Anyi sulhu tsakanin Sanata Barau da Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a Abuja.
Amon Gaskiya
Kafa ce da zata rika kawo sahihan Labarai cikin harshen Hausa 08028934564
12/05/2026
Sanatar Kogi ta tsakiya Sanata Natasha ta mayar da fom dinta na tsayawa takara sanatan Kogi ta tsakiya a jam'iyar PDP.
09/05/2026
Jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi sun isa wurin taron kasa na jam’iyyar Nigerian Democratic Congress NDC, da ke gudana a Angeles Event Centre and Mall da ke Abuja.
Manyan ’yan siyasa, magoya baya da shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na Nijeriya ne s**a hallara domin gudanar da taron wanda ake sa ran zai tattauna kan makomar jam’iyyar da kuma shirye-shiryen zaɓen 2027.
Malam Ibrahim Khalil ya musabta rahotan fitarsa daga jami'ar ADC.
Comrd Adamu Abdullahi karkasara yayi Allah wadai da kisan da wasu bata gari s**aiwa wasu matasa anan Kano, ya kuma kira ga Gwamnati da ta dauki mataki.
Wata sabuwar wuta ta taso a siyasar jihar Jigawa.
03/05/2026
A taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa,domin fitar da ɗan takarar majalisar jiha, Ahmed Speaker ya samu goyon bayan mutane 8, yayin da Hon.Sale Marke dan Majalaisa mai ci bai samu ko mutum ɗaya ba. Haka kuma, mutum huɗu sun zaɓi kasancewa ba tare da nuna goyon baya ga kowa ba.
03/05/2026
Shugaban karamar hukumar Ghari Hon. Hashimu Garba (Mai Sabulu), ya bude asibiti da makaranta a Garin Hugungumai domin inganta lafiya da cigaban ilimi a yankin.
Al'ummar Garin Hugungumai, sun nuna farin cikin su da Asibiti da Makaranta da shugaban karamar hukumar Ghari yayi musu, wanda a baya basu da asibiti sai da zuwa Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu da ya kawo musu, al'ummar Garin sun yiwa shugaban addu'a da fatan gamawa lafiya da cigaba mai dorewa.
Anasa bangaran, Mai Sabulu ya nuna farin cikinsa da tarba mai kyau da ya samu daga al'ummar Garin, bisa wannan gagarumin aiki da yayi musu.
Musa mai Sana'a yaiwa Ali Jita Kakkausan martani kan kin amsa goron gayyata zuwa zauren jita.
Sabon rikici ya barke tsakanin Ali Jita da Musa mai Sana'a.
Kungiyar Voice of Kano North ta akinci da Sanata Barau ya cigaba da wakiltar su a zauren majalissar Dattawa.
Click here to claim your Sponsored Listing.