26/05/2026
YANZU-YANZU: Jam'iyyar PDP ta tsaida Professor Isa Ali Pantami CON a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Gombe a zabe mai zuwa.
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from VOK HAUSA, Sport & recreation, Gumel Road, Kano.
Ku kasance tare da Voice of Kano VOK HAUSA Domin Cigaba da samun Ingantattun Labarai Cikin Gaskiya da adalci
Ba San zuciya ba kazafi ko kage
Whatsapp no.090393935610. / 09035683171
26/05/2026
YANZU-YANZU: Jam'iyyar PDP ta tsaida Professor Isa Ali Pantami CON a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Gombe a zabe mai zuwa.
24/05/2026
Rijiyar Lemo Dogon Bene, kusa da Masallacin Gawo kenan bayan saukar ruwan sama.
Hotuna daga Comrd Abdussalam Rijiyar lemo.
24/05/2026
’Yan takarar Gwamnan Gombe a PDP sun yi fatali da batun shigar Pantami
Manema takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, sun yi watsi da jita-jitar cewa tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, na shirin shiga takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.
Wannan jita-jitar na zuwa ne bayan da tsohon ministan ya halarci zaɓen fidda gwani ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC kuma ya shaye kaye wanda aka gudanar a ranar 21 ga Mayu, 2026.
A cikin sanarwar haɗin gwiwa da s**a fitar a ranar Asabar, manema takarar sun ce babu wani mataki na shigar Pantami cikin tsarin PDP, tare da jaddada cewa jam’iyyar za ta tsaya kan tsari guda da shugabanni za su yanke.
24/05/2026
Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II , ya yanka cake don taya ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal murnar lashe gasar Premier League na bana.
24/05/2026
2027: Dole ADC ta tsayar da gogaggen dan takarar shugaban ƙasa - Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci jam’iyyar ADC ta tsayar da gogaggen dan takarar shugaban kasa mai kwarewa domin tinkarar zaben 2027.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulda da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, Atiku ya ce Najeriya na fama da matsin tattalin arziki, rashin tsaro, hauhawar bashi da tabarbarewar hukumomi, don haka kasar na bukatar shugaba mai iya mulki tun daga ranar farko.
Ya bayyana cewa ba lokacin gwajin shugabanci ba ne, yana mai cewa Najeriya na bukatar jagora mai gogewa, wanda ya fahimci harkokin mulki da tattalin arziki tare da iya hada kan al’umma.
Atiku ya kuma gargadi wakilan ADC da su fifita kwarewa da cancanta fiye da son rai wajen zaben dan takarar shugaban kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce zabe ba ya samun nasara da surutan kafafen sada zumunta kadai, yana mai jaddada cewa shugabancin kasa na bukatar shiri da gogewa.
Ya kuma yi nuni da cewa nasarorin da aka samu a lokacin gwamnatin 1999 zuwa 2007, ciki har da gyaran tattalin arziki da rage bashin kasa, sun samo asali ne daga shugabanci mai nagarta da kwarewa.
Rahotanni sun ce Atiku zai fafata da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da tsohon shugaban kamfanin NDDC, Mohammed Hayatu-Deen, a zaben fidda gwani na ADC da za a gudanar ranar 25 ga Mayu, 2026.
22/05/2026
Hoton Nan Fitaccen mawakin hausa Umar M. Shareef yayinda ya kammala karatu a Makarantar KASU Dake Kaduna
Wanne Fata Kuke Masa
22/05/2026
Hotunan Yadda Shahararren Ɗan Gwagwarmaya, Ɗan Bello Tare Da Haɗin Gwiwa Da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya Ta Kasa S**a Gyara Makarantar Firamaren Ta Musamman Ta Koyan Kimiyya Da Lissafi Ta Kadawa A Jihar Kano
Wace Irin Fata Za Ku Yi Masa?
Daga Jamilu Dabawa
22/05/2026
Fadar shugaban ƙasa ta musanta shirin sauya sunan Najeriya da soke Shari’a a Arewacin Nijeriya
Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin yin kwaskwarimar kundin tsarin mulki domin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke dokar Shari’a a jihohin Arewa.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya tsagwaronta da aka ƙirƙira domin haddasa rikicin siyasa da tayar da zaune tsaye gabanin babban zaɓen 2026.
Sanarwar ta ce babu wani shiri da Shugaba Tinubu yake da shi na aika wa Majalisar Dokoki wani kudiri mai suna “Project True Federation” kamar yadda ake yaɗawa.
Fadar shugaban ƙasar ta zargi masu yaɗa rahoton da kasancewa masu neman haddasa rikici da rarrabuwar kai a ƙasa, tare da buƙatar ’yan Najeriya su yi watsi da labarin baki ɗaya.
Ta kuma bayyana cewa yin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa ba abu ne mai sauƙi ba, domin sai an samu rinjayen kashi biyu bisa uku a majalisun dokokin tarayya tare da amincewar akalla majalisun dokokin jihohi 24.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu na mayar da hankali ne wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da kuma samar wa ’yan Najeriya ribar dimokuraɗiyya maimakon shiga batutuwan da za su haddasa rarrabuwar kai.
Fadar shugaban ƙasar ta kuma gargadi jama’a da su yi taka-tsantsan da rahotannin bogi da ka iya ƙaruwa yayin da harkokin yaƙin neman zaɓe ke ƙara ƙamari kafin zaɓen watan Janairun 2026.
22/05/2026
Kashi 90 Cikin Ɗari Na Waɗanda S**a Samu Nasarar Lashe Zaɓukan Fidda Gwani A Takarkari Daban-daban A Jihar Katsina, Ba Zaɓi Na Ba Ne Ko Na Ce Dole Sai An Zaɓe Su, Mun Ji Ra'ayoyin Al'umma Ne, Saboda Masu Ruwa Da Tsaki Na Kowacce Karamar Hukuma, Su Aka Ba Dama Su Je Su Zauna, Su Yi Abinda Ya Dace, Zaɓe Mu Ke Son Mu Ci A Jam'iyyar APC Ba Wai Biyan Buƙatar Kanmu Ba, Cewar Gwamna Dikko Raɗɗa
Me Za Ku Ce?
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
22/05/2026
Dan Majalisar Kano Mai Wakiltar Mazaɓar Gwamna Abba Kabir Ya Koma Jam'iyyar NDC
SPONSORED
Alhamdulillah Masha Allah, A jiya ne Jam iyyar ADC Ta Tabbatar wa Hon Ahmad Sani Ahmad (ABBA JOGANA).
Tikitin Takarar Majalissar Tarayya a Kananan Hukumomin Gezawa da Gabasawa Guda Daya tilo A yankin.