El ahmad engineer lawi
tsamiyar zubau
02/06/2024
Yanzu haka nasamu sama da $1 dollar kyauta daga wurin binance, kuma nan gaba zan iya samun sama da $50 dollar kyauta kafin su rufe garabasar, BNB suke rabawa kyauta..
Ga yadda zakayi kaima kasamuđ
Step 1: Kayi registration na Binance, idan kuma ka riga kayi, shikenan ba sai kayi ba, Idan kuma ba kayi ba, Sai kayi kuma kayi Verification.
Step 2: A Homepage Éinka, zakaga wani waje na Scanning a can sama, Sai ka danna shi zai kawo maka wajen shiga Camera.
Step 3: Zakaga Option biyu ko Éaya, sai ka danna wajen Upload Photos, Sai kayi Upload Éin wannan QR Code Éin na Post Éin nan, Saika Éan jira kaÉan, zai kai ka wajen da zaka yi Claim.
Step 4: Kanayin Claim, zakaga abinda s**a baka a Balance Éin ka, Allah yasa mu dace.
Nagode..
ÂŽ Salisu Abdurrazak Saheel
Note: ni ma na samu, amma dai bai kai 1$ wanda na samu
Salisu Abdurrazak Saheel lawi copy
17/05/2024
Zamuyi Giveaway Daga Alkhairin Da Muka Samu Na Mining din Notcoin
Biyo bayan fashewar Notcoin, mun samu sabbabin mutane da s**a shigo wannan kasuwanci namu na Crypto, mun zauna mun tattauna sannan muka yanke wannan shawarar; babu abinda mutanen mu suke buĆata a yanzu kamar ilimin Crypto da Blockchain, saboda kar duk abinda s**a samu su rasa shi saboda rashin ilimin yadda zasu tafiyar da kasuwa.
Don haka yanzu mun dawo da Telegram Channel Éinmu na Fafutuka sannan zamu Éauko Ćwararru a wannan fannin na Crypto da Blockchain dama sauran fannuka na Cyber security a karantar da mutane a kyauta. Babu ko sisin ku, shine Giveaway Éin na farko.
Wannan Shine Chanel din da Kowa Zai Shiga https://t.me/fafutuka
Na biyu kuma, duk wanda yayi sharing na wannan rubutun, wanda yake Éauke da link na Telegram Channel Éinmu suma zamu basu Giveaway na kuÉi bayan na karatun da za'a samu:
1. Wanda yafi kowa yawan likes da engagement, na Éaya zai samu Kyautar N50K.
2. Na biyu Zai Samu Kyautar N20k
3. Na Uku zuwa na goma kowannen su Zai Samu Kyautar N10K.
4. Na 11 zuwa 20 kowa zai Samu Kyautar N5K
5. Daga na 20 zuwa na 30 kowa zai samu Kyautar N3k
6. Daga na 30 Zuwa na 40 kowa zai samu N2k
7. Daga na 40 Zuwa 50 kowa zai damu data 5GB Kyauta
Sannan akwai kyaututtuka da za'a bayar bayan an fara karatu acikin Channel Éin.
Channel link https://t.me/fafutuka
Duk Wanda Ya Dauki Wannan Rubutun idan Yayi Post Yai Tagging din Comr Haidar H Hasheem
Game buĆata yamin magana ta WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/FXoCUcej0qgBrVDWRtYVK2
03/05/2024
Masu buĆatar film đ˝ď¸đĽ na Al gaita kowani irine sumin magana Amman saikana telegram chart
Engineer lawi
WhatsApp number is
07040513340
26/04/2024
Kada ka zama mutumin kirki. Nazari cikin Falsafa.
Wannan mutumin bisa haÉin kan duniya babu shi ba a kuma taÉa yin sa ba, ba wani mutum da yake da wannan kalmar, face ga wasu babu wanda bai cancance ta ba sama da shi. Babu wani addini guda Éaya, al'ada, fahimta, ra'ayi, falsafa, hikima... da ta iya samar da wannan mutum bisa ra'ayin duk duniya kowa ya yarda, ba tare da samun mai s**a ba.
