25/08/2026
Assalamu Alaikum Jama'ar Unity Boys Sauna U-15,Muna taya daukacin al'ummar Musulmi, musamman ma mambobi da masoya wannan kungiya tamu ta Unity Boys, murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW).Kungiyarmu ta dogara ne akan hadin kai, zaman lafiya, da kaunar juna. Ko da yake akwai banbancin ra'ayi ko fahimta a tsakanin al'umma, a wajenmu kowa namu ne, kuma muna girmama kowa.Muna yi wa kowa da kowa fatan alkhairi da samun albakar wannan lokaci. Allah ya ƙara dankon zumunci da hadin kai a tsakaninmu, ya kuma albarkaci kungiyarmu.Happy Eid El-Maulud ga kowa da kowa! 🎉⚽🌟
17/08/2026
Muna Farin Cikin Sanar Da Ku! 🤝⚽Cikin gaddama da nuna jinjina, kungiyar kwallon kafa ta Unity Boys Sauna U-15 na farin cikin sanar da daukacin masoya da mabiya cewa ta kulla gagarumar alaka da hadin gwiwa da shahararren kamfanin magunguna na Asad Pharmaceuticals.Wannan yarjejeniya ta kulla alaka ta daukaci kudi naira, wanda hakan zai taimaka kwarai da aniyan wajen inganta kayan aiki da ci gaban matasan ‘yan wasan mu na Unity Boys.Muna mika godiyar mu ta musamman ga mahukunta da ma’aikatan Asad Pharmaceuticals saboda amincewa da irin kokari da hazakar yaran mu, da kuma goyon bayan cigaban wasanni a matakin tushe.Ku kasance tare da mu don ganin sabbin nasarori da kayatattun wasanni! 📈🔥 SaunaU15 Nasara ranar
15/08/2026
🏃♂️ More than just a team—we are a family. Building skills and friendships every single day. Unity Boys Sauna U15 to the world! ⚽️💪🔵⚪️🔥
11/08/2026
Wannan kallon na ƴar Leda ba na wasa ba ne... 😒 🪑 Yana nan a benci yana kallon yadda Ibransi (Bros)ke ta zira ƙwallaye a ragar abokan karawa, yana ta uban tunani a kan makomarsa🤔💭
08/08/2026
Nasara ba a filin wasa kadai take ba, har da bangaren ilimi da addini. 'Yan wasanmu sun ziyarci dan uwanmu Amir domin taya shi murnar babban rabo na sauke Littafi Mai Tsarki (Alqur'ani). Muna alfahari da kai Amir! Allah ya albarkaci rayuwarka. 🤲🏆