Kwallo

Kwallo

Share

A wannan page zamu din ga kawo muku labaran wasanni da dumi dumin su

13/04/2026

Arsenal na neman ɓarar da garin Man U kan Jeremy Monga, Liverpool da Chelsea na son Kroupi

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United na son kara karfin tsakiyarta a wannan bazarar, inda take sa ido kan dan wasan tsakiya na Manchester United, Manuel Ugarte mai shekara 25, a matsayin babban burinta. (Football Insider)

Tottenham Hotspur da West Ham United duk suna sha'awar daukar dan wasan tsakiya na Barcelona, Marc Casado mai shekara 22. (Tuttomercato)

Liverpool da Chelsea na shirin fafatawa wajen sayen dan wasan gaba na Bournemouth mai shekara 19, Eli Junior Kroupi, yayin da kungiyar ke shirin amincewa da tayin da zai kai kusan fam miliyan 60. (Caught Offside)

Coventry City na son mayar da aron mai tsaron ragar Brighton, Carl Rushworth mai shekara 24, ya zama na dindindin a bazara, amma za su fuskanci gogayya daga Leeds United. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na Leeds United, Joel Piroe mai shekara 26, na iya barin kungiyar a wannan bazarar sakamakon rashin samun damar taka leda, inda ake ganin Rangers na iya zama sabuwar kungiyarsa. (Football Insider)

Manchester United na shirin daukar matashin dan wasan gefe na Leicester City mai shekara 16, Jeremy Monga, a wani mataki mai ba wa mutane mamaki, yayin da Manchester City da Arsenal ma ke sha'awar dan wasan. (Teamtalk)

Fulham na duba yiwuwar kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen, Malik Tillman mai shekara 23, yayin da suke shirin rayuwa ba tare da Harry Wilson ba, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Daily Mail)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

11/04/2026

Arsenal da Chelsea da Man U da Real Madrid na son Smit, Carrick na daf da zama kocin Man U

Tottenham na kan gaba wajen neman dan wasan baya na hagu na Liverpool da Scotland, Andy Robertson mai shekaru 32, kyauta a bazara, idan har kungiyar ta Spurs ta kauce wa faduwa daga gasar bana. (Athletic)

Chelsea na iya sayar da dan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez a bazara idan har kungiyar ba ta samu tikitin shiga gasar Zakarun Turai ta kakar mai zuwa ba, inda ake alakanta dan wasan mai shekaru 25 da Real Madrid. (AS)

Manchester City ta gudanar da tattaunawa ta farko da Sporting kan daukar dan wasan tsakiya na Denmark, Morten Hjulmand mai shekaru 26, wanda kuma Manchester United da Juventus ke nema. (A Bola)

Dan wasan tsakiya na Atalanta Ederson ya ki amincewa da tayin kungiyoyi da s**a hada da Arsenal, Manchester United da Newcastle, yayin da dan wasan Brazil mai shekaru 26 ke sha'awar komawa Atletico Madrid. (AS)

Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester United, Newcastle, Barcelona da Real Madrid duk suna zawarcin dan wasan tsakiya na Netherlands da AZ Alkmaar, Kees Smit mai shekaru 20, a bazara. (CaughtOffside)

Manchester United, Arsenal, Chelsea da Paris St-Germain na duba yiwuwar daukar dan wasan gaba na Aston Villa da Ingila, Morgan Rogers mai shekaru 23, a bazara. (Sky Sports)

Arsenal ta yi cikakken nazari kan halin da dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon ke ciki a Newcastle, kuma tana sa ido kan yiwuwar samuwarsa kafin kasuwar bazara. (Teamtalk)

Celtic na shirin sayar da dan wasan gefe na Sweden Benjamin Nygren mai shekaru 24 a bazara, bayan sha'awar da Tottenham ta nuna, kuma ana sa ran fara tattaunawa kan kusan fam miliyan 26, yayin da Brighton, Bournemouth da Valencia suma ke sha'awa. (SportsBoom)

FC Cincinnati na duba hanyoyin daukar dan wasan gaba na Brazil Neymar mai shekaru 34 daga Santos zuwa gasar MLS, inda aka fara tattaunawa ta farko. (Athletic)

