Real Madrid White House fans

Real Madrid White House fans

Share

Mun buɗe wannan shafi ne domin Nishaɗantuwa ta hanyar rubuce-rubuce akan abinda ya shafi ƙungiyar

19/05/2025

MUHIMMAN ABUBUWA GUDA 10 DANGANE DA NICO PAZ DA BA KOWA NE YA SANI BA.

1. An Haife Shi a Sifaniya, Amma Yana Wasa da Ƙungiyar Ƙasa ta Argentina. Duk da cewa an haifi Nico Paz a Tenerife, Sifaniya, ya zaɓi wakiltar Argentina a matakin ƙasa, don girmama asalin mahaifinsa.

2. Mahaifinsa, Pablo Paz tsohon ɗan Wasan ƙwallon ƙafa ne, inda ya wakilci Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya ta 1998, kuma ya buga kwallo a ƙungiyoyi da dama a Sifaniya, ciki har da CD Tenerife.

3. Ya Shiga Real Madrid Yana da Shekaru 16. Ya koma Real Madrid La Fábrica (makarantarsu ta matasa) daga Tenerife a 2016, inda ya yi fice da sauri saboda ƙwarewarsa.

4. Ya Ci Kwallo a Wasan Farko na Champions League. A watan Nuwamba 2023, Nico ya fara buga gasar Champions League tare da Real Madrid kuma ya ci kwallo mai ban mamaki.

5. Ana Kwatanta Shi da Kaká da Fede Valverde. Saboda saurinsa, iya kai hare-hare, da kyakkyawan salon wasa, ana kwatanta shi da tsohon tauraron Brazil Kaká, yayin da wasu ke ganin yana da irin ƙoƙarin Fede Valverde.

6. Nico Paz na iya amfani da ƙafa biyu hagu da dama a wasan kwallo, yana iya bugawa, tsalle, da wucewa da kowacce ƙafa ba tare da matsala ba.

7. Hukumar kwallon ƙafa ta Sifaniya ta nemi ya wakilce su, amma ya ƙi kuma ya nuna biyayyarsa ga Argentina.

8. Duk da kasancewarsa ɗan wasan tsakiya mai kai hare-hare (No. 10), Nico Paz na iya taka rawa a matsayin ɗan tsakiya ko kuma a gefe, gwargwadon tsarin da ake so.

9. A lokacin da yake atisaye tare da manyan 'yan wasa na Real Madrid, ya samu horo daga shahararrun 'yan wasa kamar Modrić da Kroos wanda hakan ya taimaka masa sosai.

10. A yanzu haka Real Madrid na shirin koma da shi daga Como akan kuɗi €8 miliyan, saidai iyalinsa sun bayyana cewa suna so ya zauna shekara ɗaya a can domin ya cigaba da bunƙasa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ƙalubale ba.

Shin me zaku ce akan wannan labari?

19/05/2025
Sen. Karaye

06/05/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Isah Auwal Karshi, Real Dan Bash, Anas Usman, Musa Khalid Dz, Qaribullahi Nasiru Haland, Inuwa Abubakar, Musa Muhammad, Muhammad Salama Jr., Fatima Abdullahi, Abdulkadir Abdulkadir

10/04/2025

SHIN WANNE MAI HORARWA NE YA FI DACEWA DA REAL MADRID A TSAKANIN WAƊANNAN?

Duka Xabi Alonso da Jürgen Klopp ƙwararrun masu horarwa ne, amma wanda ya fi dacewa ya maye gurbin Carlo Ancelotti a Real Madrid ya dogara ne da abin da kulob ɗin ke fi buƙata a wannan lokaci.

AMFANIN XABI ALONSO A REAL MADRID.

1. Tsohon ɗan wasan Real Madrid ne: Yana da masaniya kan al’adun kulob ɗin da tsare-tsare da wanda ke waje ba zai taɓa sani ba (Tradition), matsin lamba da kuma abin da ake tsammani daga shugabanni.

2. Dabarun wasa da taka tsamtsam: Alonso yana da wayau sosai da kuma Dabarun wasa, kowa ya ga yadda yake tafiyar da Bayer Leverkusen da tsari mai kyau na kariya da kuma kyakkyawan salon gina ƙungiyar akan tsari mai kyau da za'a jima ana mora.

3. Matashi ne, kuma zai iya jagorantar sabon zamani kamar yadda Zidane ya yi a baya.

4. Ɗan Spain ne, Yana jin yaren Sifaniyanci, ya saba da ƙungiyar, sannan kuma ya saba da ita gasar ta Laliga da Champions league, duk abubuwan da Real Madrid ke buƙata ya sani babu wani baƙon abu a wajensa yana zuwa ɗorawa kawai zai yi kamar yadda Zidane yayi.

Rashin Amfan Xavi Alonso a Real Madrid.

Saidai duk da haka akwai wasu ƙalubale a gabansa ko Ince (Disadvantages) na kasancewa mai horarwa a Real Madrid a halin yanzu.