A ilimin halitta, akwai abunda mun yi tarayya akan sa, misali: komai kafin ya wanzu dole sai da kuzari (energy), ka san me ya sa mutane s**a yarda da haka? Saboda ba wanda ya san energy a haĆiĆanin sa, ka riĆe wannan; mutane ba suna saÉa ni a kan abunda ba su sani ba ne, ai daman ba su san shi ba, suna saÉani ne akan abunda s**a sani, saboda sun san shi.
A mafi yawan lokaci, mutane na siffanta wani da kirki ne bisa raunin da suke da shi, wanda ya iya magance mu su, misali: a wajen mai kwaÉayi, wanda bai san abun sa, kuma yake ba shi, mutumin kirki ne.
A wajen masifaffe, Wanda ya amincewa wulaĆacin sa, mutumin kirki ne, a wajen mai cin hanci, wanda zai bayar mutumin kirki ne.
Wasu kuma kirki a wajen su, na nufin mai irin fahimtar su koda mene ne halin sa, misali masu aĆida Éaya, addini Éaya, Ćabila Éaya, sana'a Éaya, sun fi jin kirki ga waÉanda suke da abu Éaya irin na su, sama da mai kishiyantar su, ka da manta sabanin tsakanin Fulani, da Mahauta.
Wasu kuma kirki a wajen su shi ne hali ya zo Éaya, kamar zafi, ko sanyi, kyauta ko mugunta.
Wasu kuma kirki a wajen su shi ne: masu abunda ba su da shi, kuma suke son sa a matsayin Ćarin daraja, misali; Ćalibi na ganin wanda ya fi shi ilmi ya fi shi kirki, haka talaka ga mai kuÉi, haka mace ga mijin ta, har sai wani dalili ya kore hakan.
Wasu kuma shekaru kamar ya'ya da iyayen su. A takaice siffanta mutum da kirki wani abu ne na daban ga mutane daban daban, kuma a kalma Éaya ga kowa da kowa babu shi a zahiri, duk wani hali da wani zai ga kirkin ka akan sa, shi ne dai halin da wani zai ga rashin kirkin ka akan sa.
Saboda Hi**er ya kashe Yahudawa ya zama mutumin banza ga Yahudu, amma ga yan N**i wannan shi ne dalilin zaman sa mutumin kirki, don haka ka da ka yi ĆoĆarin zama mutumin kirki, domin babu shi, idan kuma ka ce sai ka yi, za ka rasa zatin ka, to ya za ka yi ? Amsa: ka yi ĆoĆarin zama mutumin gaskiya, ita ce: siffa da ta tsaya da zatin ta ba tare da jingina ba, don haka ma Allah da bai jingina da kowa ba, ya siffantu da ita.
Tambaya Éaya ta rage, wane ne mai gaskiya ?
1- Shi ne mutumin da Yake Kallon lamari a yadda yake bisa azancin hankali, ba da nazarin Ćawazuci ba.
2- wanda yake a shirye ya bar abu a duk lokacin da ya fahimci ba dai-dai ba ne ba.
3- wanda ya fahimci rayuwar sa na da manufa sama wanzuwar sa.
4- wanda ya san amfani mutum amfanar da bayi ne ba amfanar da ubangiji ba.
5- Wanda ya fahimci Allah ake bauta mahalicci ba son zuciya ba.