Mai horaswa na rikon kwarya Michael Carrick na kan gaba wajen zama cikakken kocin Manchester United, bayan tsohon dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekaru 44 ya taimaka wa kungiyar samun maki 23 cikin 30 tun bayan da ya karbi ragamar aiki a watan Janairu. (Talksport)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

10/04/2026

Manyan ƙungiyoyi na zawarcin Rogers, Liverpool da City da Arsenal na son Cameroon

Dan wasan tsakiya na Aston Villa da Ingila, Morgan Rogers, na iya jan hankali a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, bayan da Arsenal, da Manchester United da Chelsea s**a sabunta sha'awarsu kan dan wasan mai shekaru 23. (Times)

Haka kuma, Bayern Munich na daga cikin kungiyoyin da ke sha'awar Rogers, kuma za su iya fafatawa da kungiyoyin Premier League domin daukar sa. (Mirror)

Kungiyar Juventus na kara samun kwarin gwiwa wajen kokarin daukar golan Brazil Alisson Becker daga Liverpool, inda rahotanni ke cewa dan wasan mai shekaru 33 na bude kofar komawa gasar Serie A. (La Gazzetta dello Sport)

Masu kungiyar Liverpool, wato Fenway Sports Group, sun yi imanin cewa dan kasar Holland Arne Slot zai ci gaba da zama kocin kungiyar a kakar wasa mai zuwa duk da rashin nasarar da s**a yi a wannan makon. (Telegraph)

Ana sa ran Aston Villa na cikin kungiyoyin da ke son daukar golan Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekaru 23 a wannan bazara. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Enzo Fernandez, tare da wakilinsa sun ba kungiyar hakuri kan kalaman da ya yi yayin da yake buga wa kasarsa wasa a Argentina, inda ya ambaci yiwuwar komawa Real Madrid. (Sky Sports)

Real Madrid na iya kara kaimi wajen kokarin daukar dan wasan gefe na Bayern Munich da tawagar France, Michael Olise mai shekaru 24, wanda kuma Liverpool ke zawarcinsa, a kasuwar bazara. (Christian Falk)

Liverpool da Manchester City sun shiga sahun Arsenal wajen zawarcin matashin dan wasan gaba na Bayer Leverkusen da Cameroon, Christian Kofane mai shekaru 19. (Teamtalk)

Har yanzu kungiyar Nottingham Forest ba ta karbi wani sabon tayi a hukumance ba kan dan wasan tsakiya na Ingila, Elliot Anderson mai shekaru 23, amma tana shirin karbar tayi kafin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda Manchester City da Manchester United ke sha'awar sa. (Talksport)

Kungiyar RB Leipzig da Castello Lukeba sun cimma matsaya cewa dan wasan baya zai bar kungiyar a wannan bazara ba, yayin da Arsenal, da Chelsea, da Liverpool da Manchester United ke duba yiwuwar daukar sa. (Teamtalk)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

09/04/2026

Dortmund ta nace wa Sancho, Tottenham ta matsa a kan Trafford
Sa'o'i 2 da s**a wuce

A karo na uku Borussia Dortmund za ta sake duba yuwuwar zawarcin danwasan gaba na gefe Jadon Sancho, dan Ingila mai shekara 26, wanda ke zaman aro a Aston Villa, kuma ake sa ran zai bar Manchester United, a matsayin wanda ba wani kwantiragi a kansa a bazaran nan. (Telegraph)

Tottenham na kara matsa lamba domin sayen mai tsaron ragar Manchester City, da Ingila James Trafford a bazaran nan, kuma golan mai shekara 23, na daga wadanda kungiyar ke matukar so ta saya a cefanen da za ta yi. (Teamtalk)

Arsenal na fatan ganin ta karfafa bayanta a bazaran nan,inda take son sayen dan bayan Real Madrid Victor Valdepenas, dan Sifaniya mai shekara 19, da kuma Jaco Ramon na kungiyar Como ta Sifaniya, wanda yake tawagar Sifaniya ta 'yan kasa da shekara 21, a cikin wadanda take son saye. (Caughtoffside)

