06/05/2026
ZINA TA YI ARHA, AURE YA YI TSADA.
Yau idan kana da N500,000 a aljihunka, da wuya wannan kuษin su ishe ka ka yi aure saboda tsadar al'ada, kayan lefe, da shirye-shiryen biki da muka kakaba wa kanmu. Amma abin takaici da tashin hankali; da N50,000, N10,000, ko ma kalaman daษin baki kawai, zaka iya kai yarinyar mutane ษakin hotel domin ka biya buฦatar haram. Subhanallah...
Mun wayi gari a cikin wata al'umma da muka tsananta abin da Allah Ya sauฦaฦa (Aure), sannan muka sauฦaฦa abin da Allah Ya haramta (Zina).
Wannan gaskiya ce mai ษaci wacce dole ne mu fuskance ta ta fuska uku:
1. Zuwa Ga Iyaye:
Don Allah a duba tsarin da ake ษora wa matasa masu neman aure. Yawan buฦatun maฦudan kuษaษe da gasar biki sune suke tsoratar da samari masu kishi da natsuwa. Wannan matsin lissafin shine yake sa yara mata su daษe a gida har shaiษan ya samu damar jefa su a halaka. Sauฦaฦa aure shine babbar garkuwar al'umma daga rushewa.
2. Zuwa Ga 'Yan Mata:
'Yar uwa, ki san darajar kanki, Jikinki da mutuncinki sun fi ฦarfin N50k, shawarma, ko sayen sabuwar wayar hannu. Kada ki yarda wani ษataccen namiji ya sayi lahirarki da ษan abin duniya da zai ฦare a rana ษaya. Duk namijin da ba zai iya zuwa wajen iyayenki ya neme ki da aure ba, baya ฦaunarki, yaudararki kawai zai yi ya watsar.
3. Zuwa Ga Samari:
Dan'uwa, ka ji tsoron Allah, Kuษin da kake ษatarwa wajen kai matan mutane hotel, idan ka tara su wallahi zasu iya yi maka aure na halas ka samu natsuwa a rayuwarka. Ka tuna cewa duk abin da ka yi wa 'yar wani, akwai wanda shima yake jiran 'yarka ko ฦanwarka a gaba.
Dole ne mu farka daga wannan baccin, mu koma kan tsarin addininmu kafin musiba ta gama mamaye mu gaba ษaya.
Allah Ya sauฦaฦa mana al'amuran aure, Ya raba mu da kowace irin hanyar alfasha.
4โฃ7โฃ
21/04/2026
DARUSAN DA KUKA JIMA KUNA JIRA.. Da farko ina son ka nutsu, ka ajiye duk wani abu da kake yi a gefe, ka bani cikakken hankalinka. Darusa ne masu tsananin ษaci, amma idan ka hadiye su kayi aiki dasu, ko an wayi gari kowa ya guje ka, zaka yi rayuwa cikin 'yanci
Na farko, Ka gane cewa babu wanda yake son ka saboda KAI, kowa yana son ka ne saboda abin da zaka iya yi masa ko irin farin cikin da kake sa shi a ciki. Ranar da karfinka ya kare baka da abin bayarwa, a ranar zaka gane cewa babu tsantsar soyayya a duniya sai ta mahaifiya.
Na biyu, Duk irin alakar da ke tsakaninka da mutum, kada ka yarda ka dora lissafin arzikinka ko nasararka a kansa. Iyayenka, 'yan uwanka, ko abokan arziki, duk zasu iya canzawa ko su mutu su bar ka a yanke. Tashi ka gina kanka da karfinka, ta yadda koda kowa ya guje ka, zaka iya tsayawa da kafafunka babu fargaba.
Na uku, Mutumin da yake kokarin ganin bayanka ba daga sama zai fado ba. Karkai mamakin wanda kuke dariya daya, kuke cin abinci guda, wanda ya san irin ribar da kake samu, shine zai fara jin haushin ci gabanka a boye saboda baya son ka wuce shi.
Na hudu, Namijin da ya auri mace domin kyawun fuskarta kawai ba tare da duba hankalinta da natsuwarta ba, tamkar mutumin da ya sayi gida ne saboda kyawun fenti ba tare da duba karfin harsashin ginin ba. Idan fentin ya kankare, asarar ta bayyana.
Na biyar, ka fahimci cewa Asalin halin mace yana bayyana ne a lokacin da namijin da take tare dashi ya dawo bashi da ko sisi. Shi kuma namiji Asalin halinsa yana bayyana ne a lokacin da ya samu komai na rayuwa a hannunsa(kuษi/muฦami), dan haka wanan canjin ba sabon hali bane, zamani ne kawai ya goge masa makeup.
