14/07/2026
to wannan shine Allah yasa mu dace
Kawo muku ingantattun labarai shine muradinmu
14/07/2026
to wannan shine Allah yasa mu dace
13/07/2026
Tukuntawa LEGIT TV
13/07/2026
Kotu ta Hana inec amincewa da shugabancin devid Mark a jam,iyyar adc
...
.
fans
BBC Hausa
13/07/2026
ABDUL MAI WALA HAULA
(Babban Mawakin Gwamnan Jihar Sokoto)
Ya yi kira ga al’ummar Jihar Sokoto da ma ‘yan Najeriya baki ɗaya da su ci gaba da yi wa jihar da ƙasa addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kai, da ci gaba.
Abdul Mai Wala Haula ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron da Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu Sokoto, FCNA, ya gudanar. A cewarsa, ci gaban kowace al’umma yana buƙatar haɗin kai, zaman lafiya da kuma addu’a. Ya buƙaci jama’a su ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya tare da yi wa shugabanni addu’ar Allah Ya ba su hikima da ikon gudanar da mulki cikin adalci da nasara.
Ya kuma jaddada cewa haɗin kan al’umma da addu’a su ne ginshiƙan cigaba, tare da fatan Allah Ya ci gaba da kare Jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya, Ya tabbatar da zaman lafiya da yalwar arziki ga kowa.
tukuntawa legit tv
13/07/2026
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 61 a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa sun kammala sauke Alƙur'ani Mai Tsarki a wani shiri na gyaran hali da koyar da addini.
A cewar sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar, fursunonin da s**a kammala shirin sun haɗa da maza 55 da mata shida.
Sanarwar ta ce da dama daga cikin waɗanda s**a sauke Alƙur'anin ba su da cikakken ilimin karatu da haddar Alƙur'ani kafin shigarsu gidan gyaran hali, amma ta hanyar koyarwa da horo na musamman sun samu nasarar kammala haddarsa.
Domin ƙarfafa musu gwiwa, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tare da haɗin gwiwar gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation sun rabawa waɗanda s**a kammala karatun kayan tallafi da s**a haɗa da sabbin kaya, katifu, barguna da kuma tallafin kuɗi domin sauƙaƙa musu komawa cikin al'umma bayan sun kammala zaman gidan gyaran hali.
Mai kula da Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yabawa Babban Kwanturolan Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagorancinsa da kuma ƙoƙarin da yake yi na bunƙasa shirye-shiryen ilimi, koyon sana'o'i da tarbiyya a gidajen gyaran hali na faɗin ƙasar nan.
11/07/2026
__Duniya Ta Lalace! 😳
__Ba a Musu Bulala. 😛
__Ba a Hukuntasu. 🤔
__Kuma Suna Nan a Cikin Kano. 🥺
__Suna Nan a Cikin Kano! 🫨
__Na Rasa Kano...
__Wai wane irin, it' it' it' Ni Kano Wani Irin Gari Ne Kam Wai Shi... 😂😂😂
Just For Weekend Fun 🤣😝😜
D One Fashion House✂
11/07/2026
A jikina nakeji, In sha Allah Duk wanda yaga wannan posting ɗin🥺👇
Wani Abun alheri yana shirin faruwa dashi 🙌✍️
11/07/2026
Wannan shine mahaifina Jarumi kuma Director nasan kun kalli fina finai da dama wanda shi ya bada umarni wato Ilyasu Abdulmumini ✅️
11/07/2026
Fitaccen mai wa'azi kan addinai daga ƙasar Indiya, Pandit Vijay Kumar Sharma, ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na murƙushe Musulmi ko kawar da addinin Musulunci ba zai yi nasara ba.
Sharma ya yi wannan furuci ne yayin jawabinsa a taron Ranar Quds da aka gudanar a watan Maris 2026, inda ya nuna goyon bayansa ga al'ummar Falasdinu.
A cikin jawabinsa ya ce Idan Amurka da Isra'ila suna tunanin za su murƙushe Musulmi ko su kawar da Musulunci, wannan mafarki ne kawai. Tsararku za ta shuɗe, ku ma za ku shuɗe, amma Musulunci ya kasance, yana nan, kuma zai ci gaba da wanzuwa har abada.
11/07/2026
hi