Nottingham Forest na sa ran danwasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson ya tafiko dai Manchester United ko kuma Manchester City, idan har ya bar kungiyar a bazaran nan, to amma kuma kungiyar tasa na neman kudin da ya kai fam miliyan 100 zuwamiliyan 120, a kan dan wasan mai shekara 23. (Florian Plettenberg)

Ba a sa ran Everton za ta nemi biyan fam miliyan 50 dominsayen danwasan gaba na gefer na Ingila Jack Grealish, kamar yadda tanadin yake a kwantiraginsa na aro zuwa Manchester City, to amma kungiyar tana da kwarin gwiwa cewa za a iya cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasan mai shekara 30 ya ci gaba da zama a Merseyside. (Athletic)

Manchester City ta bi sahun sauran kungiyoyi da dama na Jamus (Bundesliga) da na Firmiya, wajen gogayyar sayen dan wasan tsakiya na Hertha Berlin, Kennet Eichhorn, dan Jamus mai shekara 16. (Fabrizio Romano)

Dan wasan gaba na gefe, Gabriel Martinelli, dan Brazil mai shekara 24, n matsa wa domin ganin ya ci gaba da zama a Arsenal, yayin da alamu ke nuna cewa kila kungiyar ta sayar da shi a bazaran nan. (Football Insider)

A shrye Leeds United take domin ta bar dan wasan gaba na Sifaniya Mateo Joseph, mai shekara 22, ya bar kungiyar a bazaran nan, bayan zaman aro da ya yi a Mallorca. (Football Insider)

Chelsea ba ta da niyyar sayar da matashin dan wasan baya na Ingila Josh Acheampong, mai shekara 19 a lokacin bazara, duk da cewa bai taka leda sosai ba a Chelsean. (Express)

Kociyan Plate, Eduardo Coudet da kansa ya tuntubi Chelsea, da dan wasan gaba na gefe na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21, a kan aro na shekara daya. (TyC via Football London)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

07/04/2026

Liverpool na harin Camavinga, Barca da Juventus na son Silva

Liverpool na cikin shirin ko ta kwana wajen siyen ɗan wasan Real Madrid Eduard Camavinga, da Liverpool din ta jima tana son ɗaukarsa. (L'Equipe - in French)

Barcelona da Juventus na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Manchester City Bernardo Silva, ba tare da wani kwantaragi na kansa ba, a wannan kaka. (Sky Sports)

Juventus na da kwaringuiwar cewar samun gurbin buga gasar Champion zai iya basu gurbin ɗauko dan wasan Tsakiyar Uruguay Manel Ugarte kan fam miliyan talatin da biyar ga Manchester United. (Corriere dello Sport - in Italian)

Arsenal na da dama kan Liverpool, wajen aniyar ta na ɗauko ɗan wasan gefen RB Leipzig Yan Diomande. (Caught Offside)

Tottenham ba zata amince da tayin kyaftin ɗin ta Cristian Romero ƙasa da euro miliyan 50 ba (£43.6m), yayin da Atlentico Madrid ke harin ɗan wasan. (Fichajes - in Spanish)

Idan har ta tabbata Vinicius zai bar Real Madrid, Paris St-Germain ko ƙungiyoyin da ke buga Premier ne kaɗai mafita gare shi. (ESPN)

Newscastle ta shiga sahun ƙungiyoyin da ke Turai da ke son mai tsaron bayan Werder Bremen Karim Coulibaly. (Fabrizio Romano)

Liverpool da Manchester sun ƙara matsawa kan ganin sun ɗauko ɗan wasan Monaco da Fransa Maghnes Akliouche. (Teamtalk)

Borussia Dortmund na son ɗauko ɗan wasan Strasbourg da Belgium Diego Moreira, sai dai Chelsea na son ɗan wasan. (Florian Plettenberg)

Roma na son ɗaukar ɗan wasan Midtjylland Dario Osorio, da Franculino, yayin da farashin ƴan wasan gefen na Chile da Guinea-Bissau ya kai euro miliyan 55m (£48m). (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

05/04/2026

Arsenal za ta yi gogayya da Liverpool wajen neman Gordon, Chelsea na son Barco

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na sha'awar daukar dan bayan Argentina Valentín Barco mai shekara 21 daga Strasbourg (Talksport).

