Yanda zakayi kudi sharp
ka ciyo bashin 10B a banki, kayi amfani da kuɗin ka siye bankin, sai ka goge bashin naka☹️🏃🏻♂️
MAZA A YAU
Mata iyayen mune. Bamun buɗe gidan nan dancin mutunci mata bane a a saidai basu shawarwari da kare kansu daga faɗawa halaka.
Da nunawa maza mahimmancin su a gurin mace
Big shout-out to my newest top fans! Maryam Umar, Muheebbat Adam, Engr Rabiu Lawan Jahun, Amina Sulaiman, Hussaina Wan
01/06/2026
Ta Rayu Kamar Zakanya, Amma Yanzu Tana Bayan Ƙasa!
Ina cikin gudanar da aikin dare (night duty) a asibiti, kimanin ƙarfe goma na dare, shiru ya ratsa ko'ina sai sautin nishi da takun ƙafafun marasa lafiya jefi-jefi.
Kwatsam, sai ga wata baiwar Allah ta shigo cikin asibiti, damuwa fal a fuskarta, hannunta guda dafe da cikinta yayin da take tare da wani ƙaramin yaro. Daga yanayin yadda take nishi da murƙususu, da inda take dafewa alamomi s**a dan nuna min kamar appendicitis ke damunta, sai dai a matsayina na ma'aikaciyar lafiya, ban hanzarta yanke hukunci ba har sai likita ya duba ta. Cikin tausayawa, na tallafa mata da taimakon gaggawa don rage mata radadin zafin kafin gari ya waye.
Washegari da safe, cikin ikon Allah sai ga likitan ya shigo. Bayan dogon bincike da gwaje-gwaje na kimiyya, sakamako ya tabbatar da abin da nake zargi wato Appendicitis ne! Aka nemi likitan fida (surgeon) kuma aka tsara dukkan abubuwan da s**a dace don yin aikin a safiyar gobe da yardar Allah.
A take muka sanya ta a tsarin Nil Per Oral (NPO) wato azumin jiran aiki, inda aka hana ta cin komai ko shan ruwa, duk da tsananin buƙatar da take da ita a lokacin.
Wayewar gari da ƙarfe takwas na safe, likita ya iso. Abin mamaki, ita da kanta ta mike da ƙafafunta ta shiga dakin tiyata (theatre) ba tare da fargaba ba. Aikin bai zo da sauƙi ba, domin likitan ya sha wahala kwarai saboda tsananin ƙiba da tarin kitse na jikinta, amma cikin ikon Allah, aka kammala aikin cikin nasara mai ban mamaki. Tana farkawa daga maganin barci, harshenta bai gaza ba, kalmar Shahada da kiran sallah ne s**a riƙa fita daga bakinta.
Kamar tatsuniya, ita da kanta ta tashi daga gadon fida, ta taka da ƙafafunta har zuwa dakin da aka tanadar mata don hutawa! Kowa ya cika da mamaki hakan.
Bayan sa'o'i ashirin da hudu (24 hours after surgery), ƙishirwa ta addabi ta. Haka take jin sa'o'in nan kamar shekara guda saboda tsananin son ruwa, ta shiga hargowa da bala'i da mutane saboda an hana ta sha.
Ganin halin da ake ciki, likita ya bayar da ikon a ba ta ruwan Lipton cokali ko ludayi biyu kacal don ta jika makogwaronta. Haka aka yi kuwa, daga nan ne fa asibitin ta dan lafa daga hayaniyarta, inda ta koma tamkar 'yar wasan kwaikwayo (comedy) saboda hira da barkwancinta, duk da cewa a tarihinta na baya an bayyana cewa tana fama da matsalar miyagun aljannu masu haɗari.
Jiya da yamma lokacin sallar magriba, na ce bari na leƙa asibitin domin na sanya wayata a caji. Ina shiga na tarar da ita rai a ɓace, tana ta masifa da mahaifiyarta akan an hana ta shan ruwan gora (Mr. V) guda huɗu da aka siyo mata, har ma wai an yi sadaka da su. Tana ta rantse-rantse sai an dawo mata da ruwanta.
Haka, ta ɗauki waya ta kira kira likitan da kanta tana kai ƙarar cewa an hana ta ruwa. Likitan cikin raha ya rarrashi zuciyarta, yace mata Ki yi haƙuri, ina idar da sallar isha'i zan zo, har tuwo ma zan ba ki ci. Wannan magana ta kwantar mata da hankali, tana jiran isowarsa.
