AMC Hausa

AMC Hausa

Share

Kafa ce da zata rika kawo sahihan Labarai cikin harshen Hausa +2349036516556

Photos from AMC Hausa's post 13/07/2026

Ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da mataimakinsa, Mustapha Rabi'u Kwankwaso, tare da shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kano, Hussaini Isa Mai Riga, sun kai wa Sanatan Kano ta tsakiya, Rufa'i Sani Hanga ziyara a gidansa dake Kano.

Daga jiya Lahadi zuwa yau Litinin ana ta yaɗa jita-jitar cewa Sanata Hanga ka iya ficewa daga jam’iyyar NDC zuwa APC.

📷 Hamza Ahmad Telan Mata

13/07/2026

Gwamnan ya ayyana mataimakinsa, Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin wanda zai sake takara tare da shi a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ranar Litinin.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron dabarun siyasa da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja, wanda ya haɗa da manyan jami'an gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon:
Biyayya da Jajircewa: Irin ƙwazon da Garo ya nuna tun bayan hawansu mulki.
Haɗin Kai: Gamsuwarsa da yadda suke gudanar da ayyukan jihar cikin ƙwarewa da amana.
Ci Gaban Jiha: Gudummawar da mataimakin yake bayarwa wajen ciyar da Kano gaba.

"Ina mai tabbatar muku cewa ban yi nadamar zaɓen Garo a matsayin mataimakina ba, Ina da cikakkiyar amincewa da shi," in ji Gwamna Yusuf.

Daga ƙarshe, gwamnan ya yi kira ga shugabannin jam'iyya da magoya bayansa da su ƙara haɗin kai domin tunkarar babban zaɓen na 2027 da kuma dorewar nasarorin da gwamnatinsa ta fuskanta.

13/07/2026

A yau 13 ga watan Yuli tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ke cika shekara 1 da rasuwa.

Shin da me kuke tuna Shugaban..?

13/07/2026

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS), reshen Jihar Kano, ta sanar da cewa fursunoni guda 61 a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa sun yi nasarar sauke Alƙur'ani Mai Tsarki, a gudanar da wani shiri na gyaran hali da koyar da addini.

A cikin wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar, ya bayyana cewa waɗanda s**a kammala karatun sun haɗa da maza 55 da mata 6.

"Wannan shiri na ɗaya daga cikin manyan dabarun gidan gyaran hali da muke amfani da su domin dawo da mutum cikin hayyacinsa kafin ya koma cikin al'umma," in ji sanarwar.

12/07/2026

Wata jaridar masu ra'ayin mazan jiya a Iran mai suna Hamshahri ta wallafa jerin sunayen wasu fitattun shugabannin duniya da ta ce suna cikin waɗanda za a ɗauki fansa a kansu sakamakon kisan tsohon Jagoran Addini na Iran, Ayatullah Ali Khamenei.

Rahotanni sun ce Ali Khamenei ya rasu ne bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila s**a kai a ranar 28 ga Fabrairu, wadda ita ce ranar farko ta yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansa, inda a saƙonsa na farko bayan jana'izar mahaifinsa ya ce, "Ɗaukar fansa shi ne muradin al'ummarmu, kuma dole ne a aiwatar da shi."

Ya kuma ce waɗanda sunayensu ke cikin jerin ba za su samu mutuwar lumana ba.

Jaridar Hamshahri, wadda hukumomin birnin Tehran ke bugawa, ta fitar da hotunan shugabannin ƙasashe 13 tare da saƙon Mojtaba Khamenei. Sai dai sabon jagoran bai bayyana sunayen mutanen da Iran ta ce ta sanya a cikin jerin ba, kuma babu wata shaida da ke nuna cewa gwamnatin Iran ta amince da jerin sunayen da jaridar ta wallafa.

Daga cikin waɗanda ke cikin jerin akwai Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Firaministan Birtaniya Keir Starmer, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Firaministar Italiya Giorgia Meloni da kuma shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz.

A lokacin yaƙin, Iran ta zargi wasu ƙasashen Turai da kin yin Allah wadai da hare-haren da aka kai mata, tare da zarginsu da bai wa jiragen sojin Amurka damar amfani da sararin samansu.

Rahotanni sun kuma ce Mojtaba Khamenei bai fito bainar jama'a ba tun kafin fara yaƙin, kuma an ce ya samu raunuka a hare-haren da s**a kashe mahaifinsa.

12/07/2026

Gwamnatin tarayya ta amince da ƙara kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO zuwa Naira 50,000 ga kowanne ɗalibi, kuma sabon tsarin zai fara aiki daga jarabawar shekarar 2027.

Sabon kuɗin ya nuna ƙarin kusan kashi 82 cikin 100 idan aka kwatanta da kuɗin rajista na yanzu da ya kai Naira 27,500.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Ilimin Sakandare na Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya, Adeniji Ibrahim, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da Ministan Ilimi ya yi da hukumomin shirya jarabawa a ranar 31 ga Maris, 2026.

Sanarwar ta ce a taron an tattauna bukatar sake duba kuɗin gudanar da jarabawar, inda Ministan Ilimi ya umarci WAEC da NECO su fara amfani da kuɗin rajista iri ɗaya wajen gudanar da jarabawar kammala sakandare (SSCE).

Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a ta Ma'aikatar Ilimi, Folasade Boriowo, ta tabbatar da sahihancin matakin, tana mai cewa gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kuɗin rajistar.

12/07/2026

Sunan Muhammad ya ci gaba da kasancewa zakara a matsayin sunan da aka fi sanya wa jarirai maza a Ingila da Wales har na tsawon shekaru uku a jere, bayan da kusan yara maza 6,000 s**a amsa sunan a shekarar 2025.

Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Birtaniya (ONS) ta fitar sun nuna cewa sunan 'Noah' ne ya zo na biyu, inda tazarar da ke tsakaninsa da sunan Muhammad ta ƙaru da kusan jarirai 2,000.

12/07/2026

Jam'iyyar APC ta gudanar da taron masu ruwa da tsakinta a Ƙaramar Hukumar Nassarawa da ke jihar Kano domin ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar da shirye-shiryen zaɓen 2027.

Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa kan Yaɗa Labarai, Hassan Shehu Adam Twins, ya fitar.

Taron ya samu halartar shugabannin jam'iyyar, kwamishinoni, masu ba da shawara, masu riƙe da muƙaman gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki daga Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

12/07/2026

Sakataren Majalisar Masarautar Gumel, Alhaji Murtala Aliyu Muhammad, ya ce, an gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na gidauniyar Masarautar Gumel, inda aka gabatar da muhimman jawabai kan ilimi, harkokin lafiya da sauran batutuwan da s**a shafi ci gaban al'umma.

Yayin taron bitar an yi kira ga iyaye su ƙara sanya ido kan ilimin 'ya'yansu domin bunƙasa ilimi da kuma dacewa da fasahar zamani.

Haka kuma, limamai da bulamai sun gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya mai ɗorewa ga Masarautar Gumel da Jihar Jigawa baki ɗaya.

12/07/2026

Jam’iyyar APC ta sanar da kammala tura dukkan sunayen ’yan takararta 471 zuwa tsarin rajistar ’yan takara na Hukumar zaɓen Nijeriya INEC, ciki har da Shugaba Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027.

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce yanzu hankalin jam’iyyar ya koma kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe da kuma samun nasara a babban zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce jerin sunayen ya ƙunshi ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa, ’yan takarar Sanata 109 da kuma ‘yan takarar Majalisar Wakilai 360, bayan cikar wa’adin da INEC ta kayyade.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Kano