Kungiyar Inter Milan na son golan Tottenham Hotspur, Guglielmo Vicario mai shekaru 29, domin zama zabinsu na farko a raga (CalcioMercato).

Kungiyar Liverpool na shirin kara daukar dan baya, inda ake sa ran za ta maida hankali kan dan wasan Italiya Marco Palestra mai shekaru 21 daga Atalanta a wannan bazara (CaughtOffside).

Manchester United na daga cikin kungiyoyin Premier League da ke bibiyar dan bayan Arewacin Ireland Tom Atcheson mai shekaru 19 na Blackburn Rovers (Teamtalk).

Sunderland na iya yunkurin daukar dan wasan tsakiya mai kai hari Sergio Arribas mai shekaru 24 daga Almeria, idan daraktan wasanni Florent Ghisolfi ya ci gaba da nuna sha'awarsa (Sport Witness).

Arsenal na shirin gogayya da Liverpool wajen daukar dan gaban Newcastle United Anthony Gordon mai shekaru 25 (Football Transfers).

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

04/04/2026

Man U da Man City na son Anderson, Liverpool za ta sallami 'yan wasan da s**a gaza

Kungiyoyin Manchester United da Manchester City na fafatawa domin sayen dan wasan tsakiyar fili na Nottingham Forest, Elliot Anderson mai shekaru 23. Kungiyoyin na son kammala cinikin cikin gaggawa a wannan bazara, ganin irin rawar da zai taka a gasar kofin duniya tare a Ingila zai iya daga darajarsa zuwa sama da fam miliyan 100. (The Sun)

Babu tabbas kan makomar kyaftin din Manchester United, Bruno Fernandes mai shekaru 31, musamman idan kungiyar ta samu tayin kudi mai tsoka daga kungiyoyi irin su Paris Saint-Germain da Bayern Munich a wannan bazara. (CaughtOffside)

Sai dai kuma Manchester United na da niyyar rike Fernandes duk da cewa akwai sharadin sakin sa a kwantiraginsa na fam miliyan 57. (Daily Express)

Kungiyar Liverpool na shirin yin garambawul ga 'yan wasanta da ba sa taka rawar gani ba, inda shugabannin Anfield ke shirin amincewa da manyan sauye-sauye a lokacin bazara. (Daily Star)

Liverpool na iya fuskantar gogayya daga Manchester United da Newcastle United idan tana son dauko dan wasan tsakiya na Juventus, Khephren Thuram mai shekaru 25. (Daily Mirror)

Dan wasan baya na tawagar matasa ta Jamus 'yan kasa da shekara 21, Karim Coulibaly, na shirin barin Werder Bremen a wannan bazara, inda ake cewa Newcastle na daga cikin kungiyoyi biyar da ke nemansa. (Bild/Chronicle)

Dan wasan tsakiya na Ecuador, Moises Caicedo mai shekaru 24, ya ce yana da niyyar ci gaba da zama a Chelsea amma bai cire yiwuwar komawa Real Madrid nan gaba ba. (AS)

Mai tsaron raga na Brighton & Hove Albion kuma dan kasar Netherlands, Bart Verbruggen mai shekaru 23, na iya zama zabin Bayern Munich a wannan bazara, yayin da su ma Tottenham da Newcastle ke zawarcinsa. (Teamtalk)

Dan wasan baya na Colombia, Jhon Lucumi mai shekaru 27, na dab da barin Bologna a bazara, kuma Sunderland na ci gaba da sha'awar daukarsa bayan sun kasa samun sa a watannin baya. (ForzaRoma/Sport Witness)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

03/04/2026

Arsenal da Man City da PSG na neman Olmo, Salah zai koma Saudiyya

Kungiyar RB Leipzig ta sanya farashin fam miliyan 87 kan ɗan wasan gefe na Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 18, wanda kungiyoyin Liverpool da Manchester United ke zawarcinsa. (Sky Sports)

Kungiyoyin Saudi Pro League na ƙara ƙaimi wajen zawarcin ɗan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah mai shekara 33, kuma suna da ƙwarin gwiwar kammala yarjejeniya kafin gasar cin kofin duniya ta wannan bazarar. (Teamtalk)

