Asadulhifz

Asadulhifz

Share

Passionate about knowledge & growth
� Lover of kind words and positivity
� Respect, honesty & good vibes only
� Living to inspire, not to impress

12/06/2026
12/06/2026

"Sadakar sirri (Sadakar da aka yi ta a boye) tana kawar da fushin Ubangiji".
🎤
Inji Manzon Allah (S.A.W).

Akwai mutanen da sun karye a harkar kasuwancin su saboda wani bangare na fushin Ubangiji ya shafe su, akwai wadanda suke cikin damuwa iri iri a yau saboda fushin Ubangiji ya taba su, akwai wadanda sun gagara samun nasara akan abinda suke nema a rayuwa saboda fushin Ubangiji, abinda zaka yi...👇

Ka nemi wani mutum ko wasu mutane kayi musu Sadaka a boye, kada ka bari wani yasan kayi musu, sai ka koma kayi addu'a ka roki. Wannan Sadakar ba lallai ta zama mai yawa ba, gwargwadon halin ka.
A yau zaka iya yin Sadaka wa mutum ba tare da ya sani ba, misali:

Zaka iya tura recharge card ta Bank application dinka, wanda ka tura masa ba lallai yasan kaine ba, wannan Sadaka ce ta sirri, zaka iya sayan Data wa mutum ba tare da ya sani ba. Zaka iya zuwa shagon POS ka bayar da account din mutum a tura masa, ba zai ga sunan ka ba b***e ya gane kai ne, wannan sadakar sirri ne.

Wanda kake binsa bashi zaka iya cewa wane na rage maka Naira dubu 3,000 daga cikin dubu 10,000 da nake binka, yanzu dubu 7,000 zaka bani idan kazo biya, wannan Sadaka ce ta sirri daga kai sai shi, ko kuma wane na yafe maka gaba daya ka barshi kawai, hanyoyin sadakar sirri suna da yawan gaske.

Zaka iya neman aika sako kace a bashi amma kada a fadi daga gare ka ne. Musamman a ranaku irin wannan ta Juma'a, Litinin da Alhamis, ka dinga yin haka zaka samu mafita akan al'amuran da s**a yi maka kunci, in sha Allah.

Photos from Asadulhifz's post 10/06/2026

Jiya Talata Alhaji Abdulmumin Yakubu Mai Shanu (AYM), mai kamfanin AYM Shafa Oil ya fitar da zakkar dukiyar sa ta wannan shekara, kuma ya rabawa mutane dari 500, kowannen su ya samu Naira dubu 200,000.

Naira miliyan 100,000,000 kenan.
AYM Shafa ya saba duk shekara yakan tsara fitar zakkar sa a nan Bauchi duk shekara bayan aikin Hajji.
Anyi rabon a nan cikin garin Bauchi.

Zakka tana daya daga cikin Ibadun da ake so ayi su a fili a bayyane.
Allah ya cigaba da tsarkake masa dukiyar tare da dukkan sauran masu wadata dake kokarin yin abinda Allah yace a duk inda suke.

09/06/2026

Ya Biyoni Inbox Yace Min....

Profesa Watarana Na Fito Sallar Azahar Ɓarawo Ya Sace Min Wayata Ƙirar Iphone 15. Bayan Na Dawo Office Na Shiga Damuwa Saboda Kuɗin Da Suke Cikin Account Ɗina.

Nan Take Na Kira Banki Aka Rufe Min Account Ɗina Baki Ɗaya. Sannan Na Tafi Bompai Na Biya Kuɗi Aka Fara Aikin Tracking Domin Nasan Yadda Aka Sace Min Wayata A Masallaci. 24hours Labari Yazo Min An Kamo Ɓarawon Wayata. Naje Na Ganshi Saurayi Mai Ƙarfi Ajika.

Na Tambayeshi Yadda Ya Sace Min Wayata Yace Yafi Kwana Sha Huɗu Yana Bibiyar Wayar Allah Bai Bashi Nasara Ba Sai Yau, Na Tambayeshi Sana'arsa Yace Min Sata, Nace Masa Meyasa Yake Sata? Yace Min Mahaifinsa Ya Rasu Ya Barsu Su Bakwai Shine Babba, Duk Duniya Ya Rasa Mai Taimaka Masa Ya Cigaba Da Karatu Saboda Haka Ya Ajiye Karatun Ya Nufi Sata Domin Kula Da Ƙannensa Mata.