Idan ba ka gane hakan ba, a sauĆaĆe shi ne: Ka yi riĆon da sunnar manzon Allah (saw) gam, ko da kuwa kowa bai ga kirkin ba, daman ba su ne za su yi ma ka hisabi ba, ita sunna gaskiya ce mai zaman kan ta bisa zatin ta, sawa'an an bi ta ko ba a bi ta, ga Allah ake komawa, kuma Allah shi kaÉai ke ba da sakamako, ba wai kawai don an ce da kai mautumin kirki ba a duniya, sai ya ba ka aljanna a lahira, da wannan siffar ta kirki da wasu s**a ba ka, mai yiwuwa ne ita ce silar zuwan ka wuta. Kirki na haĆiĆa na cikin bin halin Manzon Allah (saw) sau da Ćafa.
Allah ya yi mana tsari.
âď¸. Bukhari Alhawari
26/04/2024
DAĆIĆAN ZAMANI (PART 1)
A wurin daĆiĆan zamani :
1. Tela yanada iko yayi Éinki da keken industrial a biyashi ya samu kuÉi.
2. Ćan Boko yanada iko yayi aikin gwamnati ko na Kamfani a biyashi albashi.
3. Techie bayada ikon ya zama developer yayi aiki da computer shi a biyashi.
Na biyun shima fa Ćila computer kawai yake dannawa ko aiki da office files da sauran takardu.
Zaka Éauki shekaru kana koyon abubuwan technology sannan ka hana idonka bacci kana aiki sanda kasamu kuÉi kuma ya riga kallon cewa a banza kake samu.
Wanima zai iya kiranka da Ćan Yahoo saboda jahilci.
A wurin daĆiĆan zamani, Ethical Hackers Yan Yahoo ne.
Ya Ćai daĆiĆin zamani, Ćłan Yahoo ba Hackers bane, saboda bama su iya hacking ba damfara kawai s**a iya itama kuma damfara ba hacking bace, ta yuwu dai suyi amfani da dabarun social engineering wajen damfararsu.
A wurin wasu daĆiĆan zamanin ba'a samun kuÉi a harkar tech dole sai anyi cuta dukda yasan cewa masu kuÉin duniya techies ne, ya san cewa kuma su
Bill Gates, Elon Musk, Mark Zuckerberg dss duk ba cuta s**ayi s**a zama abun da s**a zama ba, aiki s**ayi tukuru. Mu Éauki misalin Mark, Mark programmer ne tun yana yaro kuma gashi da harkar programming Éin ya zama Éaya daga cikin masu kuÉin duniya.
Elon Musk tun yana yaro yake da burin harkokin space, har rashe yaje s**a nuna masa bazai iya siyan rockets ba, shi kuma yacewa kansa zai iya haÉawa da kansa kuma ya haÉan, ku duba Starlink na Space X a yau.
Ku kula da impact na tech a misalin Ćasa
Net worth na Ćangote a 2014 is around 25 Billion USD.
Net worth na Elon Musk is around 2 Billion USD.
Net worth na Ćangote a 2024 is around 17 Billion USD.
Net worth na Elon Musk a 2024 is around 200 Billion USD.
Zan chigaba...
Ayi hakuri da kalmomin da nayi amfani dasu.
15/04/2024
Lokacin zafi musamman lokacin da ake samun High Ambient Temperature, ko lokacin da ake rana sosai wayoyin mu (Handset) suma suna daukar zafi sosai, a irin wannan lokacin dole mu kula da yawan ciro wayoyin mu idan muna tafiya a rana, ciro wayoyin a cikin rana zai iya haifar da increasing na temperature din wayoyin mu wanda hakan zai iya haifar ma wayoyin mu da samun matsala, musamman samun matsalar battery.
Ko a dinga fuskantar matsalar Idan an saka caji yaki saurin cika, ko caji yadinga saurin karewa, manyan wayoyi ma musamman 'TYPE C' a lokacin zafin nan zakuga suna yawan rubuto "Device Overheat". Ana bukatar a dinga cire Phone Case saboda wayar ta samu ventilation, sannan a dinga clearing app caches a cikin setting.
