Arewa Youths Media Forum AYMF

Arewa Youths Media Forum AYMF

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Youths Media Forum AYMF, Go-kart track, Abuja.

17/03/2025

They grokked me over the case of the NYSC girl from Lagos and grok shocked them!

Maybe I bribed Elon Musk, the richest man on Earth.


07/01/2024
22/09/2022

SAI DA NA ZUB DA HAWAYE😭😭😭

Na tabbata wata rana bana raye~Inji Sanata Kwankwaso

Ina jan hankalinku kuyi abin da ya dace idan kunje. "Abin dayasa na samar da wannan gidauniyar ta Kwankwasiyya Development Foundation, "Nasan wata rana bana raye, ayanzu nafi karfi ci da sha da kuma sutura.

babban burina shine! yanda 'Yayana suke karatu a makarantu masu kyau musamman na kasashen waje, haka nake so naga Dan talaka shima ya samu dama, na tabbata ilimin ku yafi gonakina da filayena muhimmanci, shiyasa nasai da wasu daga cikin kadarorina kuma na bude gidauniya domin Jama'a suma su taimaka, mu turaku Kasashen Duniya, ina da yakinin duk cikin ku babu mutumin banza,

Domin duk wanda zai samu sakamako mafi daraja a makarantun gaba da sakandire babu shakka yana da baiwar da idan yasamu dama zai amfanar da Al'umarsa da addinin sa.

Ina mai jan hankalinku kuyi abin daya dace ku fitar da iyayenku kunya muma damuka turaku kufitar damu kunya, ina addu'a Allah yayi muku albarka. Wannan ya farune lokacin da Gidauniyar Kwankwasiyya zata tura Dalibai dari uku da saba'in Kasashen ketare a shekarar 2019 a gidan sa dake Milla road a Jihar Kano

Wannan nasihar da Madugu yayiwa Daliban itace tasani hawaye, alokacin mafiya yawan Shugabanni s**a zurme da son duniya da kece raini ta hanyar banbanta Y'ayansu da Y'ayan Talakawa da tara abin duniya kamar basa tunani zasu mutu.

Ya Allah kasan abin dake zuciyar bawanka Sanata Kwankwaso ka bashi Shugabancin Najeriya kuma kayi masa Jagoranci akan mulkinsa sabo da Shugaban Halitta Muhammadarrasulillah🙏🙏🙏

Amir Abdullahi Kima Darmanawa

25/01/2022.

21/09/2022

JAN HANKALI GA MATASAN MU AKAN MUHIMMANCIN ZAMAN LAFIYA.

✍Abu Sadiq Al'Nigeria: Shugaban kungiyar Arewa Youths Concern Media Forum. Na Kasa.

Yana daya daga cikin manufofin wannan kungiyar ta AYCMF wayar da matasa akan muhimmancin zaman lfy a cikin al'ummar da suke rayuwa. da zaman lfy ake samun duk wani cigaban rayuwa yan uwa matasa mu zauna lfy mu guji tada duk wata fitina da zata rusa zaman lfyr al'ummar mu.

A matsayin ka na matashi Mai matsakaicin shekaru wanda baka taka ko wanne irin matsayi na cigaban rayuwa ba. bakada Kudi Gida Mota Mata. kafi kowa dacewa da tabbatar da zaman lfy domin samun wayannan ababen a shekarun da zaka karayi a gaba.

In kayi sanadin tashin hankali a irin wannan matsayin naka ko garin naku ne ya tashi ko aka kore ku sanadiyar abunda aka hada kai da ire irenka akayi na tada hankali. kaine a rana kaine wahallalle wanda zai zama dan gudun hijira a lagos ko Port Harcout ko kasashen ketare cikin kaskanci da wulakanci acan gida kuma ka bar iyayen ka yan uwan ka yayun ka kannen ka cikin tashin hankali.

Mafi yawan fituntunu ana tadasu ne yayinda aka hada kan wasu gurbatattun matasa ko jahilan matasa wanda s**aki tsayuwa suyi karatu su fahimci rayuwa da abunda yake cikin ta. duk abunda akazo musu dashi matukar za abasu wasu yan kudade zasu karba su aiwatar da wannan aikin ba tare da nazarin halin da iyayen su kannen su yan uwan su zasu shiga ba.

Duk lokacin da ka yarda aka assasa wata barna da kai musamman wacce zata hana zaman lfy a cikin al'ummar dakake rayuwa acikin ta. ka sani ka cuci kanka kuma a wulakance zaka mutu baza kayi nisan kwana ba sannan zaka mutu jama'a suna tsine maka albarka kuma baka samu yanke talauci ba a yayinda kake wannan ta'addancin.

Lalle matasa ya kamata mu gane muhimmancin zaman lfy a cikin al'ummar mu. kar mu yadda da bude duk wata kofa da zata rusa zaman lfyr mu. bamuda inda yafi Arewa a cikin Nigeria. kar mu yadda da cigaba da wanzuwar ta'addanci a yankin Arewar mu. dan uwa matashi kasa a ranaka bazakayi ta'addanci ba. baza ahada kai dakai ayi ta'addanci ba. baza ka bada bayanan sirri ko wanne iri ga dan ta'adda ba. domin kishin yankin ka da al'ummar ka.

Mu zama masu bada bayanan sirri ga jami'an tsaro ta hanyar kwarewa akan dukkan wani motsin da bamu yadda dashi ba. wannan shine wayewa. ba wai mu dunga boye sirrin yan ta'adda ga jami'an tsaro ba. kamar kuskuren da mukayi abaya lokacin farkon wanzuwar Boko Haram. yin hakan tamkar kiwon dan kunama ne a cikin dakin ka ya girma ya hanaka zaman lfy ya hana makotanka zaman lfy anguwar ka garin ka daga karshe ya tilasta maka barin gidan baka shirya ba. wannan shine saka makon boye sirrin dan ta'adda mu kiyaye yan uwa matasa.