Nan Take Nayi Umarnin Aje Gidansu A Bincika, Washe Gari Akaje Akazo Da Labarin Maganarsa Gaskiya Ce. Na Bashi 500k Nace Yaje Ya Siyawa Mahaifiyarsa Kayan Abinci, Sannan Na Umarci Kullum Ya Fito Yazo Kasuuwa Ya Zauna Idan An Tashi A Bashi 3k .

Tun Daga Wannan Ranar Bai Ƙara Sha'awar Ya Saci Kayan Wani Ba, . Nayi Imani Da Allah Cewa Yanzu Na Yarda Dashi Fiye Da Wasu Yaran Nan Nawa, Shiyasa Nake Kokarin Buɗe Wani Sabon Shago, Kuma Shi Zan Ajiye A Matsayin Manaja Insha Allahu Rabbi!

® Profesa Babuji
Asadulhifz Prof. Adam Muhammad Abubakar Shaikh Abubakar Gummi School Adamu Musa Kore Viral

09/06/2026

Hanyoyi 10 na Rage Damuwa

1. Yawaita ambaton Allah (zikiri)
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: “Lalle da ambaton Allah ne zukata ke samun nutsuwa.” Ka yawaita tasbihi, istigfari da salati ga Annabi ﷺ.
2. Sallah da addu’a
Idan damuwa ta yi yawa, ka nemi taimakon Allah ta hanyar sallah da addu’a cikin tawali’u.
3. Karatun Alƙur’ani
Karatun Alƙur’ani da saurararsa na kawo natsuwa da kwanciyar hankali ga zuciya.
4. Karɓar ƙaddarar Allah
Ka yi imani cewa duk abin da ya same ka yana cikin hikimar Allah, kuma bayan kowace wahala akwai sauƙi.
5. Guje wa yawan tunanin abin da ya wuce
Abin da ya faru ya riga ya faru. Ka ɗauki darasi daga gare shi, sannan ka ci gaba da rayuwa.
6. Tattaunawa da mutanen kirki
da amintaccen mutum mai hikima na taimakawa rage nauyin zuciya.
7. Motsa jiki da tafiya
Tafiya, motsa jiki ko wasu ayyuka na taimakawa jiki da kwakwalwa su sami natsuwa.
8. Tsara rayuwa da ayyuka
Yawan rikice-rikice da rashin tsari kan ƙara damuwa. Ka tsara ayyukanka bisa fifiko da cancanata
9. kyautatawa da taimakon mutane
Sadaƙa da taimakon mabukata suna sanya farin ciki a zuciya kuma suna rage damuwa.
10. kyakkyawan fata
Ka yi imani cewa Allah zai buɗe maka ƙofofin alheri. Kada ka yanke ƙauna daga rahamar Allah.

Hikima

“Kada ka bari damuwar gobe ta hana ka jin daɗin yau, domin Allah wanda ya kula da kai jiya, shi ne zai kula da kai gobe.”

Allah ya yaye mana baƙin ciki da damuwa.

05/06/2026

An kawata duniya da abubuwa biyar:

1. Ilimi da malamai
2. Adalcin shugabanni
3. Ibadar bayin Allah
4. Amanar ’yan kasuwa
5. Kyakkyawar nasiha daga masu ba da shawara

Sai kuma Iblis ya zo da tutoci guda biyar domin ya lalata waɗannan abubuwa:

* Ya zo da hassada domin ya yaƙi ilimi.
* Ya zo da zalunci domin ya yaƙi adalci.
* Ya zo da riya domin ya lalata ibada.
* Ya zo da ha’inci domin ya lalata amana.
* Ya zo da yaudara da ruɗi domin ya lalata nasiha.

Darasi:
Idan aka kiyaye ilimi daga hassada, adalci daga zalunci, ibada daga riya, amana daga ha’inci, da nasiha daga yaudara, al’umma za ta kasance cikin alheri da zaman lafiya.

تفسير الرازي مفاتح الغيب 2/402.

04/06/2026

Duk duniyan Al-Qur'ani yanzu sai labarin Shaikh Muhammad Siddiq al Minshawi ake yi, amma me ya faru ne ake ta labarin?

