22/12/2024
🔵✨ Maresca bayan antashi 0-0:
"Nayi farin ciki sosai, na gayawa 'yan wasan hakan, Nafi farin ciki fiye da wasan Brentford."
"Everton wasa ne mai wahala, filin wasa mai wahala, ƙungiya mai wahala, suna ɗaya daga cikin ƙungiyoyi biyar mafi kyawun tsaro a Turai ta bangaren Clean Sheets."
🔵✨ Maresca after 0-0 draw: “I’m very happy, I told this to the players. I’m more happy than the Brentford game”.
“Everton it’s tricky game, tricky stadium, tricky team, they’re one of the five best teams defensively in Europe in terms of clean sheets”.
22/12/2024
Everton vs. Chelsea
Tottenham vs. Liverpool
Everton abokanan hamayyar Liverpool ne.
Tottenham abokanan hamayyar Chelsea ne.
Kuna gani Everton zasu iyayin sakarci da daga mana kafa a wasanmu da su yau, domin su yiwa Liverpool buqulu.
Tottenham suma zasu iyayin sakarci da dagawa Liverpool kafa saboda suyi mana buqulun hawa saman teburi, ko kuma zasuyi ta ‘yar gida.
21/12/2024
A gobe Lahadi ne Chelsea zata kara da Everton a filin wasansu.
Muna yiwa Chelsea fatan Nasara.
Nasarar Chelsea na nufin zata haye saman teburin gasar Primier a karon farko tin bayan shekaru hudu da s**a wuce, da kuma karo na farko a karkashin jagorancin Todd Boehly da tawagarsa.
💙
20/12/2024
Marc Guiu ✌️ £6 kacal muka siyo shi daga Barcelona bayan Xavi ya fito da shi daga Academy din kungiyar🥳
Yanzu shine wanda yafi kowa cin Ball a gasar Conference da kwallaye 6 a wasanni 6 a gasar.
Wannan shine hat-trick dinsa na farko a rayuwarsa tare da Chelsea.
Shekarar 18 kacal
17/12/2024
🚨⚠️ Sanarwar daga dan wasa Mykhaylo Mudryk.
"Zan iya tabbatar da cewa ansanar da ni cewa samfurin gwaji dana bayar ga FA ya ƙunshi wani haramtaccen abu".
"Wannan yazo da cikakkiyar girgiza saboda bantaɓa yin amfani da duk wani haramtaccen abu ba ko karya kowace irin doka, ina aiki tare da ƙungiyata [Chelsea] domin bincika yadda hakan ta faru."
"Na san cewa banyi wani laifi ba kuma ina fatan zan dawo filin wasa nan bada jimawa ba."
"Ba zan iya cewa komai a yanzu ba, saboda sirrin tsarin, amma zanyi iyaka yina nan gaba bada jimawa ba."
15/12/2024
Chelsea Vs. Brentford
Kyakkyawan zubi daga Enzo Maresca.
Tosin a farkon farawa (first eleven) tare da Colwell a gefensa wanda a ganina hakan shine mafi cancanta ga kungiyar matukar Tosin zai abinda ake so.
Marasa Lafiya (Injury): Reece James, Fofana, Lavia, Mudryk, Badaichel. sai kuma Neto dakatarwa.
Jackson da Sanchez indai s**a sami katin gargadi na Yellow Card a wannan wasan to zasu rasa fafatawarmu da Everton.
Fatan Nasara ga Chelsea
15/12/2024
- Jadon Sancho dan wasan da ake kallonsa a Man United a matsayin tashi ta kare mai.
- Cole Palmer dan zaman benci a Man City.
- Pedro Neto dan wasan da baya rabo da rauni a Wolves.
- Nicolas Jackson dan wasan da ba a san shi ba a gasar La Liga.
Yanzu sune ‘yan wasa mafi ƙarfin kai hare-hare a gasar Premier.🔝
14/12/2024
Rashin nasarar Liverpool a yau da kuma idan Chelsea tayi nasarar a gobe, hakan na nufin zai zama maki daya ne kacal tsakanin Liverpool ta daya da Chelsea ta biyu.
Zagaye na gaba:
- Tottenham vs. Liverpool birnin London.
- Everton vs. Chelsea a birnin Liverpool
Chelsea zata iya hawa saman teburi kafin Bouncing day🔵
Munce, Ya Ubangiji🤲
14/12/2024
'Yan wasan Leicester City sunyi Celebration irin na Cole Palmer jiya a wasansu da Chelsea a gasar cin kofin FA na matasa.
Sun chi 2-0 amma sun sha kashi daga karshe da ci 3-2..
The Leicester players dropped the Cole Palmer celebration yesterday vs Chelsea in the FA Youth Cup.
They went 2-0 up and lost 3-2. A cold exit from the competition in the 3rd round.
14/12/2024
Thomas Frank Coach din Brentford game da Chelsea.
🗣"Sune wadanda aka ayyana akan yin nasara, Maiyuwa saboda sune Team mafi karfi a gasar Primier a halin yanzu, ta iya kasancewa shirinsu yafi na Liverpool, dukda da cewa Liverpool itace a saman teburi, amma Chelsea tana taka leda sosai, tare da kyakkyawan salon horarwa, Maresca yayi babban aiki."