A takaice dai a irin wannan yanayin akwai bukatar wayoyinmu suna zama wuri mai sanyi, ban kuma ce ka jefa wayarka a ruwa ba..đ
Barkanku da yamma.
Salisu Abdurrazak Saheel
13/02/2024
Hanyoyin Rage Saurin Zukewar Cajin Waya
Kasancewar wayoyin zamani da ake amfani dasu a wannan lokaci suna da tsare-tsare daidai da zamani, kuma ana gudanar da aikace-aikacen yau da kullum da su, kamar yadda ake sarrafa Kwamfuta wajan gudanar da aiyuka masu yawan gaske. Sannan kuma ana fama da saurin zukewar caji a lokutan da ake tsaka da amfani da su.
SCREEN BRIGHTNESS
Hasken screen, wannan ma hanya ce dake jawo saurin zukewar caji a Wayoyi. Hakan ya sa zaku ga akwai tsarin sarrafa haske a kowacce Naâura, akwai wanda yake Auto; dakanta wayar zata sarrafa hasken a wurare daban daban. Idan mutum yana waje mai duhu zata kara hasken screen daidai misali, haka idan yana cikin haske zata kara shi yadda zai iya gani da sarrafa wayarsa. Sannan akwai tsarin wanda mutum zai iya karawa da kansa daga 1 â 100 wato manual kenan. Saboda haka rage haske a screen na waya zai taimaka wajan rage shan caji. Bayan saurin zukewar caji da hasken screen ke haddasawa, akwai matsala da yake ahifarwa ga lafiyar idon bilâadama.
SOUNDS
Wato sautin Karar shigowar Kira a Waya ko alarm da sauran su. Zaku ga akwai wadanda ake yawan kiran su ko aiko musu da sakonni akai-akai, kuma sun bar karar wayar su a mataki mai kara sosai wanda hakan yana sa cajin waya ya zuke da wuri. Saboda haka zai fi kyau a rage Volume daidai misali hakan zai rage shan caji a waya. Sai dai akwai yanayin wajan da mutumu yake gudanar da harkokin sa kamar kasuwa ko inda yake da hayaniya sosai. Wannan dalili ne da zai sa mutum ya kure sautin karar wayar sa, daga baya kuma sai ya rage idan ya bar wajan.
WALLPAPER
Musamman masu launika, masu ado ko Masu mosti. Suna bada gudummawa wajan shanye cajin waya. Saboda zaku ga suna da haske sosai, hakan ya sa suke saurin zuke cajin waya da wuri. Saboda zaifi kayu ace mutum ya yi amfani da wallpaper wadda bata da launika masu yawa kuma ba mai haske sosai ba.
SCREEN ROTATE
Wato juyawar screen a waya; tsaye ko a kwance. Barin sa a kunna yana sa zukewar caji a waya da sauri. Saboda Sensor din wayar nake yake lura da yadda aka rike waya, sannan ya juya screen
BACKGROUND APPLICATIONS
Akwai mutane masu bude abubuwa da yawa a wayoyin su. Idan s**a shiga wani application zasu yi minimaizin, sai su shiga wani, shima suyi minimaizin su sake shiga wani, haka dai suke yi kullum. Ba tare da sunyi tunanin cewa dukkanin applications din da aka bude suna ci gaba da aiki a boye. Kuma daga cikn su akwai apps dinda suke amfani da Ram, Storage, Camara, wasu da Map da sauran su. A taikace an cikata dai aiyuka masu yawa a lokaci guda. Wannan itama babbar hanya ce dake zuke cajin waya. Saboda zaifi kyau a duk lokacin da aka gama amfani da application a kasha shi gaba dayakafin a bude wani. Hakan zai karawa Waya saurin sarrafa aiki kuma bazata zuke caji da wuri ba.
BATTERY SETTING
Duba bangaren setting na battery yanada matukar muhimmanci domin ganin applications masu zukar caji da yawa ko applications marasa amfani a lokacin. A battery setting ne ake iya sarrafa yadda applications za su yi amfani da battery. Hakan zai taimaka kwarai wajan rage saurin zukewar caji a waya.