Kungiyar Everton na ƙara samun kwarin gwiwa cewa ɗan wasan gefe na Manchester City da Ingila Jack Grealish mai shekara 30, wanda ke zaman aro, zai ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Daily Mail)

Kungiyoyin Manchester City da Paris Saint-Germain da kuma Arsenal duk suna sha'awar ɗan wasan Spain Dani Olmo mai shekara 27, yayin da Barcelona ta bude kofar sayar da shi. (Fichajes)

Kungiyar Atletico Madrid na dab da kulla yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Brazil daga Atalanta Ederson mai shekara 26, wanda kuma Manchester United da Manchester City ke sha'awa. (Fabrizio Romano)

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola mai shekara 55 ba zai yanke hukunci kan makomarsa a kungiyar ba sai karshen kakar wasa. (Telegraph)

Kungiyar Manchester United na shirin ƙara sabbin 'yan wasan tsakiya guda biyu a wannan bazarar, inda ake take duba yiwuwar daukar 'yan wasan Ingila Elliot Anderson na Nottingham Forest, da Adam Wharton na Crystal Palace, da kuma ɗan Italiya na Newcastle United Sandro Tonali. (Givemesport)

Kungiyar Arsenal na ci gaba da nuna sha'awar sayen ɗan wasan baya na Spain mai shekara 19 Victor Valdepenas daga Real Madrid, amma za ta fuskanci gasa daga AC Milan. (Caughtoffside)

Ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva zai bar Manchester City kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a watan Yuni, inda tuni yake nazarin zabinsa. (Fabrizio Romano)

Kungiyar Barcelona na shirin sayen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi mai shekara 24 a wannan bazarar. (Fichajes)

Ɗan wasan gaba na Netherlands da West Ham United Crysencio Summerville mai shekara 24 na cikin jerin 'yan wasan da kungiyoyi kamar Aston Villa da Everton da Tottenham Hotspur da Marseille da Napoli ke sa ido a kansa. (Teamtalk)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi? Wacce kungiya ce tafi dacewa da Olmo a England?

02/04/2026

Wakilan Tonali sun tuntuɓi Real Madrid, Liverpool da Man U na zawarcin Diomande

Ƙungiyar Everton na bibiyar halin da kwantiragin ɗan wasan tsakiya na Ingila John Stones yake ciki a Manchester City, bayan rahotanni sun nuna cewa ba a sa ran ba shi sabon yarjejeniya. Stones mai shekara 31 ya taɓa taka leda a Everton. (Talksport)

A wani bangare kuma, wakilan ɗan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali sun tuntubi Real Madrid yayin da suke neman sabuwar ƙungiya ga ɗan wasan mai shekara 25. Haka kuma Manchester City na cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan na Newcastle United. (Teamtalk)

Ƙungiyar Barcelona ce ke kan gaba wajen neman ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva mai shekara 31 daga Manchester City kyauta a lokacin bazara. (The Sun)

An sanar da aniyar cefanar da ɗan bayan Netherlands Denzel Dumfries mai shekara 29 ga kungiyoyin gasar Premier League ciki har da Liverpool, Manchester City, Manchester United, Chelsea, Tottenham Hotspur da Newcastle United. (Teamtalk)

Manchester United na sha'awar ɗan bayan Sweden Samuel Dahl mai shekara 23 daga Benfica, inda kungiyar ta tura wakilanta suna kallon murza ledar dan wasan sau fiye da 10 a wannan kakar. (Record/SportWitness)

Arsenal na bibiyar matashin ɗan wasan gaba na Bayer Leverkusen Christian Kofane mai shekara 19, inda ƙungiyar ta Jamus ke neman kusan fam miliyan 60 domin sayar da shi. (Florian Plettenberg)

Zaɓin sayen ɗan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford da Barcelona ke da shi na fam miliyan 26 ya ƙare a watan Maris, wanda ke nufin dole ne yanzu su tattauna kai tsaye da Manchester United kan farashinsa. (Cadena SER)

Kungiyoyin Manchester City da Liverpool da Chelsea na sa ido kan ɗan bayan Faransa Jules Kounde mai shekara 27 wanda ke taka leda a Barcelona. (Mundo Deportivo)

