Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa

Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sahihan Labaran Wasanne cikin harcen Hausa, Track Stadium, Adamawa, Yola.

26/05/2025

Kalaman Ruben Amorim ga magoya bayan Manchester United a filin wasa na Old Trafford bayan tashi wasansu da Aston Villa.

"Ina son neman afuwar ku game da yadda wannan kakar ta kasance. Na yi matukar jin ba daɗi ni da tawaga ta.
Sannan abu na biyu, ina son gode muku.
Muna matuƙar godiya da irin goyon bayan da kuka bamu a gaba ɗaya wannan kakar. Na san wasanni da yawa sun zo mana da tsauri.

"Yanzu muna da isasshen lokacin da zamu yi gyara.
Mu manta da abun da ya faru a baya, saboda kakar wasan ta ƙare, ta ƙare.
Ka da mu zargi juna, mu cigaba da tafiya tare tsintsiya maɗaurinki ɗaya mu kalli gaba.

"Watanni shida da s**a wuce, na ce zamu shiga mawuyacin hali. Yau, bayan wannan mummunar kakar wasan, ina son faɗa muku cewa kwanaki masu kyau suna nan zuwa.

"Idan akwai wata ƙungiya a duniya da a baya ta nuna zata iya shawo kan kowanne irin yanayi mai kyau ko mara kyau, to ƙungiyar mu ce. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.

"Na gode muku sosai - sai mun gan ku kakar wasa mai zuwa."

• Sahihan Labaran Wasanne ✍️

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Yola?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Adamawa
Yola