FC Real Madrid Hausa

FC Real Madrid Hausa Shafin Labaran Kungiyar Real Madrid na Farko a duniya da Harshen Hausa.🤍❤️

21/08/2026

Atisayen karshe kafin wasan Espanyol

‼️💥 A HUKUMANCE: José Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragi tare da Real Madrid har zuwa karshen shekarar 2029. ✍️
18/08/2026

‼️💥 A HUKUMANCE: José Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragi tare da Real Madrid har zuwa karshen shekarar 2029. ✍️

‼️💥 LABARI MAI ZAFI: Real Madrid ba ta ganin akwai  wani ɗan wasan tsakiya da ke kasuwa a halin yanzu wanda zai ƙara wa ...
09/08/2026

‼️💥 LABARI MAI ZAFI: Real Madrid ba ta ganin akwai wani ɗan wasan tsakiya da ke kasuwa a halin yanzu wanda zai ƙara wa tawagarta ƙarfi.

Har yanzu ƙofar ɗaukar sabon ɗan wasa a buɗe take, amma kulob ɗin na bibiyar kasuwar musayar 'yan wasa cikin natsuwa, kuma yana da cikakken yakinin cewa 'yan wasan tsakiya da yake da su a yanzu sun isa su fafata a manyan gasa.

Rahotanni sun ce José Mourinho ba ya fushi da Real Madrid saboda rashin nasarar ɗaukar Rodri. Ya fahimci cewa kulob ɗin ya yi tayin ɗaukar ɗan wasan, amma daga ƙarshe Rodri ya zaɓi wata yarjejeniyar daban.

🤝 An ce akwai cikakkiyar fahimtar juna tsakanin Mourinho da Real Madrid.

ℹ️ Diario AS

Sabbin dokokin da José Mourinho ya kafa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ⚖️👩🏾‍⚖️▫️ Tsauraran tsarin cin abinci: An...
08/08/2026

Sabbin dokokin da José Mourinho ya kafa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ⚖️👩🏾‍⚖️

▫️ Tsauraran tsarin cin abinci: An bayyana tsayayyen abincin karin kumallo da na ciye-ciye. ’Yan wasa ba za su ƙara samun damar zaɓar abincin da suke son ci ba.

▫️ Dole ne ’yan wasa su isa Valdebebas sa’a guda kafin fara atisaye. Duk wanda ya makara zai fuskanci hukunci, ba tare da la’akari da matsayinsa ko shahararsa ba.

▫️ Babu tarar kuɗi ga masu makara: Hukuncin da za a ɗauka shi ne a tilasta wa ɗan wasan yin atisayen motsa jiki shi kaɗai, ba tare da kasancewa tare da sauran ’yan wasa ba.

▫️ Kula da raunin ’yan wasa a cibiyar atisaye: Duk ɗan wasan da ya ji rauni dole ne ya gudanar da aikin murmurewa a Valdebebas da safe da kuma rana. Za su iya ci gaba da amfani da masu horaswa na kansu, amma dole ne aikin ya kasance ƙarƙashin kulawa da tsari na ma’aikatan kungiyar

▫️ Cin abinci tare a matsayin ƙungiya: Mourinho yana son ’yan wasa da ma’aikatan kulob su riƙa cin abinci tare a Valdebebas domin ƙarfafa haɗin kai a cikin ƙungiyar.

