02/09/2026
🚨🔥 MOURINHO YA FADI ABIN DA YAKE DAMUNSA GAME DA JUDE BELLINGHAM! 😳⚪️
🇵🇹 José Mourinho ya bayyana cewa lokacin da s**a buga da Real Madrid a Benfica, ya lura da wani abu da bai masa daɗi ba game da Jude Bellingham. 👀
🗣️ Mourinho:
«“Na lura Jude Bellingham yana karewa kusan kamar wani LEFT-BACK. Mun yi amfani da wannan damar sosai.”»
❌ “Ban ji daɗin hakan ba, kuma BA NA SON IN SAKE GANIN HAKAN BA!”
🔥 Mourinho ya bayyana a fili cewa baya son ganin Bellingham yana komawa baya sosai wajen karewa.
🤔 Shin Mourinho zai canza yadda Jude ke taka leda a Real Madrid? 👇
02/09/2026
🚨💣 MOURINHO YA SAITA SABON TSARI MAI TSANANI A REAL MADRID! 😳⚪️
🇵🇹 José Mourinho ya bullo da wasu TSARIN LADABTARWA masu tsauri a Real Madrid, a cewar The Sun. 👀🔥
⏰ Duk ɗan wasan da ya makara wajen zuwa atisaye, za a tura shi GYM maimakon ya shiga atisayen ƙungiyar. 💪
❌ Kuma mafi muni… ZA A HANA SHI FITA A WASA NA GABA! 😱⚠️
🗣️ Mourinho
01/09/2026
🚨👑 JUDE BELLINGHAM & KYLIAN MBAPPÉ — ƳAN WASAN ZAMANINMU! 🤍🔥
Tun daga gasar World Cup, Jude Bellingham da Kylian Mbappé sun kasance cikin fitattun ’yan wasan da s**a fi jan hankali a duniya. 🌍👑
Yanzu suna ci gaba da nuna wannan ƙarfin wasa mai ban tsoro a Real Madrid, kuma kallonsu cikin farin cikin wannan rigar ta Madrid babban gata ne. 🤍⚪️
✨ ’Yan wasa biyu na musamman.
🏆 Ƙarni guda, manyan taurari biyu.
👑 HALA MADRID! 🤍🔥
31/08/2026
🚨💣 LABARI MAI ZAFI — REAL MADRID NA SA IDO KAN MANU KONÉ! 🤍⚪️
🇫🇷👀 Real Madrid na bibiyar ɗan wasan tsakiyar AS Roma, Manu Koné, mai shekaru 25, yayin da Los Blancos ke kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin zaɓuɓɓukan da za su iya ƙara ƙarfi a tsakiyar fili nan gaba. 🔥
🚨 Rahotanni sun ce Real Madrid ta kalli Koné sau da dama, kuma salon wasansa ya ja hankalin ƙungiyar. 💪⚽️
Sai dai a yanzu akwai wani muhimmin bayani:
❌ Real Madrid ba ta shirin yin wani sabon saye a wannan kasuwar transfer ɗin.
🏟️ Don haka, Koné na iya kasancewa target na gaba, ba wai ɗan wasan da Madrid za ta ɗauka yanzu ba.
👀 Amma idan matsalar tsakiyar fili ta ci gaba… shin Manu Koné zai iya zama mafita ga José Mourinho? 🤔🔥
HALA MADRID! 🤍👑
30/08/2026
🤍⚪️ REAL MADRID 4–0 MÁLAGA! 🔥
Madrid ta yi babban wasa a Bernabéu, inda ta mamaye Málaga tare da samun clean sheet. 💪🏽
⭐️ Bellingham ya ci
🔥 Mbappé ya ci
✨ Arda Güler ya kammala aikin
Maki 9/9! Madrid ta fara kakar bana da ƙarfi sosai. 🤍🏆 Hala Madrid!
30/08/2026
🔥🤍 RABIN FARKO YA KAMMALA — REAL MADRID 3-0 MÁLAGA! ⚪️🔥
Madrid ta nuna ƙarfi sosai a Santiago Bernabéu, inda ta shiga hutun rabin lokaci da babban rinjaye na 3-0! 😮💨🔥
⚽️ 19’ — JUDE BELLINGHAM!
Jude ya fara buɗe ƙofar cin ƙwallo bayan Madrid ta matsa wa Málaga lamba.
⚽️ 26’ — OWN GOAL!
Matsin lambar Madrid ya tilasta wa mai tsaron Málaga, Alfonso Herrero, ya ci kansa. 😳
⚽️ 30’ — KYLIAN MBAPPÉ!
