27/12/2022
ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASAR NIGERIA, JAM'IYYAR PDP Atiku Abubakar Yaɗauki Alƙawarin kammala Aikin wutar Lambar Rimi Dakecikin jahar katsina.
Daga SportOrganization
Maigirma Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin kammala aikin wutar lambar Rimi (Lambar Rimi Solar wing) idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar Najeriya'A zaɓe mai shirin tsayawa(2023)
Atiku ya ce gwamnatinsa za ta duƙufa wajen samar da wadacciyar wutar lantarki, ta yadda za a dawo da martabar kamfanoni da cibiyoyin kasuwancin da s**a durƙushe sakamakon rashin iya mulki na wannan gwamnatin mai ci a yanzu domin samun tattalin arziƙin ƙasa mai ɗorewa
Haka zalika Atiku yasha alwashin cigaba da aikin hanyar Kano zuwa Katsina wanda gwamnatin Buhari ya fara daga baya aka watsar da aikin domin biyan,buƙatun waɗan su nada ban.
Aikin wutar lambar Rimi aiki ne da zai samar da wutar iska mai ƙarfin megawa dubu goma wanda gwamnatin tsohon shugaban ƙasa marigayi Umar ƴar'adua ta fara a shekarar 2019 bayan ya rasu aka watsar da aikin aka wawushe kuɗaɗen aikin[]
Atiku ya bayyana haka ne a zantawar shi da ƙungiyoyin ƴan kasuwa da shuwagabannin addini da masu ruwa da tsaki na PDP a lokacin da ya kawo ziyarar gangamin yaƙin neman zaɓen shi a jihar Katsina.
A ƙarshe Atiku ya gargadi al'ummar jihar Katsina cewa kada su zaɓi APC wacce ta jefa su cikin yunwa da rashin tsaro da gami da tsadar rayuwa da kisan gillah,babu ɗauki ko jajin tawa.
Atikun yaƙara kira zuwaga Al'ummar ƙasar Nijeriya baki ɗaya,dasu Duƙufa wajen ganin sun Bawa jan'iyyar PDP kariya,alokacin zaɓe dasu maida hankali,na janyo mata Al'umma domin zaɓenta yin hakane,zai kai jan'iyyar ga nasara (2023)
Wannan saƙone daga ƙungiyar true pdp social media kebbi chapter,tareda matai makin mai magana da yawun jan'iyyar ta PDP naƙasa duka,wato Excellency Alhj Ibrahim Abdullahi manga.
Dukansu ƙarƙashin jagoranci kabiru tanimu turaki (SAN)da Genaral bello sarkin yaƙi.
✍️✍️ Bande bui sport organization