22/05/2026
Falalar Sallar Juma’a da Salatin Annabi ﷺ 🤍🕌
“Juma’a rana ce mafi alkhairi a wajen Allah. A cikinta akwai sa’ar da addu’ar bawa ba ta ƙin karɓuwa. Ku yawaita salati ga Annabi ﷺ domin salatinmu na isa gare shi.” 🤲✨
اللهم صل وسلم على نبينا محمد ﷺ 💚
15/05/2026
“Allahumma salli ala Sayyidina Muhammad wa ala ali Sayyidina Muhammad, k**a sallaita ala Sayyidina Ibrahim wa ala ali Sayyidina Ibrahim, innaka Hamidum Majid.
Allah ka gafarta mana zunubanmu, ka yalwata mana arziki mai albarka, ka sa mu dace duniya da lahira, ka biya mana bukatunmu na alheri. Ya Allah ka sanya wannan daren Jumu’a ya zama daren rahama, gafara da amsar addu’a. Ameen 🤲
Al Mansoor Dku ✍️😊
12/05/2026
Ga alamomi 5 da zaka gane mutane na gari ne kuma suna maka fatan alkhairi:
Suna farin ciki da nasararka
Mutum na kirki baya jin haushin cigabanka. Idan kayi nasara zaka ga yana taya ka murna da zuciya ɗaya.
Suna baka shawara mai anfani
Ko da gaskiya zata ɗaci, suna gaya maka domin gyaranka ba domin su wulakanta ka ba.
Suna tare da kai lokacin wahala
Ba lokacin dadi kawai zaka gansu ba. Idan kana cikin matsala zaka ga suna ƙoƙarin taimako ko kwantar maka da hankali.
Basu son gulma da cin amanar abota
Mutum na kirki baya tona sirrinka ko magana a bayanka domin ya bata maka suna.
Suna tuna maka da Allah da aikata alheri
Idan kana kusa dasu zaka ji kana samun ƙarin nutsuwa, tarbiyya, da tunanin aikata abu mai kyau.
Wani lokaci halayen mutanen dake kewaye da kai suna iya canza rayuwarka. Ka zaɓi abokai masu kyau kafin lokaci ya zaɓa maka marasa kyau.
Al Mansoor Dku 😊✍️
11/05/2026
ALAMOMI 10 DA MUTUM ZAI GANE ALLAH YA YARDA DASHI 🤲❤️
1. Idan zuciyarsa tana son ibada da kusanci da Allah.
2. Idan yake jin nadamar sabo kuma yana yawan tuba.
3. Idan Allah yana sa masa sauƙin aikata alheri.
4. Idan yana taimakon mutane ba tare da girman kai ba.
5. Idan zuciyarsa tana samun nutsuwa da ambaton Allah.
6. Idan yana gujewa zalunci da cutar da mutane.
7. Idan yake da kyakkyawar niyya a dukkan ayyukansa.
8. Idan yana son masu addini da zaman kirki.
9. Idan jarabawa tana ƙara kusantar dashi ga Allah, ba nesanta shi ba.
10. Idan ƙarshen ranarsa yana cikin alheri da tuna Allah.
“Allah baya kallon yawan dukiya ko sura, yana kallon zuciya da ayyuka.” 🤍
— Al Mansoor Dku✍️
Al Mansoor Dku 😊
11/05/2026
ALAMOMI 8 DA SUKE KAWO SAUKIN RAYUWA IN SHA ALLAH.
Na yi muku alkawari a group. Ga cikakken bayani:
1- Yawaita Istigfari: Istigfari yana buɗe ƙofofin arziki kuma yana kawo sauƙin rayuwa.
2- Sallar Dare : Ko raka’a 2 kacal bayan Isha, tana kawo nutsuwa da sauƙin damuwa.
3- Yawaita Sadaka: Sadaka ba ta rage dukiya, tana ƙara albarka da kariya daga musiba.
4- Kyautatawa Iyaye : Kyautatawa iyaye na daga manyan ƙofofin samun albarka a rayuwa.
5- Neman Ilimi : Allah yana ɗaukaka mai neman ilimi kuma yana masa sauƙi a rayuwa.
6- Yawaita Salati ga Annabi ﷺ 🥰: Salati yana gusar da damuwa kuma yana kawo rahamar Allah.
7- fadin “La hawla wa la quwwata illa billah” ✨
Taska ce daga taskokin Aljanna, tana ƙarfafa zuciya da rayuwa.
8- Yin kyakkyawan zato ga Allah : Allah yana tare da zaton bawansa, ka kyautata zato za ka ga alheri.
Allah ya sauƙaƙa mana rayuwa ameen
Rubuta Ameen a comment section Domin shiga cikin wannan addu'ar.
Kayi following na shafin nan domin karin tunatarwa kullum in Sha Allah
11/05/2026
Ka tsaya a matsayinda Allah ya ajiyeka
11/05/2026
ALKAWARIN ALLAH BAYA CHANZAWA YIN WMN RUBUTUN BAZAI RAGEMIN KOMAIBA A ABINDA NAKEJI AMMA INABUQATAR ADDU,ARKU🥹
Muddin karasa asalin abinda kakeso a rayuwarka to kullum kana tunanin bazaka qara samun mak**ancin wnn abunba Amma kasani Allah baya rabaka da wani abu face saiyyabaka Wanda yafishi kaide kawai ka dage da addu a kuma kayi hakuri in Sha Allah komai zai wuce
AMMA NIDE NASAN NAYI RASHIN MATA MARYAM BAIWAR ALLAH
MARYAM
-Mai hakuri
-Ga ilimi
-Ga sanin yak**ata
-Bawair Allah Bata girman Kai ko kadan
-class Daya muke tafini ilimi Amma ko ajinkinta Bata nuna hakan muna rayuwa da girmama juna Amma dayake Allah bai kaddara aure a tsakaninmuba warhaka tana gidan mijinta nikuma gani a nan 🥶 inata faman Shan wahala akan soyayyah
Bansan tanadinda ubangiji yaminba Amma Ina kyautata zaton k**ar yanda tamin addu a kan Allah yabani wacce tafita Ina roqon ubangiji da amshi addu arta allahuma Ameen 🤲🥹
Kuyimin adda a Allah yamin zabi na alkhairi 🤲🥹 zuciyata zafi take
✍️Al mansoor Dku 😊
Al Mansoor Dku 😊✍️
11/05/2026
Idan Ka Karanta Wannan Addu'ar Sau Uku Safe da Yamma Babu Abinda Zai Cutar Da Kai a wunin Yau inji manzon Allah s a w
👇
بِسمِ اللهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اِسْمِهِ شَيْءٌ فِي اْلأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السّّمِيعُ الْعَلِيمُ. (ثلاثاً)
follow👇
Al mansoor Dku 😊