NOTIFICATIONS
Shima wannan hanyace wadda ke sa zukewar caji da wuri. Saboda a duk lokacin da sako ya fado cikin waya sai ta yi Haske, Kara har da Vibration. Kuma zaku ga akwai wanda yake amafni da manhajar whatsapp kuma yan cikin group babu iyaka, a duk lokacin da aka yi sharing daga wadannan group sai wayarsa tayi Notifying dinsa akan shigowar sakonnin komai yawan su. A kowanne lokaci sako ya shigo waya sai tayi haske ko kara kuma idan kun duba akwai applications masu yawa da suke amfani da notification, Text Messaging, WhatsApp, Twitter, Facebook, Instagram da sauran su⌠Saboda haka idan akwai application din da bakwa bukatar notification dinsa sai ku shiga setting na application din zaku ga inda akace Notification Setting daga nan sai ku kashe shi, yin hakan zai rage shan caji a wayoyin ku.
VIBRATION
Shima hanya ce dake sa saurin shan caji a waya. Akwai wadanda kullum wayar su a vibration take amma akwai dalilin yin haka. A duk lokacin da kira ya shigo ko notification wayar za ta girgiza domin ankarar da mai ita. Hakan yana haddasa saurin karewar caji. Dan haka zaifi kyau mutum ya lura da lokacin da ake da bukatar amfani da vibration da kuma lokacin da ba a bukatar sa. Ta haka ne za a rage saurin zukewar caji a waya.
WIFI, BLUETOOTH DA MAP
Barin wifi, Bluetooth da Map a bude bayan an kamala amfani da su kamar sharing ko bincike. Hakan yana saurin karewar caji a waya. Saboda barin su a bude sune cikin aikine na bincike ko da anyi minimizing din su. Zaifi kyau a kasha su a duk lokacin da aka gama amfani da su.
TEMPERATURE
A lokacin zafi wayoyi sun fi samun matsalar karewar caji da sauri. Haka zalika idan aka saka caji shima baya saurin a lokaci ko yanayin zafi. Saboda haka zai fi kyau a sarrafa waya a wajan da babu zafi sosai.
A takaice wadannan sune abubuwan da suke haddasa saurin zukewar caji a karshe ma s**a she battery ba tare da mutane sun sani ba. Dan Haka sharace na ke bayar wa akan lura da dukkan abubuwanda na bayyana a sama, saboda a sami saukin matsalar caji.
lawi
Abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ayi laâakari dasu kafin siyan Computer.
Wannan batu ya taso ne bisa yawan tamabayoyi da jamaâa suke aikowa akan neman sanin yadda mutum zai tantance irin Computerr da ta dace ya siya domin gudanar da aiyukan yau da kullum. Sanin muhimman abubuwa kafin mutum ya mallaki naâura yanada amfani kwarai da gaske. Abubuwan suna da yawa amma zanyi bayani akan wadanda s**a muhimmanci.
Jamaâa da dama s**anyi laâakari da kyalkyalin Computer ko sunan kamfanin da ya kera Computer, duk da cewa sunan kamfani yana da matukar tasiri musmman kamfanin da yayi shuhuwa wajan samar da nagartattun naâurori. To amma wasu lokutan akan yi zaben tumun dare. kaga mutum kwana biyu da siyan Computer, yazo yana neman siyar da ita domin ya sayi wadda zata dace da bukatar sa. Kuma dole ne ya yi asara wajan sake siyar da ita.