Jim kaɗan bayan wannan takaddama, ina zaune a cikin pharmacy, sai ga mahaifiyar ta, ta rugo da gudu cikin firgici tana kiran ɗauki “A zo a gani, kumfa ne ke fitowa ta hancinta!"
Gabanmu ya fadi! Muka garzaya da gudu zuwa dakinta, amma tuni ta fara nisanta da mu. Mun yi dukkan dabarun neman taimakon gaggawa na lafiya (resuscitation) da za mu iya, amma ina! Lamarin ya ki sauyawa.
A daidai lokacin ne likitan ya ƙaraso cikin dakin, sai dai kash, kamar dama zuwansa take jira, a take dukkan alamun rayuwarta (vital signs) s**a ci gaba da faduwa kasa, har komai ya koma zero!
Ta cika! Ta riga mu gidan gaskiya.
Wannan mutuwa ta girgiza dukkan ma'aikata da marasa lafiya a asibitin. Abin da ya fi ban tausayi shi ne mahaifiyarta, wadda suke zaune suna hira da ita mintuna kalilan da s**a gabata, tana jiran zuwan likitan don a ba diyarta ruwa da tuwo, ashe kwananta ya ƙare.
Ya Salam! ta rayu kamar zakanya, mai juriya da jaruntaka, amma a yau gashi an rufe ta a cikin duhun ƙasa. Ubangiji Allah ya jifanci kurenki, ya yafe miki kurakuranki, ya ba mahaifiyarki da sauran iyali juriya da juriya kan wannan rashi.
Amin.
Nurse zainab Bashir
(Ummu Ammara)
31/05/2026
Honourable yace yaga zane kuma zane yayi kyau amma yace kar a sake wani. Yace idan kuma kasake wani saidai ku haɗu a kotu. 😂🧑🦯
30/05/2026
Wallahi ni mace ce amma sai da jikina yayi sanyi😥
Ina cikin scrolling naci karo da wannan post din saurayi da budurwa ne shekarar su 7 suna tare shine wannan content creator din ya gansu sai yake ce musu yana yin wani gwaji ne na relationship,,,, Shine ya ce mata zata iya sa wannan saurayin a Whatsapp status dinta with caption "The love of my life" akan kudi 200k Kai tsaye tace no🤔
Gayen nan was shocked 😱yace a maimaita mata tambayar,ta kara cewa no ko 1 million za'a bata bazata sa ba tace waye zai kula da sauran dawainiyarta???
Kunsan me? Gidan da take ciki shi ya kama,wayar da take hannunta shi ya siya,iyayenta shi yake dawainiya dasu 😓 yace ya watsar da nashi iyayen ya rungumi hidimar iyayenta🤔yace wata daya daya wuce 500k ya tura mata 😂 amma kunsan duk me take cewa nawa??nawa??nawa??? Duk abinda ya lissafan nan sai tace how much? Kwata kwata nawa ne??tace iya dubu 50 yake bata,50k fa👀 Amma ta raina🤣
To yanzu dai ta watse 💔ya kwace wayanshi da takalmin kafarta yace kuma zai kira iyayenta ayi ta ta kare😓ashe duk lokacin nan kawai yana datsawa kare ciyawa ne 😂
Maza gareku,ko zaku dinga yiwa mata hidima kada ku sake ku watsar da iyayen ku Saboda ko banza zaku dinga samun addu'a ga kuma lada,,kunga silar addu'ar nan idan Wanda kuke tare da ita ba macen kirki bace sai Kuga Allah ya raba ku da macuciya cikin salama👌
Amma wannan ba lada ba la'ada 😅 Abin tausayi abin dariya Wlh🤣😂 Allah ya kyauta
Zainab Abdulrahman ✍️
A gaskiya wasu matan basa kyautawa
Yau dai daya ina nayi furucin da ban tabayi akan yan uwa na mata ba
Miji ne ya hada solar a gidan sa dan ya dinga Jin dadin rayuwar sa da iyalin sa
Kawai sai matar tace ina so indinga siyar da pure water tunda unguwar nan bama samun Nepa
Yace kuma zakiyi ciniki sosai
Yaje ya siyo mata leda biyar duk aka gayawa yan unguwa ana saida ruwa cikin ikon Allah aka dinga zuwa ana siya
Baiwar Allahn nan tanata samun ciniki har yakai ya kawo ana siyarda Leda goma sama da haka a rana kuma fa solar sa ake kunnawa
