02/09/2026
😂🐐 MESSI YA SAKE REPOSTING TALLAN MICHELOB ULTRA A INSTAGRAM! 🍺🔥
A cikin tallan, an rubuta:
🏆 RECORDS — SHATTERED
📈 EXPECTATIONS — REDEFINED
🌍 THE WORLD — INSPIRED
🐐 GOAT DEBATE — SETTLED
Sannan a caption ɗin an ce: “Más de 20 años. Seis Copas…” — sama da shekaru 20, kofuna shida. 😭😂
Kuma ga abin da ya fi ɗanɗano… Messi da kansa ya sake wallafa tallan! 👀🍿
To yanzu idan aka ce “GOAT debate settled”, su sauran ’yan wasan su zauna su karanta receipt ɗin kawai. 😂😂
… kuma gaskiya, ina son wannan sosai! 🐐🔥
02/09/2026
🚨 MUHIMMIN SANARWA GA MASOYAN SHAFINMU ⚽🔥
Muna shirin kawo manyan sauye-sauye a wannan shafi. 👀🔥
Daga cikin sauye-sauyen akwai sake fasalin shafin, canza suna, sabon salo na content, da kuma mayar da shafin wata babbar kafa ta muhawarar kwallon kafa, adawa da ra'ayoyi. 🗣️⚽
Za mu rika kawo muku muhawara irin ta:
🔵🔴 BARCELONA 🆚 REAL MADRID ⚪
🐐 MESSI 🆚 RONALDO
⚽ 'Yan wasa 🆚 'Yan wasa
🏆 Kungiya 🆚 Kungiya
🔥 Ra'ayoyi, muhawara, tambayoyi da batutuwan da za su sa masoya kwallo su bayyana ra'ayinsu.
👥 ANA NEMAN SABABBIN ADMIN!
Muna kuma bude damar daukar sabbin Admin domin taimakawa wajen tafiyar da sabon tsarin shafin.
Abubuwan da ake nema: ✅ Masoyin Barcelona ko Real Madrid
✅ Ko masoyin Messi ko Ronaldo
✅ Mai yawan bibiyar kwallon kafa
✅ Mai iya kawo muhawara cikin mutunci
✅ Mai iya aiki da Facebook da tsara posts
✅ Mai kasancewa mai gaskiya da adalci wajen muhawara
Ba sai ka kasance masoyin kungiya daya kawai ba. Abin da muke nema shi ne mutum mai kishin kwallon kafa kuma mai iya kawo ra'ayi mai karfi + hujja. 🔥
📌 Idan kana sha'awar zama Admin, ka rubuta “INA SHA'AWA” a comment.
SABON SUNA. SABON SALO. SABON ZANGO. 🔥⚽
ADAWA ZALLA na dab da zuwa… 👀🔥
02/09/2026
🇦🇷👏 ARGENTINA ZA TA TSAYA DOMIN MESSI! 🐐💙
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina (AFA) ta shirya cewa dukkan wasannin gasannin ƙasar na maza da mata a zagaye na gaba za su tsaya a minti na 10.
👏 Za a yi minti ɗaya na tafi domin girmama tarihin da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina.
🔟 An zaɓi minti na 10 ne saboda lambar rigar Messi.
🇦🇷❤️ Shekaru 21, kofuna, tarihi da abubuwan tunawa marasa iyaka.
Gracias, Leo. 🐐👏
02/09/2026
🇦🇷💔 SAƘON BANKWANA NA LIONEL MESSI GA ARGENTINA
Bayan shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar Argentina, Lionel Messi ya yi bankwana da tawagar ƙasar. 🥹
🗣️ Ana danganta wannan saƙon da Messi:
“Abu ne mai wahala in bayyana abin da nake ji. Na san wannan rana za ta zo, amma lokacin da ta zo da gaske, komai ya bambanta.
Na sanya rigar Argentina sama da shekaru 20. Na zo nan ina yaro, kuma yanzu ina barin tawagar bayan na fuskanci kusan duk wani yanayi da ƙwallon ƙafa za ta iya kawo maka.
Na yi rashin nasara, na sha s**a, kuma akwai lokutan da nake jin komai ya ƙare. Amma koyaushe ina dawowa, saboda ƙaunata ga Argentina ta fi komai ƙarfi.
🏆 Na samu damar lashe kofunan da na yi mafarkin lashe su tun ina yaro. Amma abin da ya fi sa ni alfahari ba kofunan kaɗai ba ne — shi ne sanin cewa BAN TAƁA DAINA YAƘI DOMIN WANNAN RIGAR BA.
🇦🇷❤️ Ina barin tawagar ƙasar, amma Argentina ba za ta taɓa barin zuciyata ba.”
💔🐐 Ƙarshen wani babban zamani na ƙwallon ƙafar Argentina.
02/09/2026
🚨🗞️ ALƘALI YA ƘI BUƘATAR REAL MADRID! ❌
A cewar Cadena SER, alkalin da ke jagorantar shari’ar Negreira ya ƙi buƙatar Real Madrid na ƙara binciken shari’ar da wasu watanni shida.
Binciken dai bai ƙare gaba ɗaya ba, amma ba za a tsawaita wa’adinsa kamar yadda Real Madrid ta nema ba. 👀
🍿 Yanzu dai sai a ga wane sabon abu za su mayar da hankali a kai! 🤷♂️
01/09/2026
🚨😳 PIERS MORGAN YA BAR LIONEL MESSI A WAJE DAGA CIKAKKEN XI NA SA! 🐐👀
🗣️ Piers Morgan ya bayyana cewa Lionel Messi ba ya cikin ’yan wasan da zai zaɓa a cikin All-Time XI ɗinsa.
🤔 Shin kun yarda da zaɓinsa?
01/09/2026
🚨🔵🔴 GABRIEL JESUS ➡️ BARCELONA! 🇧🇷9️⃣
👕 Gabriel Jesus zai sanya lamba 9 a Barcelona.
🔥 Sabon ɗan wasan Barça ya shirya fara sabon babi!
⭐️ Maki nawa daga 1 zuwa 10?