1. Rashin ƙwarewa a manyan gasanni: Bai taɓa jagorantar manyan ƙungiyoyi ko gasar zakarun Turai ba a matsayin mai horarwa, kuma ba'a tabbaci ko takamaiman sanin yadda zai fuskanci manyan taurari ba.

AMFANIN JURGEN KLOPP A REAL MADRID.

Jorgen klopp na daga cikin waɗanda aka fi alaƙantawa da Real Madrid idan har aka sallami Ancelotti a kowanne lokaci. Ga wasu daga cikin manyan amfaninsa ga Real Madrid:

1. Yana daga cikin Ƙwararrun masu horarwa ajin farko (Top class coaches) Wanda zaɓi ne mai matuƙar kyau ga Real Madrid da kowa ya gamsu da ƙwarewarsa kuma ya dace da Real Madrid.

2. Ya ci Champions League da Premier League: iya buga gasar champions league da Premier league shine Abu mafi muhimmanci da ya ɗaukaka darajar jorgen klopp, duk wani mai horarwa da Real Madrid zata kawo ba zata gamsu da shi ba matuƙar bai da ƙwarewa a champions league.

3. Klopp yana da kuzari da ƙarfafa guiwar yan wasa, sannan Yana iya sarrafa 'yan wasa masu girman kai kamar takwarorinsa Mourinho, Guardiola, Simeone, sannan kuma yana inganta haɗin kai a cikin tawaga.

4. Salon wasa mai hatsari, gamsarwa da jan hankali: Zai iya kawo sabon salo na kai hare-hare masu hatsari akai-akai a Real Madrid kamar yadda yake yi a Liverpool da kuma yadda yayi lokacin da yake a Dortmund.

Rashin Amfaninsa ga Real Madrid.

1. Matsalar rashin iya yare da kuma al'ada (Language barrier and cultural fit): Jorgen klopp Bai taɓa horarwa a Sifaniya ba, hakan na iya sa ya fuskanci matsaloli wajen daidaitawa da sabon muhalli da yanayin da ya tsinci kansa ko kuma ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya saba, wanda Real Madrid tana buƙatar wanda ya santa kawai zai ɗora saidai yan gyare-gyare da sauye-sauye da ba'a rasa ba.

2. Yana da saurin shiga damuwa da gajiya: Jorgen klopp yana da saurin harzuƙa a aikin koyarwa wanda hakan ka iya haifar da matsala tsakaninsa da hukumomin Real Madrid. Batun gajiya kuma mutum ne da yake yawan buƙatar hutu saboda daukar zafi, hakan ya sa Ya dakata daga horarwa saboda gajiya. Ta iya kasancewa kuma ya shiryawa matsin lambar aikin Real Madrid da s**a fi kowa a duniya.

A ƙarshe, a fahimtata Idan har Real Madrid na son sabon shiri na dogon lokaci da ke da dangantaka da kulob ɗin da sabbin dabaru to Xabi Alonso ya fi dacewa.

Idan kuma suna son canji nan take, shahara da gogewa a manyan matakai to Jürgen Klopp ya fi tabbaci.
Amma bisa ga al’adar Real Madrid? Xabi Alonso ne zaɓi mafi yiwuwa, ana kallon sa a matsayin magaji, kuma lokaci ya yi daidai.

Kai fa, wane kake so a matsayin masoyin kulob ɗin?

Group leader:
Lawan M Ahmad Karaye

14/01/2025

SHIN KO KUN DALILIN DA ANCELOTTI YA BAYAR NA ƘIN SAKA RAUL ASENCIO A WASANNI?

Raúl Asencio, matashin mai tsaron baya dan shekara 21 daga makarantar koyon kwallon kafa ta Real Madrid, yana fuskantar ƙalubale wajen samun damar fara wasa akai-akai tare da babbar ƙungiyar. Duk da irin ƙwazon da ya nuna, ciki har da wasan da ya taka rawar gani tsakanin Real Madrid da Liverpool, amma bai samu damar kasancewa a cikin waɗanda ke fara wasanni a jere ba.

Babbar matsalar da ke hana shi wannan damar ita ce dawowar Aurélien Tchouaméni daga rauni. Dawowar Tchouaméni ta sa koci Carlo Ancelotti ya yi wasu gyare-gyare a dabarun da yake gani sune zasu cece kungiyar, inda ya saka Tchouaméni a matsayin mai tsaron baya, wanda hakan ya sa Asencio ya zauna a benci. Ancelotti ya bayyana cewa Asencio yana ɗan saurin jin gajiya, kuma wannan ya sa ya yanke shawarar da ya yanke na saka Tchouaméni a tsakiya.

Hakanan, dawowar tsohon mai tsaron baya David Alaba daga rauni na iya ƙara rage yawan damar da Asencio zai samu na fara wasanni. Da kwarewar Alaba da matsayin da ya riga ya kafa a ƙungiyar, zai zama ƙalubale ga Asencio ya samu damar zama a matsayin wanda zai fara wasa.