Yanxu da aka fara zafi sai ake samun cinikin sosai sai mijin yace yanxu abinda ya kamata muyi
Solar nan mu daina kunnawa cikin dare karfe 9 da safe in kika kunna zuwa 4 ruwan yayi sanyi har dare zakiyi ta ciniki
Tunda ana zafi sai mu ringa kwana a tsakar gida mu kashe solar kar aiki yayiwa solar yawa yalalace dawori
Hmmm bada yini yake a gida ba iya dare yake dawowa kuma yace a kashe solar saboda tayi business da solar da safe Amma ya sadaukar da Jin dadin sa saboda farin cikin ta
Yace wlh ban taba tambayar ta yadda take da ribar ba ko sau daya ban taba cewa ta bani aron biyar ba
Yan uwana s**a zo yawon sallah bana nan zasu tafi s**a bugo min waya mace mata ta basu 2k idan na dawo zan bata
Tace babu nace to ta basu 500 su hau adaidaita su tafi gida tace itafa bayarwa ne bazatayi ba
Ba a wasa da kudin business
Shi kuma yace an daina anfani da solar sa wlh baza a kara kunna masa solar a saida ruwa ba saidai ta sai na ta solar
Shine ta tafi gidan su yaji jiya shi kuma yace ya Rantse da zatin Allah bazai je ba ko sun kirashi sai tayi wata2 a gidan su sannan zai je😞
Don Allah wai kun taba saving number wani ko wata da wani kalan suna ya gani kuka ji kunya? ya kuka yi? 😂
28/05/2026
Abokina CHIDI yaiwa ɗan uwansa kyautar ƙoda "Kidney" shekaru takwas baya wato a 2018. Bawai sayar masa ko rance ba, A'a kyauta ya sadaukarwa da ɗan uwan nasa ƙodarsa sakamakon tashi ta lalace bayan ɗimbin dialysis.
Anyi aikin asibitin koyarwa na jami'ar fatakwal wato (University of Port Harcourt Teaching Hospital), inda likitoci s**ai nasarar bude cikinsa tare da yanke ƙoda ɗaya lafiyayya, tare da sanyawa ɗan uwansa me suna EMEKA, domin ya tsira da rayuwarsa.
Lokacin tiyatar shekarun CHIDI 26 years old a duniya.
Haka ya shafe sati shida yana jinya shima bayan sadaukar da ƙodar kafin ya gama murmurewa, wanda a lokacin ne kuma ya rasa aikinsa na LOGISTICS COMPANY saboda ya wuce ka'idar kwanakin da aka basa batare da dawowa bakin aiki ba sanadiyar jinya.
Don haka koda ya koma gida haka fafutuka ta dawo farko, saida ya kuma gino rayuwarsa daga farko, yai ta faɗi tashi wajen nema. A duk wannan yanayi bai taɓa danasani ko yai ƙorafin rasa aikinsa ba koda sau ɗaya, wajensa muhimmin abu shine ya zamto anyi nasarar aiki ɗan uwansa EMEKA ya sami lafiya, wannan yafi masa komi.
Allah da ikonsa kuwa anyi nasarar Dashen ƙodar da akaiwa EMEKA kuma ya sami lafiya sosai, tamkar bai taɓa ciwo ba. Wanda zuwa shekarar 2020 wato shekaru biyu da yin tiyatar EMEKA ya kuma buɗe shagonsa na sayar da kayan ginegine wato building materials shop a unguwar Rumuola, Sannan zuwa shekarar 2022, kasuwancin EMEKA ya haɓɓaka yakai ga ya kuma buɗe manyan gurare biyu, sannan ya mallaki sabuwar motar hawa.
Hakazalik ya mallaki sabon gida wato muhalli a unguwar Ozuoba. Rayuwa tayi kyau, cigaba ta ko ina....domin gida kadai anan maganace ta ɗaruruwan milyoyin naira.
A gefe guda CHIDI na cike da farin ciki ganin yadda rayuwa taiwa dan uwansa kyawu duk da shi har yau buga-buga yake. Amma bai taɓa korafi ko yaji ba dadi ba, sai farin ciki, kuma bai taba zuwa don tambayarsa komi ba, shima ɗin a haka alhamdulillah tunda yana iya biyama kansa bukatu da abinda yake samu.