Allah ya zaunar damu lfy

21/9/2022

Photos from Arewa Youths Concern Media Forum's post 19/09/2022
Profile pictures 31/08/2022

Kungiyar Arewa Youth Concern Media Forum ta sauya logon kungiyar da Wanda aka santa dashi abaya.

Wannan shine sabon logon kungiyar Wanda zatana amfani dashi insha Allah. Allah ya taimake mu akan abunda muka sa a gaba na alkhairi.

Sanarwa : AYCMF National P.R.O Comr. Abubakar Usman Bello Editer.

30/08/2022

DOMIN KISHIN AREWA DA AL'UMMAR AREWA MATASAN MU SU ZAMA JAKADU NA KWARAI A DUK INDA S**A TSINCI KANSU.

AREWA YOUTHS CONCERN MEDIA FORUM (AYCMF)

Kungiyar AYCMF kungiya ce da aka kafata domin tunkarar lamuran matasan arewacin Nigeriamai jihohi 19 da Abuja 20 akan kyawawan manufofi guda biyar 5.

Kungiyar aycmf tanada tsarin shugabanci tun daga kan shugaban kungiya na kasa (National
Chairman) da shugaban kungiya na jiha (State chairman) har zuwa shugaban kungiya na karamar
hukuma (Local Government Coodinator).

Kungiyar AYCMF kungiyace mai zaman kanta (NGO) wacce take gudana karkashin shuwagabannin
kungiyar tare da tafiyar da al’amuran kungiyar a karkashin su.

MANUFOFIN KUNGIYAR AYCMF

1. Wayar wa matasa kai akan illa da hadarin dake cikin shiga kungiyoyin ta’addanci domin a yanzu yankin mu na arewa makiya na gida dana waje suna dab da maida mana shi cibiyar ta’addanci. ta'addanci ya yawaita a Arewacin Nigeria akwai bukatar mu motsa domin yaki da tunanin ta'addanci a kwakwalen matasan mu musamman masu tasowa.

2. Wayar wa matasa kai akan illa da hadarin dake cikin kungiyoyin (ASIRI) wanda abaya munajin labarin su ne a wasu yankuna na kasar nan amma yanzu sun tarar damu har cikin gidajen mu. kungiyoyin Asiri sun yawaita a Arewacin Nigeria. yana daga cikin ayyukan su zabar da jinin al'ummar saka mutane a mummunar hanya kamar fyade ga kananun yara luwadi madigo yankar wani saahin jikin mutum tone kabari hada rigima domin a zubda jini dss.

3. Wayar wa da matasan mu kai akan hadarin dake cikin (SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI)
wanda yana daya daga cikin abunda yake karawa ta’addanci tagomashi a yankin mu na
arewa. matasa sune kashin bayan al'umma amma in s**a zama nagari masu amfanarwa ba masu cutar da al'ummar ba. Shaye Shayen Miyagun Kwayoyi bazai taba barin matasa su zama abun alfahari ga al'ummar su ba.

4. Wayar wa matasa kai akan muhimmacin (DOGARO DA KAI) in matasa s**a zama masu
dogaro da kawunan su zaiyi wuya su bada hadin kai azo da wani abun da zai wargaza musu zaman lafiyar su a yankin su b***e a rude su.

5. Wayar wa matasa kai akan illa da hadarin dake cikin (ZAMAN BANZA) in matasa s**a tsinci kansu suna zaman banza babu irin abunda baza su karba ba daga miyagun kungiyoyi in an kawo musu.

Wannan sune manufofin kungiyar AYCMF wanda take kokarin isar dasu a lungu da sakon arewacin Nigeria insha allah. Wayar da kan matasa shine aikin mu.

KUNGIYAR AYCMF TANA DA TSARUKAN GUDANAR DA AYYUKAN TA
GUDA BIYU (2)

1. Kungiyar AYCMF tana bin hanyoyin isar da sakonnin wayar wa matasa kai a duk inda yake tara dandazon matasa. Muna amfani da wannan damar mu shirya wani gangami a jagoranci wayarwa matasa kai ( awareness) a wajen.

2. Kungiyar AYCMF tana amfani da kafafen sadarwa gidajen Tv, Radio, da kafafen sadarwa na zamani kamar facebook, instagram,twitter, whatsapp … wajen rubuce rubuce domin isar da sakonnin kungiyar.

Kungiyar AYCMF tana karbar shawarwari daga wajan masana akan dukkan abunda ya shafi
ayyukanta. Muna tuntubar masu ilimi akan abunda ya shafi tsarawa a kungiayr tun daga kan jami’an
tsaro da jami’ai masu kula da fataucin miyagun kwayoyi dss.

Kungiyar AYCMF tanayiwa membobin ta shidar zama yan kungiya (MEMBERSHIP IDENTITY CARD) domin komai munayin sa ne akan tsari.
Muna maraba ga kowanne matashi namiji ko mace mai kishin wannan al’umma tamu ta arewa a wannan kungiyar.

Kuzo mu hada karfin mu waje guda domin tunkarar matsalolin yankin mu wanda bamu da kamar sa duk duniya.bayan wannan manufofin guda biyar kungiyar AYCMF tana kokari wajen isar da koken mutanen arewa da kiraye kiraye ga gwamnati a inda ya kamata ayi kira ga gwamnatin akan wata matsala in ta taso.

Allah muke rook ya zunar da arewa da Nigeria lafiya ya hada kan al’ummar arewa mu zama
tsintsiya madaurinki daya.

✍️ AYCMF MANAGEMENT
30/8/2022

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Abuja