Labaran wasanni

Labaran wasanni

Share

domin zafafan labaran wasanni kui mana follow da like

30/08/2026

Fc Barcelona Zata mara P.S.G da Real Madrid a October tazarar kwana biyar tsakanin wasannin 😱
Shin Wasa nawa kuke Ganin Fc Barcelona zata iya ci a wannan satin Zataci P.S.G sannan taci Real Madrid ?
Shin ya kuke gani ?

Photos from Labaran wasanni's post 30/08/2026

Messi yaci kwallo hudu ⚽ ⚽ ⚽ ⚽ a wasan Inter Miami da Sukaci Bakwai da 'Daya (7-1) a kwallonsu da s**a Kara da Montreal Team din su Alexis Sanchez Tsohon Dan wasan Arsenal da Fc Barcelona me buga Lamba tara.
Shin anya Zamu Saken Ganin kamar Messi da Cristiano Ronaldo kuwa ? 😢🤔

Photos from Labaran wasanni's post 29/08/2026

🚨 LABARAN WASANNI: SIMAKAN YA WARWARE CECE-KUCEN DA AKE KAN KWALLON DA RONALDO YACI WANNAN SATIN! 😮🇵🇹
Wasu magoya bayan kwallon kafa suna ta caccakar Cristiano Ronaldo a kafafen sada zumunta, bisa tunanin cewa Mohammed Simakan bai yi farin ciki ba bayan Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo daga Shot din da Simakan ya yi, sabida anga ya rufe fuska da tafi biyu alamar jimami, domin wasu na ganin shot din nasa zai shiga raga koda Ronaldo be kara shot din ba.
Sai dai bayan an tashi wasan, da 'yan jarida s**a tambaye shi ko yana jin Ronaldo ya karɓe masa ƙwallon da ya kamata ace shi yaci, Simakan ya ce ya yi matuƙar farin ciki da ya zamo ya yiwa daya daga cikin manyan yan kwallon da duniya ta taba gani a tarihi assist wato Cristiano Ronaldo. 🐐🔥
⚽ Don haka, abin da wasu s**a ɗauka a matsayin rashin farin ciki, Simakan ya ce farin ciki ne saboda ya ba Ronaldo assist! 🇵🇹👏
Shin meye naku fahimtar ?

Photos from Labaran wasanni's post 29/08/2026

🚨 LABARI DA DUMI DUMI

Akwai rahoton dake cewa ƙungiyar Athletic Bilbao na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, inda aka samu tabbatarwa cewa Shugaban ƙungiyar na atletic Bilbao ya dakatar da tallafin tikiti huɗu kyauta da ake bai wa 'yan wasa na shiga fili kallon wasa.

Rahoton ya kuma ce ƙungiyar ta fara ɗaukar matakan rage kashe kuɗi a kullum domin shawo kan matsalolin kuɗin da take fuskanta.

Abin da ya ɗauki hankalin mutane shi ne, wannan ita ce ƙungiyar da a baya baya ta tuntubi La Liga domin neman bayani kan tabbacin ko Barcelona tanada kudin da zata iya register din Nico william inda s**a samu tabbacin aa s**a zagaya s**a hana nico zuwa Fc Barcelona din, kila da sun siyarwa Barcelona da yanzu basa wannan matakin. 👀

Yanzu kuma ana zargin ita kanta Athletic Bilbao na fuskantar nata ƙalubalen na kuɗi. 😮

🗣️ Wane ra'ayi kuke da shi kan wannan batu? Ku faɗa mana a sharhi!

📌 LABARIN WASANNI — Ku biyo mu domin samun sahihan labaran ƙwallon ƙafa da na wasanni cikin sauri. ⚽🔥

25/08/2026

Daukacin Team na Wannan gida, me suna [Labaran Wasanni] muna taya daukacin musulmin duniya murnar zagayowar Ranar haihuwar Manzon allah (S.A.W), muna masu yiwa annabi salati da fatan allah ya kara mana kaunar annabi da bin sunnah tasa, allah ya kara bamu zaman lafiya a dukkanin fadin duniya 🙏🏻

24/08/2026

🚨 PAUL POGBA YA RAGE FARASHIN GIDANSA NA ALFARMA DA ZE SIYAR

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Paul Pogba, ya rage farashin katafaren gidansa na alfarma da ke Cheshire [keshaya] yanki dake tsakanin Manchester da Liverpool daga £3.95m zuwa £3.5m a naira kudin kimanin naira bilyan shida ( 6 billion naira), bayan ya sha fama wajen samun mai siya. 🏡💰

Gidan mai ɗakuna biyar ya ƙunshi filin wasan ƙwallon ƙafa na cikin gida, gidan kallon fina-finai mai zaman kansa, dakin motsa jiki da kuma ɗakin kula da lafiya. 😮‍💨⚽

