Filin Kwallo

Filin Kwallo

Share

Samu labaran wasannin kwallon kafa domin nishadantarwa.

28/03/2024

Dan wasan baya na kungiyar FC Barcelona Pau Cubarsi ya lashe kyautar gwarzon matashin dan wasan Laliga na watan Maris.

22/11/2022

Manchester United ta sallami Cristiano Ronaldo.
Zaman Cristiano a Man U yazo karshe bayan kungiyar ta fitar da sanarwar raba gari da dan wasan a yammacin yau talata. Sanarwar da Man U ta fitar ta yi bayani kamar haka -
"Cristiano Ronaldo zai bar kungiyar Manchester United ba tare da bata lokaci ba bayan yarjejeniya da aka cimma tsakaninmu da wakilan dan wasan. Kungiyar Manchester United tana kara gode masa bisa gudummowar daya bawa kungiyar a zamansa na farko da na biyu, inda ya samu nasarar zira kwallaye 145 a wasanni 346 daya buga. Muna yi masa tare da iyalansa fatan wanyewa lafiya. Kowa yanzu a kungiyarmu ta Manchester United ya mayar da hankali ne wajen dorawa akan cigaba da ake samu karkashin mai horaswa Erik Ten Hag kuma ana aiki tare tsintsiya madaurinki daya domin cimma nasara." - Manchester United

20/11/2022

Karim Banzema ba zai taka leda a gasar cin kofin duniya ba, saboda rauni.

18/11/2022

Manchester United na duba yiwuwar soke kwantaragin Cristiano Ronaldo. Rahotanni na cewa kungiyar na kokarin daukar matakin ne biyo bayan wata hira da Cristiano Ronaldo yayi inda a cikin hirar tasa ya caccaki kungiyar da me horaswa Erik Ten Hag da kuma wasu 'yan wasa. Bayan hirar ne kungiyar ta Man U ita ma ta fitar da sanarwar cewa zata dauki matakin daya dace. Rahotannin sunci gaba da cewa a Manchester United na nazartar kwantaragin da Ronaldo ya sanya hannu domin nemo inda dan wasan ye keta ka'idojin da aka gindaya a cikin kwantaragin, wanda hakan zai basu damar soke kwantaragin dan wasan ba tare da bashi ko anini ba a matsayin kudin sallama.

18/11/2022

Dan wasan baya na kungiyar Barcelona Alejandro Balde zai maye gurbin Luis Gaya a 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar sifaniya da zasu buga a gasar cin kofin duniya a kasar Qatar. Hakan ya biyo bayan rauni da Luis Gaya din yaji, wanda ya sa mahukuntan kungiyar s**ai hanzarin cire sunansa da sauya shi da Balde kafin rufe kofar sauya sunayen 'yan wasa, za'a rufe kofar sauya sunayen 'yan wasa a gobe asabar karfe biyar na yamma agogon Nigeria.

18/11/2022

RONALDO YAYI RUWAN YABO AKAN MESSI

Masu sharhi a harkar kwallon kafa a wasu lokuta na ganin cewa akwai wata gogayya ko kuma kishi tsakanin 'yan wasa Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi, in da mafi yawanci magoya bayan kowane dan wasa a cikinsu suke ganin nasu gwanin yafi kwarewa.

Se dai a wata hira da Cristiano Ronaldo ya yi, dan wasan ya yabi Lionel Messi sosai. Ga kadan daga cikin abin da Ronaldo din yace.

"Messi dan wasa ne me abin mamaki da ban sha'awa, yana daga cikin yan kwallo da s**a fi kwarewa a duk duniya. Mun kasance muna buga kwallo da Messi a mabanbantan kungiyoyi sama da shekara goma sha shida (16) da s**a wuce, muna da mu'amala me kyau a tsakanin mu. Bazan ce abokina ne na kusa-kusa wanda muke mu'amalar yau da kullum tare ba, se dai nace Messi kamar wani dan wasa ne da muke bugawa kungiya daya.