🚨SABON LABARI: Ana sa ran dan wasa Bellingham, Kylian Mbappé, Marc Cucurella, Aurélien Tchouaméni da Ibrahima Konaté za ...
08/08/2026

🚨SABON LABARI: Ana sa ran dan wasa Bellingham, Kylian Mbappé, Marc Cucurella, Aurélien Tchouaméni da Ibrahima Konaté za su koma daukar horo tare da Real Madrid a ranar Litinin mai zuwa idan allah ya kaimu

Dan wasa Eder Militao ya dawo daukar atisaye a ciyawa
08/08/2026

Dan wasa Eder Militao ya dawo daukar atisaye a ciyawa

🚨 Sabbin dokokin da José Mourinho ya kafa a Real Madrid 🤍👇▫️ 🍽️ Tsauraran dokokin abinci: An kafa tsayayyen jadawalin ka...
07/08/2026

🚨 Sabbin dokokin da José Mourinho ya kafa a Real Madrid 🤍👇

▫️ 🍽️ Tsauraran dokokin abinci: An kafa tsayayyen jadawalin karin kumallo da abin ci na bayan atisaye. 'Yan wasa ba za su ƙara zaɓar irin abincin da suke so ba.

▫️ ⏰ Zuwa filin atisaye da wuri ya zama dole: Dole ne 'yan wasa su isa Valdebebas awa ɗaya kafin fara atisaye. Duk wanda ya makara za a hukunta shi, ba tare da la'akari da sunansa ko matsayinsa ba.

▫️ 🏋️ Babu tarar kuɗi ga masu makara: Maimakon tara, duk wanda ya makara zai yi horon ƙarfafa jiki na musamman shi kaɗai, ba tare da sauran 'yan wasa ba.

▫️ 🏥 Jinyar masu rauni a cibiyar atisaye: Duk ɗan wasan da ya ji rauni dole ne ya gudanar da jinyarsa a Valdebebas safe da yamma.

Ana ci gaba da ba wa 'yan wasa damar amfani da masu horar da su na kansu, amma duk wani shiri dole ne ya kasance ƙarƙashin kulawa da amincewar masu horar da Real Madrid.

▫️ 👥 Cin abinci tare: Mourinho na son 'yan wasa da masu horarwa su riƙa cin abinci tare akai-akai a Valdebebas domin ƙarfafa haɗin kai.

🗞️

‼️💥 LABARI MAI ZAFI: Rahotanni sun bayyana cewa Real Madrid ta kammala dibar yan wasanni a wannan bazara. Abin da kaɗai ...
07/08/2026

‼️💥 LABARI MAI ZAFI: Rahotanni sun bayyana cewa Real Madrid ta kammala dibar yan wasanni a wannan bazara. Abin da kaɗai zai iya sauya wannan matsaya shi ne idan ƙungiyar ta samu wani babban tayin kuɗi kan ɗaya daga cikin ‘yan wasanta, amma ana ganin hakan ba zai faru ba a wannan matakin.

Yanayin ɗakin sauya kaya na Real Madrid ya sauya gaba ɗaya ƙarƙashin jagorancin José Mourinho. A kakar wasan da ta gabata, akwai yanayi mai cike da rashin jituwa, amma a wannan kakar akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakanin ‘yan wasa da masu horasawa a wajan atisaye

Sabon kwantiragin Vinicius Jr. a Real Madrid:- Albashin da za'a biya shi €25M a kowacce shekara- Yarjejeniyar har zuwa 2...
06/08/2026

Sabon kwantiragin Vinicius Jr. a Real Madrid:

- Albashin da za'a biya shi €25M a kowacce shekara
- Yarjejeniyar har zuwa 2031
- Ƙaramin kaso a haƙƙin hoto %

An cimma yarjejeniyar yanzu-yanzu. Inji Carlos_carpio

Dangane da Rodri, mun bayar da rahoto a ranar Litinin game da COPE cewa Barcelona tana da sha'awarsa, Amma mun yi la'aka...
06/08/2026

Dangane da Rodri, mun bayar da rahoto a ranar Litinin game da COPE cewa Barcelona tana da sha'awarsa, Amma mun yi la'akari da cewa yarjejeniya ba za ta yiwu ba saboda sun yi imanin cewa ya riga yana kan neman kulla yarjejeniya da Real Madrid.

A cewar abokina Victor Navarro, Yanzu an bada tayin Rodri zuwa Barcelona akan Yuro miliyan 60.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FC Real Madrid Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category