25/11/2021
Arsene Wenger: Mikel Arteta na fatan tsohon kocin kungiyar zai koma Gunners.
Mikel Arteta ya lashe FA Cup karo biyu a matakin dan wasa a lokacin da Arsene Wenger ke kocin Arsenal
Mai horar da Arsenal, Mikel Arteta, ya ce yana son ya dawo da tsoho kociyan Gunners, Arsene Wenger kungiyar, ya kuma ce ya tuntube shi kan batun.
Wenger, mai shekara 72, ya ja ragamar Arsenal ta lashe kofin Premier League uku da FA Cup karo bakwai a kaka 22 da ya horar da kungiyar da ke Arewacin Landan
Mikel Arteta ya yi kaka biyar yana buga wa Arsenal tamaula a karkashin Wenger.
"Za mu yi murna ya dawo kusa da mu," in ji Arteta.
"Ina jin zai ji dadi ganin yanayin da zai samar, saboda yadda ake girmama shi da yadda kowa ke kaunarsa a kungiyar, saboda aikin da ya gudanar."
Arteta ya maye gurbin Unai Emery a matakin kociyan Gunners a Disambar 2019, wata 19 bayan da Wenger ya yi ritaya a karshen kakar 2017-18, wanda ya ja ragamar kungiyar karawa 1,235.
Arteta ya lashe FA Cup a matakin kociyan kungiyar a 2019-20, sai dai kuma kungiyar ta kare a mataki na takwas a Premier League a bara, karon farko da Gunners ta kasa samun gurbin buga gasar zakarun Turai, bayan shekara 25.
Arsenal tana ta biyar a kan teburin Premier League, bayan wasa 12 a kakar nan, wadda za ta kara da Newcastle United ranar Asabar.