Idan mutum bashi da ilimin fahimtar ingancin naâurori, to yanada kyau ya tuntubi wanda ya sani musamman dalibai masu nazari a fannin ilimin Computer. A matakin farko yanada kyau mutum ya tantance bukatar irin Computerr da ta dace ya siya, ta girke (Desktop) ko ta yawo (Laptop). na biyun su kuma karfin aljihu (Budget), na ukun su kuma ga su kamar haka;
Masarrafi (Processor): shi ne a matsayin kwakwalwar naâurar Computer, kuma ana bayyana saurinsa wajan sarrafa aiki a matakin GigaHertz (GHz). Yanada kyau a sayi Computer wadda take mafi saurin sarrafa aiki, amma kuma ta kanyi tsada sosai saboda saurinta shi ne darajarta. Shi yasa a wannan matakin yake da kayu mutum yayi nazari akan bukatarsa ta mallakar Computer da kuma irin aikin da zai yi da ita. Idan ya kasance aikin da zaiyi da ita bai wuce rubuce-rubucen ba, irin na aikin ofis ko amakacin haka, baya bukatar siyan Computer sama da 1Ghz na msarrafi. Idan kuma ya kasance aikin sa mai nauyi ne kamar aikin sarrafa Hotuna, Bidiyo masu nauyi da inganci sosai, to anan akwai bukatar babban masarrafi kamar 1.5Ghz zuwa 2.5Ghz ko 3.0Ghz.
Rumubn Aiki (RAM ko Memory): Kusan duk saurin masarrafi (CPU) a Computer ya dogara ne da girman rumbun aiki. Dukkan aiyukan da akeyi da naâurar Computer a cikin wannan rumbu ake gudanar da shi. Kuma ana auna adadin girmansa a tsarin maâauni na Gigabyte (GB). Saboda haka a kowacce irin bukata ana so ya kasance mai girma akalla 4Gigabyte.
Rumbun Ajiya (Hard Disk Drive): Wannan shi ne wajan da ake adana dukkan aiyuka, manhajojin aiki, manhajara sarrafa naâura ma acikin sa ta ke da sauran abubuwan da ake iya adanawa a Computer. Shi ma girmansa yana taka muhimmiyar rawa wajan siyan Computer. A shekarar 2014 aka samar da sabon samfurin rumbu ajiya na musamman mai suna Solid state. Ya bambanta da na asali kamar haka; Saurin aiki da kuma kasancewar sa babu tarkace masu motsi a cikinsa kamar na asali. Amma kuma yanada matukar tsada sosai. Anan mutum zai iya siyan kamar 320GB, 500GB, 650GB, 750GB ko 1Terrabyte.
Injin Sarrafa Hoto (Graphics Card): Wannan ma yanada matukar faâida, saboda shi ne jigo wajan sarrafawa da tace hoto da bidiyo a Computer domin bada ingantaccen hoto a manunar Computer (Display). haka kuma akwai manhajoji wadanda aikinsu ya dogara ga ingancin hoto ko bidiyo domin samun cikakken sakamakon aikin su Misali HD Videos da Advance Games. An fi samun na musamman masu inganci fiye da wadanda s**a zo a cikin Computer. Sai dai tasada sosai kuma an hada su da Computer ta hanyar USB ko kuma Hanyar karawa Computer sassa na musamman (expansion slot).
Manhajar sarrafawa (Operating System): Kusan kaso tamanin (80%) na kwamfutoci da ake aiki dasu aduniya suna amfani da manhajar sarrafa Computer na kamfanin Microsoft, wato Windows. Wasu lokutan akan siyar da Computer da windows akan ta, haka zalika akn siyar da su babu windows akan su. Sai dai mutum ya zabi irin wanda yake so domin a saka masa ko ya ska da kansa. A halin yanzu windows mafi dacewa akan Computer shine windows 10 ko kuma windows 8.1. Sannan kuma akwai sabon fitowa wato Windows 11.
Wadannan abubuwa sune s**a fi dacewa da ayi laâakari da su a duk lokacin da aka tashi siyan Computer. lawi
16/01/2024
Sana arka mutuncinka
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Website
Address
Kano