Mbappé ya samu damar zinariya kuma bai yi kuskure ba — 3-0! 🚀🇫🇷
📊 A rabin farko, Madrid ta mallaki kusan 63% na kwallo, ta samu harbi 4 da s**a nufi raga, yayin da Málaga ba ta samu ko ɗaya a kan raga ba.
🔥 Madrid ta taka wasan cikin iko, ta matsa lamba, kuma ta hukunta Málaga duk lokacin da dama ta samu.
Yanzu abin jira shi ne: za mu ga ƙarin ƙwallaye a rabin na biyu? 👀🔥
🤍 HALA MADRID! 🤍
29/08/2026
🚨⚪️ EXCLUSIVE: REAL MADRID TA KAMMALA YARJEJENIYAR SAYEN SERGIO MARTÍNEZ! HERE WE GO! ⭐️🔥
Real Madrid ta cimma yarjejeniya ta karshe domin daukar matashin ɗan wasa Sergio Martínez, mai shekaru 19. 🇪🇸🤍
✨ Martínez zai shiga Real Madrid nan take, ba tare da komawa Racing aro ba.
📝 Kwangilarsa za ta kasance har zuwa Yuni 2030, yayin da kudin cinikinsa ya kai kusan €3M. 💰
🇬🇧🇩🇪🇸🇦 Ya kuma ƙi tayin kungiyoyi daga Ingila, Jamus da Saudiyya, saboda burinsa na komawa Real Madrid, bayan tattaunawa da José Mourinho. 👑
🔥 Matashin ya zaɓi Real Madrid!
⭐️ Ku ba wannan signing ɗin maki daga 1 zuwa 10! 👇🇪🇸
29/08/2026
🚨🏆 JOSÉ MOURINHO YA FADI ABIN DA YAKE TUNANI GAME DA BALLON D’OR! 😳🔥
🎙️ An tambayi Mourinho: “Wane ɗan wasa ne ya fi cancantar lashe Ballon d’Or?”
🗣️ Mourinho:
«“A ganina, Ballon d’Or ya kamata ya tafi ga irin ’yan wasan da za mu ci gaba da kewarsu har abada bayan sun yi ritaya.”»
🇦🇷 Ya ambaci manyan tarihi kamar Maradona, Ronaldinho, Ronaldo Nazário, Cristiano Ronaldo, Messi, Zidane da Matthäus. 👑
❌ Mourinho ya ƙi amincewa da ra’ayin cewa lashe Champions League ko World Cup kaɗai ya isa ya ba ɗan wasa Ballon d’Or.
😳 Ya ce idan lashe Champions League ne kawai ma’auni, to Luis Enrique ya kamata a ba shi kyautar!
🇪🇸 Game da Spain da De la Fuente, Mourinho ya ce sun cancanci yabo sosai — amma zama mafi kyawun ɗan wasa a duniya wani abu ne daban.
👀 Kuma sai ya ƙara da wata magana mai ɗaukar hankali:
💥 “Ballon d’Or yana da ɓangaren siyasa a cikinsa, kuma idan siyasa ta shiga, ni ba na son hakan.”
🔥 Mourinho ya kuma ce akwai ’yan wasa biyu, uku ko huɗu da s**a cancanci kyautar, kuma “mun san su… suna nan.”
😱 TO WANE ƊAN WASA MOURINHO YAKE NUNI DA SHI?
👇 Ku fa, waye ya kamata ya lashe Ballon d’Or a wannan shekarar? 🏆🤔
29/08/2026
🚨🤯 KYLian MBAPPÉ YA KAI 100 G/A A REAL MADRID! 🇫🇷⚪️
A cikin wasanni 105 kacal da ya buga wa Real Madrid, Kylian Mbappé ya riga ya kai 100 Goal Contributions! 😱🔥
⚽ 89 Goals
🅰️ 11 Assists
💯 Wasanni 105 — G/A 100!
🔥🤯 Wannan ba wasa ba ne… MBAPPÉ MACHINE! 🚀👑
Hala Madrid! 🤍🏆
28/08/2026
🚨🔥 VINI JR. VS ARSENAL A EMIRATES! 🏟️⚔️
Vinícius Jr. zai kara fuskantar Arsenal a Emirates Stadium bayan da aka shafe watanni ana alakanta shi da yiwuwar komawa Gunners a wannan bazarar. 💣🇧🇷
Amma Vini ya ƙi komawa Arsenal, ya zaɓi ci gaba da zama a Real Madrid kuma ya sanya hannu kan sabon kwantiragi. 🤍👑
Yanzu dai lokaci ya yi da zai nuna musu abin da s**a rasa! 😮💨🔥
⚽ Shin Vini Jr. zai iya zura ƙwallo a ragar Arsenal? 👀
👇 Ku yi hasashen ku: Vini zai ci ko ba zai ci ba?