A shekarar 1965, Shaikh al Minshawi ya rubuta wasika wa gidan rediyon Al-Qur'ani na Misra (a lokacin su ne kaɗai suke bayar da dama a yi recording na karatun Al-Qur'ani), ya sanar da su cewa akwai wassu wurare a album nashi da yana so ya sake recording nasu, kuma shi zai ɗau nauyin duk expenses na recording ɗin. Haka kuwa aka yi. Ya je ya sake recording ɗin.

Ana nan, Shaikh ya rasu, duniya ta ci gaba a yanda take, an ma manta da karatun, aka ci yaba da yaɗa wancan tsohon karatun....

A makon nan, gidan rediyon Al-Qur'ani na Misra sun sanar cewa za su fara yaɗa wancan recording da Shaikh yayi, bayan shafe kimanin shekaru 61 da yin recording ɗin.

Ɗan uwa, ka dage ka shuka alheri. Yanzu Shaikh Minshawi ya kusa shekaru 60 a kwance a kabari, amma kullum sai an saurari karatunsa a duniya... Kwatsam! Sai ga karatunsa da mutanen da ya rayu da su ma ba su taɓa ji ba, mu kam muna nan muna morewa. Ya kake gani idan a ce wata tsiya ce ya shuka?

Ina nan ina tattara sabon recording ɗin,... In sha Allah idan na kammala zan saka su a telegram in bayar da link nasu ga duk mai bukata. Wallahi karatun sun yi daɗi, kuma suna ratsa zuciya.... Minshawi ultra pro max ne!

03/06/2026

Idan kullum zamu kashe Naira 500 a recharge na kiran waya, Naira 500 a Data. Duk shekara muna kashe Naira dubu 365,000 kenan ko kusa da haka.

Amma zai yi wahala idan ka hada lissafin abinda muka bayar a Masallaci ko wani aikin alkhairi ya kai Naira dubu 20,000 a shekara, ina magana game da mafiya yawan mu ne ba duka ba.

Wanda baya kashe kudi ma waya shine wanda a shekara yake cin Data da recharge card din Naira dubu 60,000 zuwa 70,000. Wannan dai tunatarwa ce nayi ma kaina da sauran 'yan uwa, domin ajali kusantowa yake, kwanaki karewa suke, kuma za'a yi lissafin abinda aka bamu a duniya da bayanin yadda muka kashe.
Asadulhifz Shaikh Abubakar Gummi School Prof. Adam Muhammad Abubakar Ruky Precious Adamu Musa Kore Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo

23/05/2026

Idan kana karanta Al-Qur'ani a hankali kana lura da messages and messagers wato sakon Ubangiji da kuma wadanda Allah ya baiwa sakon su isar. Zaka ga cewa Ubangiji yana da tsarin bayar da Annabta ko Manzanci ga 'dan garin da ake so suyi Imani, ko kuma 'dan Kabilar, misali;

1. Game da Adawa (mutanen Annabi Hudu), sai Allah yace "Zuwa ga Adawa mun aika musu 'dan uwan su Hudu".

2. Samudawa (mutanen Annabi Salihu), sai yace "zuwa ga Samudawa mun aika da dan uwan su Salisu".

3. Mutanen birnin Madayana (mutanen Annabi Shu'aibu), sai Allah yace "zuwa ga birnin Madayana mun aika da dan uwan su Shu'aibu".

Abinda nake in nuna mana shine, Allah yayi ta cewa 'dan uwan su, wato kaso 98 na Annabawan da Allah ya aika ya aike su ne zuwa ga mutanen garin su, Kabilar su, Yaren su, 'dan uwan su.

A cikin Suratu Ibrahim Allah yace "babu wani Manzon da muka aike shi face da Yare (language) din mutanen sa ya tafi, domin yayi musu bayanin sakon".

Wato "Bi Lisani kaumihi"
بلسان قومه
Da harshen mutanen sa.
Daga cikin hikimar yin haka itace;

Idan ana so Da'awah ta karbu, mutane su fahimci sakon da aka kawo musu toh ayi musu da Yaren da suke ji, a aika musu da wanda zai iya yin magana fluently da Yaren su, saboda shi ya san mutanen sa, suma sun sanshi, da zaran yayi bayani zasu gane zasu fahimta cikin sauki.

Idan ka dauki Bahaushe kace yaje yayi wa'azi da yaren Igbo ba za'a samu abinda ake so ba sai dai in dama a cikin ya tashi, yana yin Yaren kamar yadda suke yi, kuma ya fahimce su. In ba haka ba babu yadda za'a yi su gane b***e su karba.