Duk da cewa Asencio ya nuna gwanintarsa a tsaron baya na Real Madrid, tare da dawowar wasu manyan 'yan wasa, na tasiri ga damar da yake da ita na fara wasa akai-akai.

Group leader:
Lawan M Ahmad Karaye

19/12/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Adamu Gimba, Yushau Usman, Abdul Rmg, Jafar Muhammad, Hafizu Labaran Isah Zango, Abdul Aliyu, Ibrahim Umar Liman, Abbakar Salman, Abdullahi Lbrahim

05/12/2024

Duk inda ka ke neman cikakken ɗan wasa, ajiye maganar adawar da ke tsakaninmu, Mbappe ya kai. Wannan abu ne da duk wanda ya san ƙwallon ƙafa kuma ya ke bibiya da kalla ya sani, sedai adawa kawai, wannan kuma wani abu ne na daban.

A lokacin final na World Cup 2022 da aka yi a Doha, Qatar, shine ɗan wasa ɗaya da ya [kusa] canza labarin, ya zamewa magoya bayan Messi da Argentina barazana.

Idan maganar ƙwallo ta mutum ɗaya ake, Kylian ya kai. Ya san zura ƙwallo, yana da ƙarfi a jiki, yana da hanzari, yana da stamina, ga taƙura abokan karawa, ga accurate shot, ga gudu. Ni na yarda Mbappe cikakken ɗan ball ne, babu abinda bai haɗa ba na zama cikakken ɗan sama (attacker).

Lamarinshi a Madrid wani abu ne da ya kan shafi ko wanne irin ɗan wasa. Sanin kowa ne, har masu zaginshi a yanzu, Kylian yana da kyawu na sama-sama a duniyar ƙwallo. Hakan ma ya sa Madrid s**a bibiyeshi tsawon shekaru, hakan ya sa duniya ta ke kallon motsinshi, hakan ya sa farincikin magoya bayan Madrid ya ƙi misaltuwa a lokacin da ya je cikinsu. Amma wannan wani abu ne da tarihi ya yarda cewa ya kan shafi ko wanne ɗan wasa, musamman farkon zuwanshi team.

Uzuri ya kamata a yi masa, a bashi cikakken lokacin da zai goge a Spain. Bana iya cewa ba, amma tabbas zai goge, mu kuma abokan hamayya muna tsoron wannan lokacin.

29/11/2023

ƁOYAYYEN LABARIN DA BA KOWA YA SANSHI BA 🤔🤔🤔

A shekarar da Argentina taci kofin duniya (world cup) ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga (P. K) har sau 5 a cikin waɗannan wasannin da wannan gasar 🙄🙄🙄

A shekarar da Real Madrid ta ɗauki Kofin zakarun Turai (Champions League) sai 3 a jere cikin shekaru 3 daga 2016, 2017 da 2018 amma cikin wannan shekaru 3 ɗin sau 4 ne kacal ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga 😬😬😬

28/11/2023

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta fitar da ƴan wasan da zasu buga mata wasan gode a gasar Zakarun Turai da ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Napoli 🤝

03/11/2023

Jude Bellingham ya lashe kyautar Gwarzon ɗan Wasan watan October.

02/11/2023

MESSI YAYI KARIN HASKE AKAN HAMAYYARSA DA CRISTIANO RONALDO.

Ɗan jarida yake tambayar messi: "Yanzu ka lashe kyautar Ballon d'Or na takwas inda yanzu ka tsere wa Cristiano Ronaldo da guda 3 kana da 8 shi kuma yana da 5. Shin ko gasar taku kare kenan?”.

Messi: "Gasa ce mai cike da ban al'ajabi da muka ɗauki tsawon lokaci a tsakanin mu".

"Cristiano Ronaldo gwanine sosai a fannin motsa jiki, kuma yana da kyau sosai a ƙwallon ƙafa kuma ina tsammanin mun amfana da junanmu saboda dukkan mu mun kasance muna gasa da juna koyaushe kowannenmu yana son ya sami nasara kuma ya lashe komai".

"Ina tsammanin lokaci ne mai kyau sosai a gare mu da kuma dukkanin waɗanda ke son ƙwallon ƙafa gaba ɗaya".

“Abin da muka yi duka a tsawon wannan lokacin abu ne na yabawa wasu ke cewa abu ne mai Sauƙi a kai ƙololuwar sama, amma a zauna ɗin shine wuya kamar yadda mukayi da Ronaldo. Mun zauna a saman tsawon shekaru goma zuwa goma sha biyar, hakan yana da matukar wahala.

"Yana da matukar wahala a ci gaba a wannan matakin kuma ina tsammanin abu ne mai kyau da kuma tarihi ne da muka ajiye da za'a dinga tunawa a ƙwallon ƙafa ga duk wani ma'abocin ƙwallon ƙafa ko wanda ke jin daɗin kwallon kafa".

01/11/2023
Lawan M Ahmad Karaye

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Kano