A ฦarshe, zaka iya kyamatar wannan gaskiyar kaci gaba da gina rayuwarka a kan kuskure, amma ina tabbatar maka; wata rana duniya zata tilasta maka koyon wadannan darussan a aikace, kuma a lokacin zakai kuka da nadama. Wannan ba rubutu ne na neman a burge ka ba, allurar farkarwa ce na coka maka ita.
4โฃ7โฃ
21/04/2026
Wata Macen sai tayi sati babu Data, Maza kuduba mai sunan mahaifiyarku albarkacin wannan Sunan, A sa mata Data 1GB๐ฅฐ
21/04/2026
โWelcome to Kano โ Heart of Northern Nigeria โค๏ธโ
4โฃ7โฃ
21/04/2026
๐จ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐....
4โฃ7โฃ
21/04/2026
KA KULA DA ZUCIYAR KA DOMIN BA KOWACE IRIN MACE BACE TA DACE DA GURBI A CIKIN TA
Matashi ka sani zuciyar ka ba filin wasa ba ce, ba wuri ne da kowa zai shigo ya fita yadda ya ga dama ba.
A yau, mutane da yawa suna baiwa soyayya muhimmanci amma sun manta da tsaron zuciyarsu.
โข Ba kowace mace da ta nuna kulawa take nufin ta dace da kai ba.
โข Ba kowace dariya take nufin gaskiya ba.
โข Ba kowace kusanci yake nufin makoma ba.
Wasu suna shigowa ne don su ษauki lokaci, ko su ษauki kulawa, ko su bar maka rauni aciki.
Gaskiya mai ษaci:
zuciya mai sauฦin buษewa tana da sauฦin karyewa.
Shi yasa dole ka koyi lura da halaye ba kalamai kaษai ba, ka bada lokaci kafin ka yarda da kowa, ka daina baiwa kowa gurbi a zuciyarka cikin sauri.
Domin wani lokacin, abin da kake kira soyayya gwaji ne kawai.
Zuciyarka na da daraja ka bada ita ga wanda ya cancanta, ba wanda ya zo kawai ba don cika manufa ba.
Tambaya:
Shi wai a ganinku, me ya fi sa mutum saurin bada zuciyarsa a soyayya?
4โฃ7โฃ
02/01/2026
๐ฝโ๐๐ป๐ธ๐ ๐๐๐๐ผโ๐
05/03/2023
โขโโข โขโโฃ โขโโฃโขโโฃ โขโโฃ โขโโฃ
โโฃโ โโโ โฅโฃโโโโ โโโค โโโ
โโฅโ โโโ โโฅโฃโโโ โโโฃ โโโ
โฅโโฅ โฅโโฅ โฅโโคโฅโโฅ โฅโโฅ โฅโโฅ
๐๐๐ ๐ผ๐ก๐ก๐๐ ๐ผ ๐ฟ๐ช๐ ๐จ๐๐ฃ๐๐ ๐ข๐ช๐ ๐ ๐ง๐๐จ๐
โ๏ธ๐ผ๐๐๐ฃ๐๐ ๐ข๐ช๐ ๐๐จ๐ค ๐ ๐ค๐ ๐ข๐ช๐ ๐ ๐๐ช๐ง๐๐คฆโโ๏ธ
๐คฒ๐๐๐จ๐, ๐ข๐ช๐ฉ๐ช๐ฃ๐ ๐๐๐๐๐ฌ๐ ๐ง๐๐๐๐ข๐๐ง๐ ๐โก
๐๐๐๐๐ ๐๐๐ง๐๐๐ฃ ๐ฟ๐ช๐ ๐ผ๐๐๐ฃ๐๐ ๐ข๐ช๐ ๐ ๐ง๐๐จ๐โ
๐๐๐ ๐ผ๐ก๐ก๐๐ ๐๐๐๐๐ง๐๐ ๐๐๐ข๐ช ๐๐๐- ๐๐๐โ๏ธ
๐๐๐ข๐๐ฃ๐๐ฃ, ๐ข๐ช ๐จ๐๐ฃ๐๐ฃ ๐ ๐๐จ๐ ๐ข๐ช๐๐ ๐ ๐๐ง๐๐๐ฃโ
โค๏ธ๐๐ช๐๐๐ฎ๐๐ฃ ๐ข๐ช ๐ ๐๐จ๐ ๐ข๐ช๐๐ma ๐๐๐๐ก๐๐ฎ
17/01/2023
๐จ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐....
01/12/2022
May Allah protects us from any of an evils acts and shaytan