Football Priority Hausa

Football Priority Hausa

Share

-Football Priority Hausa⚽
-Labaran ƙwallo 🗣
-Hausa football community 📩

02/06/2026

An yi wa tawagar Brazil gaisuwar karramawa da feshin ruwa (water cannon salute) a lokacin da suke barin ƙasar Brazil da kuma lokacin da s**a shiga ƙasar Amurka. Domin fafutukar neman lashe kofinsu na shida na Gasar Cin Kofin Duniya 💪🇧🇷

02/06/2026

Irin gagarumin ayarin motocin da kasar Turkiyya (Türkiye) ta shirya lokacin da motar 'yan wasan kungiyar take kan hanyar zuwa filin jirgin sama, yayin da suke shirin fara tafiyarsu ta gasar cin kofin duniya 🇹🇷

Hanyar bankwana mai ban mamaki da ban sha'awa da aka yi musu 😍

02/06/2026

IBRAHIMA KONATE YANA SHIRIN KOMAWA REAL MADRID DA ZARAR AN SAKE ZABEN PEREZ!

An cimma matsaya baki da baki ta sa hannu na Shekaru huɗu ga dan wasan mai tsaron baya (centre back) yayin da Madrid ta kunna zabin sayensa tun bayan da ya bar Liverpool a makon da ya gabata.

Konaté ya dakatar da tayin da yake samu daga kungiyoyin gasar Saudi League domin jiran Real Madrid.
Idan har an sake zaben Florentino Pérez, Konaté zai sanya hannu a kwangilar.

01/06/2026

Davide Ancelotti shi ne sabon babban kocin kungiyar Lille. Dan kasar Italiyan ya maye gurbin Bruno Genesio, kuma ya sanya hannu a kan kwangilar shekaru biyu. Wannan zai kasance karo na farko da zai fito a matsayin babban kocin kungiya a nahiyar Turai, a wani kulob da zai fafata a sabon tsarin rukunoni (league phase) na gasar zakarun Turai (Champions League) mai zuwa.

01/06/2026

Hukumar FIFA ta tabbatar da cewa za ta hana ƙaryar da masu tsaron raga (goalkeepers) ke yi na samun rauni domin samun lokacin tattaunawa akan dabarun wasa (tactical timeouts) a gasar cin kofin duniya ta 2026.

Daga yanzu, ba za a sake barin 'yan wasa su rika zuwa wajen benci domin karbar umarni ko dabarun wasa daga wajen kocinsu ba idan mai tsaron raga ya fadi da sunan ya ji rauni.

31/05/2026

Rundunar 'Yan Sandan London (Metropolitan Police) ta tabbatar da cewa taron murnar bikin nasarar Arsenal shi ne mafi girma a hukumance a tarihin jerin gwano na taron biki a Birtaniya!

🔹 Kididdigar farko ta nuna cewa mafi ƙarancin mutanen da s**a halarci taron sun kai Dubu 800,000.

🔹 Jimillar yawan jama'ar ta wuce duk yadda ake tsammani, inda ta zarce masoya miliyan 1.5!

An kwashe sa'o'i 2.5 ana gudanar da bukukuwan murnar.

[TelegraphFootball]

30/05/2026

Mikel Arteta ya ce ya zauna ya sake kallon dukkan bugun fanareti (penalty) da aka bayar a gasar zakarun Turai (Champions League) ta wannan kakar.

Kocin na Arsenal bai ji dadin hukuncin da alkalin wasa ya yanke ba na rashin basu fanareti bayan da Noni Madueke ya fadi a cikin akwatin raga (box) a lokacin kararin lokaci (extra-time).

30/05/2026

Kai Havertz ya zura kwallon da ta kawo nasarar lashe kofi a:

✅ Lokacin da Chelsea ta lashe kofin zakarun Turai (Champions League).

✅ Lokacin da Chelsea ta lashe kofin duniya na kungiyoyi (Club World Cup).

✅ Lokacin da Arsenal ta lashe kofin gasar Premier League.

Kuma yanzu haka ya sake zura kwallo a raga tun kafin mintuna 5 su cika a wasan karshe na gasar zakarun Turai (Champions League final).

Mutum ne shi da aka sani gurin nuna bajinta a manyan wasanni 👏

30/05/2026

Kai Havertz ya saka Arsenal a Gaba mintuna 6 da Fara wasa.

Arsenal ta fara jiyo Ƙamshin Kofin Zakarun Turai

30/05/2026

Barcelona tana bukatar ta riƙe Marcus Rashford duk da cewa ta sayi Anthony Gordon.

Kamar yadda ESPN ta rawaito, kulob din yana da niyyar sake tattaunawa akan sharuddan yarjejeniyar cinikin da kungiyar Manchester United. 👀💰

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Kano