Haka kuma idan kace kai mutumin birni zaka je kauye ka koyar dasu, na farko harshen ka ba zai zama dai dai da nasu ba, watakil akwai abubuwan da dole kayi amfani da kalmar Turanci, sannan shigar ka da Tufafi ka dole zata bambanta dasu, hakan zai kara girman barrier of understanding tsakanin ka dasu.

Toh haka muke fama a bangaren Da'awah a yau, mutane da yawa zasu shiga Musulunci amma koyar dasu shine babban aiki. Duk wanda ya shigo Musulunci kuma aka koyar dashi Musulunci a cikin watanni shida (six months) toh in sha Allah zai tabbata kuma ya dauwama a cikin Musulunci.

Amma sabanin haka toh da wahala su iya zama a cikin Musuluncin, koda sun zauna zasu zama cikin wadanda basu san komai game da addinin su ba.

Sai dai, yaya za'a yi a koyar dasu?

Dole ayi koyi da salo ko strategy da Allah yayi bayani a Al-Qur'ani, shine aje a dauko wasu daga cikin mutanen kauye da s**a Musulunta a shigo dasu cikin gari, cikin birni, ayi camping dinsu na watanni 6 a koyar dasu, idan sun goge sai su koma kauyukan su don su koyar da Musulunci da Yaren su.

Sai dai yin hakan yana bukatan a Gina babbar Islamic center, ayi wajen da za'a Gina dakunan kwana, Azuzuwa, Masallaci, Abincin su, abun shan su, Syllabus, daukan nauyin Malaman da zasu karantar dasu na watanni shidan. Wannan kuma zai ja miliyoyin kudade masu yawan gaske.

Idan ba'a samu haka ba dole a cigaba da local system na daukan mutanen birni suna zuwa kauyuka suna koyarwa suna dawowa gari.
Wannan tsarin shima da nasa kalubalen, shine wasu wuraren suna da nisa da birni ko bakin babban T**i, kafin ka shiga dajin kaje ka koyar har ka fito Awanni ne masu yawa, abu na biyu ana bukatan Ababen hawa, Motorcycle ko Babur masu yawa, mota Hilliux da 'kananan Motoci.

Kaga duk wata ko duk sati sai anyi fueling an saka Man Fetur. Sannan idan kuka je kauyen most of the time sai kun je kun hado kan mutanen, saboda wasu sun tafi Gona, wasu kasuwa, wasu suna wajen wani wasa, mutanen kauyuka kadan ne zasu tara mutanen su idan sun san zaku zo koyar dasu ilimi.

Idan kuma kace zaka tura Malamai suje su zauna a kauyen suyi wata daya ko biyu suna koyarwa dole ka dauki nauyin iyalan su da s**a bari a gida, dole ka kula da security din Malaman daka tura din, domin ba zaka tura su kauye haka kawai ba tare da security plans da tsari mai kyau ba.
Dole ka dauki nauyin Abincin su, da Magani idan rashin lafiya ta taso.

Aiyuka ne masu yawan gaske, masu wahala, idan bamu yi ba toh makiyan mu zasu yi, kuma kauyukan dake gefe da manyan biranen mu zasu shiga wasu addinan daban daban. Domin mutanen su ba zama s**a yi ba, suna aiki kamar yadda wasu Musulmi suke yi domin yin kira zuwa ga addinin su a nan Arewa da muke rayuwa.

Mutane su shigo Musulunci ba abu ne mai wahala ba, amma a koyar dasu har su tabbata a Musulunci da ilimi shine abu mai wahala, kuma mai cin kudi da lokaci sosai. Wadannan dai aiyuka ne da muke fatan Allah ya bamu ikon yin abinda zamu iya kafin ajali yazo mana, domin ba zasu kare ba.

Aiyuka ne da a rana daya zasu ci kudi mai yawa idan aikin za'a yi sosai yadda ya kamata, b***e a sati, wata ko shekara. Wadannan wasu ne daga cikin kalubalen mu a fagen Da'awah da kuma bukatun mu, muna addu'a Allah ya bude mana Kofar arziki da zamu yi haka domin daukaka addinin mu da kuma neman kada a wajen Allah.

Allah yasa mu dace.
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo Prof. Adam Muhammad Abubakar Adamu Musa Kore Shaikh Abubakar Gummi School Asadulhifz Ruky Precious

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Kano