantar firamare ta Iguodala, Benin City, lokacin da Sufeto Janar Kayode Omonaro, wanda ke aiki bisa bayanan sirri da ya samu daga wata karuwar Anini, ya mamaye gidan kuma ya k**a shi ba tare da wata turjiya ba.
A cewar rahotanni da dama, lokacin da 'yan sanda s**a kwankwasa kofar dakin, Anini da kansa ya bude kofar.
Da aka tambaye shi "Ina Anini yake," sai ya yi ƙoƙarin yaudararsu. "Kai, Anini yana kan gado a cikin ɗaki," haka ya amsa da sauri zai gujewa Omonaroro da tawagarsa.
Omonaroro ya miƙa hannu ya harbi idon Anini na hagu. Domin ya raunata karfinsa, 'yan sanda s**a buɗe masa wuta a ƙafa. A lokacin, ya san komai ya ƙare masa, sai ya sake tambayar ko shi ne Anini, sai ya amsa, "Ɗan'uwana, ba zan yaudare ka ba; ba zan gaya maka ƙarya ba, ni ne Anini." An k**a shi aka kai shi hedikwatar 'yan sanda daga nan aka kai shi asibitin sojoji inda aka yi masa magani aka kuma yanke masa ƙafarsa da ta ji rauni.
Yadda Kafafen Yada Labarai S**a Bada Rahoton K**a Anini
Lokacin da aka k**a shi a watan Disamba na shekarar 1986, mujallar Thisweek ta buga hoton Anini da ya ji rauni sosai a gadon asibiti tare da taken "Anini ido da ido da hukunci.
Sai dai jaridar Guardian Nigeria ta yi Allah wadai da tsarin da 'yan sanda s**a bi wajen k**a Anini.
Hukuncinsa da Aiwatarwarsa
Alkali James Omo-Agege, Shugaban Kotun hukunta yan Fashi da Mak**ai ta Benin ta Farko wadda ta yi shari'a kan Anini, da ƙungiyarsa, da DSP Iyamu, ya yanke musu hukuncin kisa a watan Fabrairun 1987. A ranar 29 ga Maris, 1987, an kashe Anini a bainar jama'a tare da Osunbor ta hanyar harbin bindiga. An riga fara kashe membobin ƙungiyarsa tare da DSP Iyamu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press (AP) ya ruwaito cewa "dubban mutane daga kowane bangare a jihar Bendel a yau (29 ga Maris, 1987) sun kalli yadda aka kashe manyan 'yan fashi da makami Lawrence Anini da Monday Osunbor a bainar jama'a a birnin Benin."
'Yan mintuna kafin a harbe shi, Anini "ya karɓi alhakin duk wani zalunci da ya aikata wa al'umma kuma ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa," in ji AP.
A cewar wani rahoto da jaridar African Guardian ta buga a shekarar 1986, Anini ya shaida wa manema labarai cewa ya haifi 'ya'ya biyu, Osaro da Emadiobogbe da matarsa, Ugo.
Laifukan Anini sun bar wa iyalinsa abin kunya, kuma shekaru bayan mutuwarsa, 'ya'yansa sun ce har yanzu ana yi musu lakabi da 'ya'yan wani mai laifi duk lokacin da suke tafiya a kan t**i.
.