Muryar Wasanni

Muryar Wasanni

Share

Muryar Wasanni Jaridace ta wasanni dake zagaye fadin duniya don kawomuku labarai a duniyar kwallon kafa cikin harshen hausa, Tik-Tok, Facebook da ma you tube.

29/05/2026

🗞LABARI💥Atlético Madrid sun yi wara magana kan Barcelona dangane da sha'awarsu ga ɗan wasan gaba Julián Álvarez ta hanyar wallafa wasu zafafan tayi na barkwanci ga taurarin Barça Lamine Yamal, Pedri da Raphinha a kafofin sada zumunta. Follow Muryar Wasanni

Wani rahoto a ranar Alhamis yana cewa Barça suna fatan sanya hannu kan Álvarez, bayan sun hadu da wakilan dan wasan na ƙasa da ƙasa na Argentina kuma sun ji cewa dan wasan ya fi son shiga cikinsu fiye da wasu zaɓuɓɓuka kamar Paris Saint-Germain da Arsenal.

Atlentico dai sunce babu wani abu makamancin haka game da zawarcin Alvarez inda suke bayanin cewa Barcelona sun fiya yada karya.

29/05/2026

🗞LABARI💥 Anthony Gordon yayi jawabi kan sanya hannu da Barcelona. “Na gano daga baya a Barca cewa suna sona amma da zaran na san Barca hanya ce mai muhimmanci, babu wata tambaya. Kullum ina son Barca. Ita ce kulob mafi girma a duniya. Shigarta abu ne da na yi mafarki a kai tun ina yaro.” Follow Muryar Wasanni

Gordon kuma yana iya amsa wasu tambayoyi a cikin Sifaniyanci yayin bikin bayyana shi.🇪🇸

29/05/2026

LABARI 💥 Anthony Gordon ya rattaba hannu na shekara 5 a Barcelona bayan kammala komawar shi ƙungiyar akan kuɗi yuro million 80.

29/05/2026

LABARI 💥 Hukumar UEFA ta tabbatar da cewa filin wasan Como da ke gasar Seria A bai cika ƙa’idojin UEFA ba.

Dan haka Cesc Fabregas da tawagarsa ba za su buga wasanninsu na gida a filinsu ba a gasar Champions League ta kakar wasa mai zuwa.

A maimakon haka, za su riƙa buga wasannin su na gida a filin wasan Sassuolo. Follow Muryar Wasanni

29/05/2026

LABARI 💥 Ederson yana amsan fam dubu 45 duk sati a Atalanta,,yayin da yanzu idan ya je Manchester kuɗin zai ƙaru zuwa fam dubu 75 duk sati. Follow Muryar Wasanni

29/05/2026

🗞LABARI💥Real Madrid, Bayern Munich, da Chelsea duk suna sha'awar daukar Ibrahima Konate. Follow Muryar Wasanni

29/05/2026

🗞LABARI💥 Ana zatom Ibrahima Konate zai bar Liverpool a bazararnan inda zai zama dan wasa na kyauta. Follow Muryar Wasanni

29/05/2026

🗞LABARI💥Eric Djemba-Djemba ya ce yakamata a soke tarihin bada taimakon cin kwallaye 21 na Bruno Fernandes bayan bidiyo ya nuna cewa kwallon da Patrick Dorgu ya ci wa Man Utd ta fito ne daga mai tsaron ragar Brighton, Bart Verbruggen. Follow Muryar Wasanni

Yana mai cewa "Ina ganin yakamata a soke ta Za ka iya gani a fili abin da ya faru "Ƙwallon ba ta tsallaka layin yadda ya kamata ba kuma ta dawo daga mai tsaron ragar zuwa cikin raga. A ra'ayina, ya kamata su cire shi. Idan dokoki dokoki ne, to bai kamata a ƙirga shi a matsayin taimako ba."

Me kuke ganin yasa yace haka ?

28/05/2026

LABARI 💥 Brazil ta tabbatar da cewa Neymar bai ɗau horo da tawagar jiya ba, sai dai ya je asibiti domin yin gwaji wajen likita. Follow Muryar Wasanni

28/05/2026

🗞LABARI💥 Bankin Scotland sun fitar da takardar kudi na £20 mai hoton Scott McTominay a bugu na musamman 💷. Follow Muryar Wasanni

An nuna shahararren bugun ƙafarsa a sama a karawa da Denmark, wanda ya taimaka wajen jagorantar su zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

26/05/2026

🗞LABARI💥Manchester United sun tabbatar da nadin Michael Carrick a matsayin sabon kocinsu na dindindin. Follow Muryar Wasanni

Carrick daga matsayin mai rikon kwarya a watan Janairu zuwa yanzu ya tabbatar da qwarewarsa da fikirarsa.

Kuna ganin zai iya lashe premier league a kaka mai zuwa ?

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Address


Kano