Ina ganin girman Lionel Messi mutuka domin yana magana me kyau ko da yaushe a kaina. matarsa ma da budurwata suna ganin girman juna domin dukkansu 'yan asalin kasar Argentina ne

Me zance a kan Messi? Zance babban dan wasa ne wanda ya cimma manyan abubuwa a harkar kwallon kafa" - Cristiano Ronaldo

18/11/2022

Manchester United na son dauko Mbappe domin ya maye gurbin Ronaldo. Masu sharhi na ganin zaman Ronaldo ya zo karshe a Man U , biyo bayan hira dayayi da 'yan jarida yana s**ar kungiyar tasa da kuma me horaswa.

18/11/2022

Sadio Mane ba zai buga gasar cin kofin duniya ba wanda za ayi a kasar Qatar.

Dan wasan na gaba na kasar Senegal yayi rauni a ranar takwas (8) ga Nuwamba din da muke ciki a wasa tsakanin Bayern Munich da Werder Bremen. Se dai duk da raunin, kasar Senegal ta saka sunansa a cikin sunayen 'yan wasanta da zasu buga a gasar cin kofin duniyar, a bisa fatan cewa dan wasan zai warke akan lokaci kafin fara gasar ko kuma koda an fara gasar ze warke bada jimawa ba.

Se dai a yanzu haka an cire sunan Mane daga cikin ;yan kwallon kasar Senegal da zasu taka leda bayan da likitoci s**a tabbatar da cewa raunin dan wasan bazai warke anan kusa ba.

18/11/2022

Real Madrid zata bude wajen shakatawa a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Kungiyar ta fitar da sanarwa a shafinta na yanar gizo. Sanarwar ta ce kungiyar ta cimma yarjejeniya da hukomomin kasar domin bude wajen, kuma ana fatan budewa a karshen shekarar 2022. Wurin zai kasance yana da bangarori da s**a hada da wurin ababen tarihi a kan kungiar da wurin hutawa da nishadi da wajen yin wasa da kuma wajen siyar da kayan kungiyar.

17/11/2022

Kungiyar Kwallon Kafa ta kasar Faransa ta sauya sunan Christopher Nkunku da Randal Kolo Muani biyo bayan rauni da Nkunku yaji a yayin atisaye da kungiyar a kasar Qatar. Kungiyoyi da zasu buga gasar cin kofin duniya suna da damar chanja sunayen 'yan wasa har zuwa awanni 24 kafin a fara wasan farko na gasar.

17/11/2022

Hukumar gasar kwallon kafa ta Laliga ta yanke hukuncin hana buga wasanni har guda uku (3) akan dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Robert Lewandowski. Hakan ya biyo bayan rashin kunya da hukumar ta ce dan wasan ya yi bayan korarsa da aka yi a wasa tsakanin Barcelona da Osasuna, inda kafin Lewandowski ya fita daga fili ya nuna alamar cewa kamar alqalin wasan yana shaye-shaye, wannan ya saka hukumar yanke hukuncin akan dan wasan. Shi ma Gerard Pique an yanke masa hukuncin hana buga wasanni har guda hudu (4), saboda laifin zagin alqalin wasa da hukumar ta ce yayi. Se dai wannan hukunci bazai shafi Pique ba domin ya riga da ya ajiye kwallon kafa. Kungiyar Barcelona tana da damar daukaka kara se dai da wuya su samu nasara a janye hukuncin da aka yiwa Lewandowski gaba daya.

16/11/2022

Messi ya ce ya kusa rataye takalmansa, ma’ana dai zai yi ritaya.
Jaridar Football Espana ta rawaito dan wasan yana cewa.
"Ina son kwallon kafa, ina son naga ina taka leda kuma ina jin dadi idan inayi. Babu abin da na sani a gaba daya rayuwata in banda na buga kwallo, saboda haka na tabbata duk abin da zanyi bayan nayi ritaya dole ze shafi kwallon kafa, amma bamu san me gobe zatai ba. Bana tunanin ci gaba da buga kwallo na tsawon lokaci a nan gaba." - Lionel Messi

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Kano