FC Barcelona Hausa

FC Barcelona Hausa

Share

Visca Barça ❤️❤️❤️

26/05/2026

🚨 LABARAI 8 NA YAU A MINTI 1 — BARÇA NA MOTSI! 🔵🔴🔥

‎🚨🔵🔴 Yau labarai 8 sun zo a dunƙule! Transfers, kyaututtuka, da motsin kulob ɗin da ya lashe La Liga! Duba duk abin da ke faruwa a Barça yau! 👇🎥

26/05/2026


‎🚨 Atlético Madrid kwanakin bayan sun tuntuɓi Laporta akan Marc Casadó 👀

‎Diego Simeone na matuƙar son ɗan wasan. Saboda salon Casadó da ƙimar shi, yasa mai horarwar yayi magana dashi ta kai tsaye domin ya gamsar dashi akan tsarin shi na Athletico Madrid.

‎Amma, abinda ɗan wasan yafi baiwa fifiko bai taɓa canjawa ba:

‎Marc Casadó yana son yin nasara a Barcelona, ƙungiyar shi tun yarinta.

‎[🗞️Diario Sport]

👇 Marc Casadó: A siyar, aro, ko a ajiye? 🔵🔴

‎🤝 Kungiyoyin Premier League da Saudi Arabia, what na biɗa, me Barça zata yi? 🤔

26/05/2026

🚨🇪🇸 Spain ta yi watsi da ‘yan wasan Real Madrid gaba ɗaya domin World Cup. 😭⚪❌

Luis de la Fuente ya kalli Dean Huijsen, Raúl Asencio, Álvaro Carreras, Dani Carvajal, Fran García da Gonzalo García… sannan ya yanke shawarar cewa gara ya buga da mutum 10 maimakon ya ɗauke su zuwa World Cup. 🤡💀

Wannan zaɓin dai ya girgiza magoya bayan Madrid sosai. 👀🔥

Ƙwallo ba suna ba ne kawai… dole ne ka nuna cewa ka cancanta a fili. 😭🇪🇸

26/05/2026

‎🔥🇪🇸 Tauraron Barça Ebrima Tunkara ya yi wani abin al’ajabi tare da Spain U17 a wasan da s**a buga da Estonia U17 cikin mintuna 60 kacal. 🤯💎

‎⚽ Ƙwallo 1
‎🎯 Assist 2
‎✅ Ya samo penalty 1
‎🪄 Dama 10 ya ƙirƙira
‎🔥 Yayi yanka 4 masu nasara
‎💪 Yayi gumurzu 6 ya yi nasara
‎🎯 Raba ƙwallo 19 da s**a kai inda ake so
‎📌 Ya haɗo ƙwallo 4 masu inganci
‎❌ Ba a ƙwace masa ƙwallo ko sau ɗaya ba 😳

‎Wannan ba ƙoƙari ba ne kawai… saƙo ne daga wani ɗan baiwa na musamman. 🌟❤️💙

‎Ebrima Tunkara na nuna alamun cewa wani babban tauraro na tasowa a La Masia. 👀🔥

‎Ana cewa, dashi Flick zai yi shirye shiryen shiga sabuwar wasanni mai zuwa


26/05/2026

‎😔 Gerard Martín bayan an gaza saka sunan shi a jerin masu buga WORLD CUP:

‎🗣️ “Na so buga gasar World Cup. Da rana (Lokacin da ake faɗar suna) ina kallon TV domin ganin ko akwai wata ƙaramar dama, amma a ƙarshe babu...” 💔

‎🗣️ “Na san akwai yiwuwar hakan, amma abu ne mai wahala sosai.”

‎🗣️ “A ƙarshe dai ba a rubuta hakan a gare ni ba. Amma lokaci na gaba, in sha Allah zan kasance a can.” 🌍💪

‎Wannan ita ce ƙwallo… wani lokaci mafarki yana kusa cika, amma wani lokaci bai cika ba. 😔

‎Amma yadda Gerard Martín ya nuna ƙarfin zuciya da juriya yana nuna cewa bai sare ba tukuna. 🔥❤️💙

25/05/2026

❤️‍🩹 Shin Tsakanin Gerard Martin da Huijsen wanene yafi wani cancantar zuwa World Cup bayan kakar wasan da s**a yi amma basu je ba?

Ka manta da Madrid ko Barça suke!

25/05/2026

🚨 Yanzu Yanzu: Héctor Fort ya dawo cibiyar horaswar Barcelona yau bayan kammala zaman aron da ya yi. 🔵🔴

Matashin ɗan wasan zai shiga tawagar farko domin shirye-shiryen kakar wasa mai zuwa, inda zai yi ƙoƙarin burge Hansi Flick kafin sabon kakar wasa ta fara. ✅🔥

Wata babbar dama ce gare shi domin nuna cewa ya shirya domin mataki na gaba a Barça. 👀💫

Flick dai na ci gaba da bai wa matasan La Masia dama sosai. ❤️💙

Shin kuna son ganin Hector Fort a Barça baɗi?

25/05/2026

🚨📸 | Rigar Barça guda huɗu ta kakar wasa mai zuwa.

A
B
C
D

Wacce ce tafi kyau?

[memorabilia1899]

25/05/2026

Abokina har ƙasa saida ya canja amma duk da haka bai samu gurbin buga World Cup ba 😂

25/05/2026

Ba wanda zai taɓa Lamine Yamal a Spain, koch ɗin Spain bai ɗau mataki akan shi ba.

Negreira na aiki 😂😂😂

25/05/2026

‎🚨 A hukumance: BARÇA ta cike tawagar Spain, an bar Real Madrid na cizon yatsa a WORLD CUP! 🇪🇸🏆

‎Hakan na zuwa ne bayan Joan García, Eric García, Pau Cubarsí, Gavi, Pedri, Dani Olmo, Ferran Torres, da Lamine Yamal sunan su ya bayyana a cikin sunayen tawagar kasar Spain ta kofin duniya na 2026 watau World Cup!

‎Dole mu taya Barça murna! 👏

‎🚨🇪🇸 To saidai kuma Dean Huijsen da Dani Carvajal basu samu shiga cikin tawagar ta ƙasar Spain ba a World Cup squad inda babu ɗan wasa ko ɗaya faga Real Madrid a ciki. ❌

‎A ɗauka cewa Spain ta gayyaci Dean Huijsen da Dani Carvajal cikin tawagar tasu, babu yadda za'a yi ƴan Real Madrid saboda mutum biyu su goya mana baya da ƴan wasa 8 a ciki. Duk wasan Spain adawa zasuyi da ƙasar

‎Saboda haka, gwanda haka, a zuba adawar da gaske ba wani waye waye...

‎⏳Fatan alkairi ƙasar Spain da Argentina

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Diso, Gwale LG
Kano
700103