Zagayen wasanni

Zagayen wasanni

Share

⚽ Zagayan Wasanni
Labaran ƙwallon kafa na gida & waje
Sakamako • Transfer • Nazari
Ku biyo mu don sabbin labarai ⚽🔥

05/12/2025

Good

09/09/2025

[⚠️] Yanzu Yanzu : Rikicin dake tsakanin masu shirya Ballon D’Or da Real Madrid har yanzu yana da tsanani 🔥

Bayan bidiyoyin rashin girmamawa da aka nuna game da Vini Jr da yin dariya da shi, har yanzu ba a bayar da uzuri ba. An aika wata tawaga daga Faransa zuwa Madrid don ganawa domin samo mafita, amma taron ya kare a cikin yanayi mara kyau.

(MARCA)

Kuyi following domin samun wasu labaran

09/09/2025

🚨✔️ KURUNKUS: MAFARKIN SZOBOSZLAI YA CIKA AKAN CRISTIANO RONALDO.......

Wani labari mai ban mamaki a duniyar ƙwallon ƙafa… Mafarki ya zama gaskiya.

📆9 ga Satumba, 2009 — Hungary vs Portugal

Dominik Szoboszlai ya shiga filin wasa tare da ‘yan wasan Portuga matsayin yaro da ake riƙe hannunsu...

🗣️Dominik Szoboszlai a 2022:

“Lokacin da nake shekara 8 kuma wasan Hungary da Portugal za'a buga a filin Puskás Arena, na shiga filin tare da ‘yan wasan Portugal Na tsaya a kusa da shi mutane uku kacal ne tsakani na da Cristiano Ronaldo Wannan shi ne mafi kusa da na taɓa zuwa wajen ganinsa, amma ina fata na kusanci shi watarana fiye da haka.”

📆9 ga Satumba, 2025 — Hungary vs Portugal yau Kenan

A Yau, bayan shekaru 16, Dominik Szoboszlai zai shiga filin wasa a matsayin kyaftin ɗin ƙungiyar ƙasa ta Hungary sannan zai sake saduwa da gwarzon sa kuma kyaftin ɗin Portugal, Cristiano Ronaldo 🤯❤️

🗣️Dominik Szoboszlai kan fuskantar Cristiano:
“Na shaida da kaina Ya faru daidai shekaru 16 da s**a wuce. Ina tuna shi sosai. Har yanzu ina tuna yadda na ji a lokacin.

Na taɓa buga wasa da manyan ‘yan wasa, amma ban taɓa buga wasa da shi ba Cristiano Ronaldo shi ne gwarzon da nake kallo tun ina yaro Yanzu za mu zama abokan hamayya, kuma ina fatan ya sanya wannan wasa ta zama abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba.” inji Szoboszlai

🗽Yakuke ganin batun dan wasan???


29/01/2025

Domin Real Madrid ta fita a sahun 8 ɗin farko, dole sai waɗannan abubuwan sun faru:

• Su samu nasara akan Brest da ƙwallaye 3 ko sama da haka.

• Ayi canjaras tsakanin Lille da Feynoord

• A yi canjaras ko rashin nasara tsakanin Monaco da Inter

• Barcelona ta samu nasara akan Atlanta.

• Rashin nasara tsakanin Aston Villa da Celtic.

• Kada Bayern Munich ta samu nasara da sama da ƙwallaye 2 ko Leverkusen ta yi rashin nasara.

• Real Madrid C.F.

27/01/2025

|🚨✅| Shugaban kungiya mafi girma a tarihin kwallon kafa!!!
📝 An sake zabar shugaban Real Madrid na yanzu, Florentino Perez na tsawon shekaru hudu bisa tsarin yarjejeniya. Ba tare da abokin hamayya ba, ganawar da ta tabbatar da nasarar da Pérez ya dauki tsawon mintuna 29 ana yi. 🇪🇸👑

🏆 Florentino ya lashe kofuna 38 a Real Madrid a matsayi na biyu a matsayin shugaban kungiyar (2000 har zuwa 2006 da 2009 har zuwa yau).

🥇 A cikin 2024, ya sami kyautar Globe Soccer Award don mafi kyawun shugaban kowane lokaci (G. O. A. T).

🍫Maki nawa zakubawa Perez daga 1 zuwa 100??






27/01/2025

Kocin Real madrid yace wannan shine Mbappe din da muka sani ...
Kara da cewa dama na fada muku ku kara masa lokaci.






Photos from Zagayen wasanni's post 11/10/2023

Hazard mai shekara 32 ya jingine takalmansa bayan shekara 16 yana murza leda a matsayin ƙwararren ɗan wasa, kamar yadda ya bayyana.

Da me za ku fi tunawa da ɗan ƙwallon?

10/10/2023

A shekaru 35

• Zidane ya yi ritaya ⠀
• Ronaldo ya yi ritaya
• Kaka ya yi ritaya
• Ronaldinho ba shi da kungiya
• Xavi ya buga wa Al Sadd wasa
• Henry ya taka leda a NewYork RB
• Pelé ya buga wa NY Cosmos wasa
• Messi ya bugawa Inter Miami wasa

• Cristiano Ronaldo ya mamaye hazakar Juventus gun Lashe gasar Serie A.

10/10/2023

"Lionel Messi da Neymar a kodayaushe sune ababen koyina Kuma abin tunani na," in ji Bryan Zaragoza, Bayan ya zazzaga Kwallaye 2 a ragar Barcelona.

©️ Zagayen wasanni

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address

Kano
700252