🗞️ labari daga MailSport

Photos from Labaran wasanni's post 20/08/2026

📰 ROBERTO CARLOS YA FADI GASKIYA KAN JITA-JITAR CEWA YA MUSULUNTA YA KARYATA ZANCEN, 'Yan JARIDA DA YAWA SUN YADA KARYA
Tsohon fitaccen ɗan wasan Brazil kuma gwarzon Roberto Carlos ya yi magana a karon farko kan jita-jitar da ta bazu cewa ya musulunta bayan aurensa da wata ’yar kasar Morocco mai suna Souhaila Al-Tahiri.
Rahotannin da s**a fito daga kafafen yada labarai na Turkiyya sun ce Roberto Carlos, mai shekaru 53, ya musulunta kimanin makonni huɗu da s**a gabata, bayan ya karanta Kalmar Shahada a wani taro da Sheikh Jihad Hamada, daya daga cikin fitattun ’yan kungiyar Musulmi a Brazil.
Abin da ya kara rura wutar jita-jitar shi ne wani rubutu da Ali Sahin, ɗan majalisar dokokin Turkiyya daga jam'iyyar Justice and Development Party, ya wallafa a shafin X.
Sahin ya bayyana cewa ya gana da Sheikh Jihad Hamada a São Paulo, inda Sheikh ɗin ya ce Roberto Carlos ya dade yana tuntubarsa, kafin daga bisani ya ziyarce shi makonni huɗu da s**a gabata, ya karanta Shahada sannan ya karɓi Musulunci.
❌ ROBERTO CARLOS YA KARYATA BATUN MUSULUNTARSA
Amma Roberto Carlos ya fito fili ya musanta wannan rahoto, inda ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa ya musulunta.
A wata hira da jaridar Saudiya ta Okaz ranar Laraba, ya ce:
“Ina matukar girmama Musulunci, kuma abin farin ciki ne ganin matata tana yin sallah, amma jita-jitar da ake yadawa cewa na musulunta ba gaskiya ba ce.”
💍 GAME DA AURANSA DA ’YAR MOROCCO
Roberto Carlos ya kuma bayyana cewa bikin aurensu ne ya sa mutane s**a fara zargin cewa ya musulunta.
Ya ce an gudanar da bikin aurensu ta hanyoyi fiye da ɗaya, domin an yi la’akari da addinai da imanin ’yan uwa.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin ’yan uwansa Katolika ne, don haka aka gudanar da wani biki da ya dace da imaninsu, sannan aka kuma gudanar da wani biki da ya dace da matarsa da abokanta Musulmai.
A takaice: Roberto Carlos ya tabbatar da cewa yana matukar girmama Musulunci, yana girmama matarsa da addininta, amma ya ce labarin cewa ya musulunta ba gaskiya ba ne.

Photos from Labaran wasanni's post 15/08/2026

🔥 : Ronaldo Ya Dawo training Al Nassr Da Sabon Salon Gyaran Gashi! 🇵🇹🟡🔵

Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da Al Nassr a Riyadh, bayan hutun da aka ba shi bayan kammala gasar World Cup da kuma aurensa da Georgina Rodríguez.

✨ Ronaldo ya bayyana da sabon gashi mai launin Gold/copper, abin da ya bambanta da salon gyaran gashin da ya saba yi.

💍 Ronaldo da Georgina sun yi aure a Portugal ranar 11 ga watan Agusta, taron ya samu halartar ‘ya’yansu biyar.

⚽ Yanzu Ronaldo yana shirin sabon Season na wasanni a Saudi Pro League, amma rahotanni sun ce kocin Al Nassr, Ange Postecoglou, na iya ba shi lokaci kafin ya dawo wasa, domin kauce wa yiwuwar rauni bayan ya fara atisaye ne kawai bada jimawa ba sabida ya samu fitness sosai duk da ronaldo din dan wasane da be wasa da training koda lokacin hutunsa.

📅 Ana sa ran zai iya samun damar buga wasa a ranar 18 ga Agusta da Al Diriyah.

Ronaldo ya dawo! 🐐🔥

14/08/2026

🇭🇷 Ivan Rakitić ya bayyana irin MATSANANCIN MATSIN LAMBA da ake fuskanta a Barcelona daga yan jarida🤯🔵🔴

🗣️ Ivan Rakitić:

“Daya daga cikin wasannin farko na gasar La Liga bayan da na koma kungiyar Barcelona, mun doke Granada da ci shida ba ko daya 6-0. Na zura kwallo daya, sannan na taimaka aka ci ta biyu da kai.

Bayan an tashi wasan, yazama dole naje domin yin magana da manema labarai. Amma tambayar farko da aka yi min bayan mun ci 6-0 ita ce:

‘Me ya faru da ku yan wasan? Wataƙila farkon Sizin ne, amma har yanzu ba ku taka leda yadda ya kamata ba baku buga wasa mekyau...’ 😳

Sai na cewa yan jaridan wajen Mun ci 6-0, na zura kwallona ta farko a Nou Camp, mun yi nasara… amma tambayar farko ita ce, “Har yanzu ba ku taka leda yadda ya kamata 😂 🤯

Domin a Barcelona, ba wai kawai batun samun nasara ba ne...

🔥 akwai Batun ya kayi ka yi nasara cikin salon da ya dace. sannan dole ka buga wasa me kyau me burgewa🔵🔴

25/07/2026

Abun mamaki wani uba tare da yardar yan uwan sun radama yaron su suna Messi domin soyayyar su ga Lionel Messi na kasar Argentina 😱

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kano
Kaduna