Celta Vigo na son ɗan wasan tsakiya na Spain Fer Lopez mai shekara 21 ya ci gaba da zama a ƙungiyar bayan karewar aro daga Wolverhampton Wanderers. (Faro de Vigo/SportWitness)

Mai horarwa Roberto De Zerbi na son sayo ɗan wasan tsakiya na Italiya Manuel Locatelli mai shekara 28 daga Juventus don taka leda a Tottenham Hotspur a lokacin bazara. (Calciomercato)

A ƙarshe, Manchester United da Liverpool na zawarcin ɗan wasan gefe na Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 19 daga RB Leipzig. (Sportsboom)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

01/04/2026

City na son Anderson, United na harin Tonali, Liverpool za ta ɗauko Conceicao

Manchester City ta shiga gaban Manchester United a yuƙurin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest Elliot Anderson, kafin fara buga gasar cin kofin duniya. (Mail - subscription required)

Manchester United ta sami ƙarfin guiwa ɗauko ɗan wasan tsakiyar Italiya Sandro Tonali, yayin da Newcastle ta buɗe ƙofar siyar da ƴan wasanta, a farashi mai kyau a wannan kakar. (Sun)

Liverpool na son siyen ɗan wasan Portugal da Juventus Francisco Conceicao, a mastyin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah, idan ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar nan. (Gazzetta - in Italian)

Manchester United na cikin ƙungiyoyi da ke son ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Brazil Joao Gomes, da zai iya kasancewa a kasuwa kan fam miliyan 39 idan har Wolves ta faɗa a gasar Premier. (Caught Offside)

Manchester United na harin siyen ɗan wasan bayan Toulouse da Ingila Charlie Cresswell a wannan kaka. (Teamtalk)

Bayern Munich ba su da sha'awar siyen ɗan wasan tsakiyar Ingila Phil Foden daga Manchester City saboda basu da kuɗin da za su iya siyen sa a wannan kakar. (Bild - in German)

Ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, na son ci gaba da zama a Manchester United a kaka mai zuwa, saboda fatan da yake na zai samu damaidan har Michael Carrick, ya kasancewa wanda zai ci gaba da horar da yan wasan ƙungiyar. (Mail - subscription required)

Arsenal da Manchester City ne wadan da s**a fi nuna son ɗaukar ɗan wasan Igila da Newcastle Tino Livramento idan ya yaƙi sabunta kwantaraginsa da Newcastle. (Football Insider)

Villarrael na son ɗan wasan Crystal Palace Ismaila Sarr a wannan kaka. (Fichajes - in Spanish)

Nico Schlotterbeck ya musanta shiga kwantaragi da Borussia Dortmund, wanda hakan ya baiwa Real Madrid sabon fata na damar ɗaukar ɗan wasan. (AS - in Spanish)

Ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, da ke taka leda a matsayin ɗan wasan aro a Barcelona, na cikin ƴan wasa biyar da za su bar Manchester united a wannan kaka, inda United ɗin ke fatan samun fam miliyan ɗari idan ta siyar su. (Sky Sports)

Barcelona na son ɗan wasan Benfica Andreas Schjelderup a matsayin wadan zai maye Rashforda a mastayin ɗan wasan ƙungiyar na din-din-din, bayan Rashford ɗin ya kamala zama amatsayin ɗan wasan Aro daga Manchester United a wannan kaka. (Record - in Portuguese, subscription required)

Ɗan wasan gaban Faransa Hugo Ekitike ya shiga jerin ƴan wasan da ke gaba da Real Madrid ke son sauka ganin irin ƙwazon da dan wasan yayi a wannan kaka a Liverpool. (Teamtalk)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

31/03/2026

Madrid na son Fernandez, Juventus na harin Ugarte na United

Real Madrid za ta duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, ko ɗan wasan tsakiyar Ingila da ke taka leda a Crystal Palace Adam Wharton, idan ta gaza siyen ɗan wasan tsakiyar Manchester City Rodri, a kakar wasan nan. (Mundo Deportivo)

Sai Real Madrid ta yi wa Manchester City tayin fam miliyan hamsin sannan za ta ja hankalin City ta siyar mata da Rodri. (Football Insider)

Juventus na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Uruguay Manuel Ugarte. (Gazzetta)

