Mal. Salisu M. Dahiru Guri

Mal. Salisu M. Dahiru Guri

Share

Da’awah TV dedicated to Mal Salisu M. Dahiru Guri. Tafseer TV

07/05/2026

Assalamu alaikum
Muna masu bawa al'umma hakuri yau karatun littafin sharhu aqeedati ahlissunnati waljama'a littafin ibn uthaimin bazai samu ba sakamakon wani uzuri sai sati mai zuwa in allah ya kaimu wadda ya gani yasanar da wadda bai gani ba

Photos from Mal. Salisu M. Dahiru Guri's post 18/03/2026

Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Alhamdulillah, muna gode wa Allah da Ya ba mu ikon fara wannan tafsiri kuma muka kammala. Muna roƙonSa Ya karɓi ibadunmu, Ya yafe mana kurakuranmu.
Ya ku ‘yan uwa, kada mu bauta wa Allah a Ramadan kawai, mu ci gaba da abin da muka koya—tsoron Allah, haƙuri da nisantar sabo.
Idan Allah Ya kaimu, za mu sake haɗuwa a badi. Idan ba mu kai ba, Allah Ya haɗa mu a Aljanna.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Photos from Mal. Salisu M. Dahiru Guri's post 08/03/2026

Hotuna|| Daga Darasin Tafsir Al-Qur'ani Na Yau asabat 18 Ga Watan Ramadan 1447, A Masallacin ibn Taimiyya dake unguwar kandaharKaramarHukumarGurilocalgovt jigawa state ).

Allah Yakarbi Ibadun Mu, Allah Yasa Mu Wanye Lafiya🙏

Photos from Mal. Salisu M. Dahiru Guri's post 04/03/2026

Hotuna|| Daga Darasin Tafsir Al-Qur'ani Na Yau laraba 15 Ga Watan Ramadan 1447, A Masallacin ibn Taimiyya dake unguwar kandaharKaramarHukumarGurilocalgovt jigawa state ).

Allah Yakarbi Ibadun Mu, Allah Yasa Mu Wanye Lafiya🙏

02/03/2026

Assalamu alaikum
Sakamakon wani uzuri daya taso yau babu Tafsirin Alqur’ani da malan yaka Gabatarwa a masjid ibn Taimiyya Guri sai Gobe in allah ya kaimu.

Wadda ya gani yasanar da wadda bai gani ba

Photos from Mal. Salisu M. Dahiru Guri's post 28/02/2026

Hotuna|| Daga Darasin Tafsir Al-Qur'ani Na Yau Asabar 11 Ga Watan Ramadan 1447, A Masallacin ibn Taimiyya dake unguwar kandaharKaramarHukumarGurilocalgovt jigawa state ).

Allah Yakarbi Ibadun Mu, Allah Yasa Mu Wanye Lafiya🙏

Photos from Mal. Salisu M. Dahiru Guri's post 21/02/2026

Yayin bude tafsir na watan Ramadan wadda ake gabatarwa duk shekara daga masjid ibn Taimiyya Guri

17/02/2026

Assalamu alaikum
SANARWA
Majlis na Ibn Taimiyya dake unguwar Kandahar, ƙaramar hukumar Guri, na sanar da al’umma cewa In shā Allah za a fara Tafsirin watan Ramadan ranar Asabar.
Tafsirin zai gudana ne karkashin jagorancin:
Sheikh Salisu M. Dahiru – Guri
Alaramma Lawan – Guri
🗓 Rana: Asabar
⏰ Lokaci: 05:10pm – 06:10pm
📍 Wuri: Majlis Ibn Taimiyya, Unguwar Kandahar, Guri LGA
Ana kira ga daukacin al’umma da su halarta domin amfana da karatun.
Allah Ya sa mu dace, Ya karɓa mana, Ameen.
Sanarwa daga: Media Team
Majlis Ibn Taimiyya

03/01/2026

Guzurin safiya

Ka aikata alheri ba tare da jiran sakamako ba, domin lada yana zuwa ne a lokacin da ya fi dacewa—kuma sau da yawa ta hanya mafi alheri fiye da yadda ka zata.

Mal. Salisu M. Dahiru Guri

02/01/2026

Barka da Juma’a.
Rana ce da take tunasar da mu cewa lokaci na wucewa, amma hisabi na zuwa.
Abin da muka aikata jiya ya wuce, amma yau dama ce ta gyara kuskure.
Mu tuba, mu kyautata, mu kusanci Allah kafin lokaci ya kure.
Mai hankali shi ne wanda ya ribaci wannan rana mai albarka.
Allah Ya sa mu kasance cikin masu anfani. Ameen.

Mal. Salisu M. Dahiru Guri

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Guri LGA
Kano