Sansanin kwallon kafa

Sansanin kwallon kafa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sansanin kwallon kafa, Sports Team, Nigeria, kano, fagge, Kano.

05/07/2025

kylian Mbappe ya jefa kwallonsa ta farko a gasar fifa club world cup a yayin karawarsu da Dortmund inda yaci kwallo ta 3

05/07/2025

Mbappe zai kara da tsohuwar kungiyarsa sayen da rigar real Madrid

05/07/2025

Real Madrid ta tsallaka wasan semi final ita PSG bayan da real Madrid din ta doke Dortmund 3 2 yayinda psg ta doke beyern Munich 2 0 yakuke ganin wasan zai kasance

02/07/2025

Dan wasan gaba na Real Maridar Rodrygo ya nemi barin Ƙungiyar, Arsenal ta shirya bashi matsayi na farko a cikin tawagarta.

Da zarar an kammala gasar Club World Cup, za a fara tattaunawa kan yarjejeniyarsa ta barin Real Madrid.

Menene ra'ayinku?

01/07/2025
28/06/2025

Most followers in social media from 1 to 10

27/06/2025

WASA 3, KWALLO 2, ASSIST 1, A FARKON KAKARNAN.
Shin Kuna ganin Gonzalo Garcia yayi kokari a Madrid kuwa?

27/06/2025

TOTTENHAM DA ARSENAL NA ZAWARCIN DAN WASAN ENGLAND.
Arsenal za ta yi gogayya da Tottenham wajen ɗaukan ɗanwasan Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze mai shekara 26 wanda aka yi wa farashi fam miliyan 68. (Sun)

Arsenal na ƙyalla ido kan Eze wanda farashinsa bai kai ɗaya zaɓinta ba na ɗanwasan Real Madrid Rodrygo mai shekara 24. (Talksport, external)

Tottenham ta ƙiyasta farashin Cristian Romero mai shekara 27 kan sama da fam miliyan 60 kuma ba su shirya cefanar wa Atletico Madrid shi ba kan farashi mai sauƙi. (Telegraph - subscription required)

Napoli da Juventus na shirin biyan Manchester United fam miliyan 25 kan Jadon Sancho mai shekara 25 amma ba za ta iya biyan fam miliyan dubu 250 kowane mako ba ga ɗanwasan. (Metro)

Manchester United na duba yiwuwar sayen ɗanwasan Paris St-Germain da Faransa Warren Zaire-Emery mai shekara 19. (Teamtalk)

Photos from Sansanin kwallon kafa's post 27/06/2025

ROUND 16 REAL VS JUVENTUS.
Wana wasa kuke ganin zaija hankalinku

26/06/2025

LIVERPOOL DA ARSENAL KE KAN GABA WAJEN NEMAN GYOKERES.
Liverpool ta bi sahun Manchester United da Arsenal a zawarcin ɗanwasan Sporting mai shekara 27 Viktor Gyokeres. (Correio da Manha - in Portuguese)

Chelsea ta kusa ƙulla kwantiragi da ɗanwasan Borussia Dortmund da Ingila ɗan ƙasa da 21 Jamie Gittens mai shekara 20, yayin da ƙungiyar ta Bundesliga ke fatan samun shi kan fam miliyan 50. (ESPN)

Manchester United na iya amincewa da tayin fam miliyan 45 don ta samu cefanar da ɗanwasan Argentina mai shekara 20 Alejandro Garnacho. (Star)

Newcastle na ƙyalla ido kan ƴanwasa irin su Johan Bakayoko mai shekara 23 da ke buga wa PSV Eindhoven da Belgium da ɗanwasan Borussia Dortmund da Jamus, Kerim Adeyemi mai shekara 23 idan haƙarsu ba ta cimma ruwa ba a ƙoƙarinsu na ɗauko ɗanwasan Nottingham Forest da Sweden Anthony Elanga mai shekara 23. (Teamtalk)

Manchester United na fuskantar ƙalubalen sayar da ɗanwasan Netherlands Tyrell Malacia mai shekaa 25 wanda ya taimaka wa PSV Eindhoven lashe kofin Eredivisie yayin da yake zaman aro a kakar da ta wuce. (Athletic - subscription required)

26/06/2025

TSOHON DAN WASAN LIVERPOOL YAYI RETIRED IRIN TA KWALLON KAFA.
Adam Lallana, tsohon ɗan wasan Liverpool wanda ke taka leda a Southampton ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa a shafinsa na Instagram.

A wata sanarwa mai ratsa jiki da ya wallafa ranar Laraba, ya ce ba shi da wata nadama saboda barin ƙwallo a yanzu bayan ya kwashe shekaru 18 yana wasa a ajin ƙwararru.

Lallana, wanda ke da shekaru 37 a duniya, tsohon tauraron tawagar ƙwallo ta Ingila ne, wato Three Lions, wadda ya buga wa wasa har 34.

Adam Lallana ya koyi ƙwallon ƙafa ne a makarantar koyar da ƙwallo ta Southampton har sanda ya kai shekaru 18 a duniya a 2006.

Farawa da kammalawa a Southampton

Bayan fara ƙwallo a Southampton, Lallana ya koma Brighton da kuma Liverpool sannan ya buga wa ƙasarsa Ingila a gasar kofin duniya ta 2014. A ƙarshe ya koma Southampton inda a nan ne ya yi ritaya.

A zamansa na farko a Southampton, ya buga wasanni sama da 250 inda ya taimaka mata komawa ajin Firimiya daga ajin League One karo biyu. Ya sake komawa can bara 2024, shekarar da s**a faɗo daga Firimiya.

A 2014, Lallana ya koma Liverpool kan fam miliyan £25, inda ya kwashe shekara 6 ƙarƙashin Brendan Rodgers da Jurgen Klopp a matsayin koci, inda ya lashe kofin Zakarun Turai a 2018–19 da na Firimiya a kakar 2019–20.

Da yake bayyana farin cikinsa da yadda rayuwarsa ta wasa ta kasance, Lallana ya ce "Yayin da nake kawo ƙarshen rayuwar wasana, ina hakan ne cike da gamsuwa da alfahari".

Photos from Sansanin kwallon kafa's post 26/06/2025

⚽ *Wasannin Club World Cup: Real Madrid vs RB Salzburg*
Real Madrid za ta kara da Red Bull Salzburg a Philadelphia a wasan ƙarshe na rukuni H na gasar FIFA Club World Cup. Ƙungiyar ta lashe wasa ɗaya da kuma canjaras ɗaya, tana jagorantar rukuni H da maki 4, yayin da Salzburg ke bi da maki iri ɗaya amma da ƙasa da su a bambancin kwallaye.

🏃‍♂️ *Kylian Mbappé Ya Koma Atisaye*
Bayan jinya da cutar hanji, Kylian Mbappé ya koma atisaye tare da tawagar Real Madrid. Ana sa ran zai taka leda a wasan da za su yi da Salzburg.

Xabi Alonso Ya Koma Kallon Matashin Dan Wasan Real Madrid*
Joan Martinez, matashin dan wasan Real Madrid, ya dawo daga dogon jinya kuma Xabi Alonso yana sa ido a kansa domin ganin yadda zai taka rawa a kakar wasa mai zuwa.

🗣️ *Gonzalo Garcia Torres Ya Yi Magana Kan Makomarsa*
Gonzalo Garcia Torres, dan wasan gaba na Real Madrid, ya bayyana cewa makomarsa a ƙungiyar zai dogara ne da shawarar kulob din da kuma mai horo.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Culinary Team

Attire

Website

Address

Nigeria, Kano, Fagge
Kano