Newcastle ta ƙarfafa aniyarta ta ci gaba da riƙe ɗan wasan tsakiyar Italiya Sandro Tonali a kakar wasannin nan, sakamakon gazawar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Seria A siyensa. (Talksport)

Newcastle ta amince da tayin siyen ɗan wasan gefen Independiente del Valle Johan Martinez. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan baya na Manchester City da Netherlands Nathan Ake na duba yiwuwar komawa taka leda a tsohuwar ƙungiyarsa ta Chelsea. (Sun)

Manchester United da Arsenal na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan gaban Barcelona Ferran Torres a wannan kaka. (Fichajes)

Chelsea da Liverpool ne a kan gaba wajen rige-rigen ganin sun yi nasarar daukar ɗan wasan tsakiyar Senegal Lamine Camara daga Monaco. (Caught Offside)

Bologna na duba yiwuwar siyen ɗan wasan Nottingham Forest Lorenzo Lucca, da ke matsayin dan wasan aro a Napoli zuwa ƙarshen kakar wasanni. (Gazzetta)

Tattaunawa don tsawaita kwantaragin ɗan wasan bayan Ingila Tino Livramento da Newcastle ta zo ƙarshe, sai dai an gaza cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu, wanda hakan ya bai wa ɗan wasan damar barin ƙungiyar a kakar nan. (Football Insider)

Liverpool za ta fuskanci gogayya sosai daga Bayern Munich wajen siyen ɗan wasan bayan Faransa Maxence Lacroix daga Crystal Palace. (Teamtalk)

Babban cefanen da Barcelona ke son yi na siyen ƴan wasanta a kakar wasannin da ake ciki, shi ne siyen ɗan wasan Atlentico Madrid Julian Alvarez. (Mundo Deportivo)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

30/03/2026

Bayern na fargaba kan masu son ɗaukar Kean daga Saudiyya, Bernardo Silva na son barin Manchester City

Shugaban Bayern Munich Uli Hoeness na kaffa-kaffa kan yadda ƙungiyoyin da ke taka leda a gasar ƙwararu a Saudiyya ke ci gaba da jan hankalin ɗan wasan gaban Ingila Harry Keane, a dai-dai lokacin da Bayern ɗin ke tattaunawa da ɗan wasan, kan tsawaita zamansa a ƙungiyar har zuwa 2027. (Kicker - in German)

Ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silava, ya shaidawa Manchester City aniyarsa na shirinsa na barin ƙungiyar, idan kwantaraginsa ta ƙare a ƙarshen kakar wassani. (Caught Offside)

Aston Villa, da Beryern Munichi, da Chelsea da Liverpool na sa ido kan ɗan wasan bayan Crystal Palace Maxence Lacroix. (Teamtalk)

Liverpool da Newcastle United na son ɗaukar ɗan wasan Sporting ɗan asalin Colombia Luis Suarez. (Correio da Manha - in Portuguese)

Babu wata tattaunawa tsakanin ɗan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay, da ƙungiyoyin da ke taka leda a Saudiyy, a yayin da hankalinsa har yanzu ke Napoli da ke Italiya. (Fabrizio Romano)

Barcelona za ta tsawaita kwantarangin ɗan wasan gaba Poland Robert Lewandowski, da kwantaraginsa zai ƙare a kakar wassanin da ake, ciki har da rage masa albashi, da wasu haƙoƙi da za a ringa bashi na irin ƙwazon da yayi a wassanin da ya buga wa ƙungiyar. (Sport - in Spanish)

Juventus na duba yiwuwar ɗauko Lewandowski da ɗan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a Tottenham daga Paris St-Germain, zuwa ƙungiyar. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Chelsea da ɗan wasan bayan Faransa Malo Gusto, 22, sun ce Liam Rosenior shi ne gwarzon mai horar da ƙungiyar duk kuwa da s**ar da ake yi masa kan rashin kataɓus ɗin da s**a yi. (ESPN)

Inter Miami ta fara tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Brazil Casemiro kan yiwuwar komawa ƙungiyar don ci gaba da taka leda, yayin da zai bar Manchester United a ƙarshen kakar wassani, sai dai akwai tayi da yake samun daga wasu manyan ƙungiyoyi a Turai da Saudiyya.

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Address

Kano