Sai de Allah da ikonsa a farkon wannan shekarar ta 2026 ne CHIDI ya fara fuskantar matsala ta matsanancin ciwon baya, amai da sauran su, wanda bayan gwaje-gwaje likitoci s**a tabbatar da ƙodarsa guda ɗaya data rage tana cikin halin matsi, sakamakon hawan jini, da stress na rayuwa, inda s**a tabbatar da bata lalace ba amma kwai buƙatar ayi aiki domin ceto ta kar a rasata, kuɗin aiki da magunguna Naira milyan ɗaya da dubu ɗari takwas wato estimated at ₦1.8 million.
CHIDI a lokacin gaba da baya Naira dubu ɗari uku da arba'in yake dasu ₦340,000 Don haka kai tsaye ya tafi wajen dannuwansa EMEKA ya samesa gida, yai masa bayanin halin da ake ciki.
in da EMEKA batare da tsawa, cin mutunci, baƙar magana ko hantara ba ya tarɓesa, ya zuba masa ruwa mai sanyi a cup ya sha...
“Sannan ya faɗamasa cewa; CHIDI ina godiya da dukkan abin da kai mun na sadaukarwa, Allah ya saka maka da alkhairi, I appreciate all you did for me. AMMA a yanzu nayi aure, ina da iyali kamar yadda kake gani, Mace ɗaya da yara uku, bazan iya saryar da farin cikin iyalina ba na dauki kuɗin da zan iya musu hidima suji daɗi ba na baka domin wannan buƙata, kurum mui addu'a Allah ya baka lafiya. Wato de I cannot destabilize my family for this. Let us pray about it.”
Sannan ya ɗauko dubu ashirin ₦20,000 ya miƙa masa tare da faɗin wannan shine iya taimakon da zan iya ma a yanzu.
CHIDI ya kirani a wannan dare yake mun bayani, Sam ba tare da kokawa ba, zagi ko tsinuwa ga EMEKA, Hasali cewa yai da bukata zata kuma tasowa zai qara masa abin da yai. He only said, “I would do it again.”
Magana ta gaskiya wannan abin ya baƙanta mun rai fiye da komi
A yanzu EMEKA na nan na gina katafaren shago na uku na kayan gini a yankin Rumuola, yayin da CHIDI ke cigaba da gwagwarmayar neman lafiya da iya abinda yake dashi, kuma yana cigaba da ɗaga kiran EMEKA a duk sanda ya kirasa a waya don gaishesa.
Wani aboki na kusa da CHIDI ne ke bada wannan labarin batare da saninsa ba.
Ban baku wannan labarin don ku yanke hukunci ba. Kurum tambaya ce guda ɗaya gareni:
Yayin da wani ya sadaukar maka da sassan jikinsa domin ceto rayuwarka, ME KAKE GANIN WANNAN MUTUMIN NA BINKA BASHI AKAI??
Fadin Allah ya saka masa da alkhairi kadai ban jin zai wadatar. Dole ka bashi wani matsayi na musamman.
Allah yasa mugama lafiya. Ya qara mana hakuri.
25/05/2026
A'a,ba fah tayi fah😆🤣
Kudi na zuwa.
Aure na zuwa.
Haihuwa na zuwa.
Lafiya na zuwa.
Kwanciyar hankali na zuwa.
Rufin asirin dindindin na zuwa.
Biyan bashin da ke kan ka na zuwa.
Ginin gidan kanka na zuwa.
Hutu da jin dadin iyayenka na zuwa.
Cikakkiyar nasara na zuwa.
In sha Allah...
Amma bayan duka wadannan... ina son ku sani kuma, mutuwa tana zuwa.
Saboda haka ita ma ku yi mata tanadi mai kyau.
Duk wannan fadi-tashin da muke yi, na gina rayuwar duniya ne wacce tana da iyaka. Babbar asara ita ce matashi ya wayi gari ya ci nasara a idon mutane, amma ya fadi a idon Mahaliccinsa.
Mu zubar da gumi mu nemi kudi don mu kare mutuncin mu da na iyalai, amma kada mu taba keta alfarmar addinin mu, ko ci da gumin wani don mu nemi duniya.
Karfin jikinka da kwakwalwarka na wucin gadi ne. Neman duniya kada ya hana ka Ibada, domin ita kadai ce ainihin jarin da zaka tafi da shi idan numfashin karshe ya zo.
UMAR ALIYU DAHIRU
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Telephone
Website
Address
Ɗorayi
Kano