11/09/2023
Labari: Roméo Lavia zai yi jinyar akalla makwanni shida saboda raunin da ya ji a idon sawun sa a atisayen makon jiya. Alamu na farko bayan gwaje-gwajensa sun nuna cewa Lavia ya sami rauni na ligament. [AdrianJKajumba]
© Wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Antony ya Kara bada sabon bayani game da halin da yake ciki.
"Na yi magana da Ingrid a WhatsApp. Lokacin da ta je Portugal don halartar bikin zagayowar ranar haihuwar dan uwanta, ta nemi da ta zo nan Manchester domin haduwa da ni, domin tana son haduwa da ni sosai, sannan ta tambaye ni shin ko na fi son jajayen kaya ko fari? Na sayi tikiti kuma na tanadar mata otal. Kuma tabbas na hadu da ita a otal din kuma mun yi haduwa ta kud da kud da yarda da juna."
"Bayan wannan haduwar, ta dage cewa mu sake haduwa saboda wasu abubuwan da aka tsara, ban sake ganinta ba tun daga wannan lokacin, yayin da ta koma Brazil. Tun daga nan ban sake haduwa da ita ba. Duk wadannan bayanan da na fada a yanzu babu shakka gaskiya ne, sun tabbata akwai su a cikin sakonnin WhatsApp, duk da cewa akwai abubuwa wadanda ban bayyana su ba don kare hakkin sirri. Zan samar da hanyoyin da s**a dace don tabbatar da rashin laifi na”.
©️ Wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Ga Barawo ga mai kaya.......
tsakeyar mako
11/09/2023
Tsohon kocin Mata na kasar Spain Jorge Vilda wanda aka kora ya bayyana burin sa na son horar da Real Madrid, kamar yadda ya fada wa Radio MARCA.
Real Madrid za ta nemi sabon koci a bazara mai zuwa, inda kwantiragin Carlo Ancelotti zai kare a karshen kakar wasa ta bana.
© Wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Vini yace inaaaa, ba za'a barshi a baya ba.. ya kuka ga wannan wankan?
©️ wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Romeo Lavia yana fatan buga wasansa na farko a Chelsea bayan hutun kasashen duniya.
Dan wasan tsakiyar Belgium ya samu rauni a idon sawunsa.
Ana sa ran Lavia zai kasance a cikin 'yan wasan da za su kara da Bournemouth a karshen mako mai zuwa, amma duk da haka har yanzu akwai shakku sosai.
© wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois na cigaba murmurewa cikin nasara, kamar yadda ya wallafa a shafin sa na Instagram.
©️ wasan tsakeyar mako
11/09/2023
Lamine Yamal: "Nico Williams ya bukace ni da in gode masa saboda taimakon da yayi min na zura kwallo. Ina fatan wannan ne farko kuma ina fatan in lashe kofuna da dama da wasanni da dama, na zura kwallaye da taimakawa ga tawagar kwallon kafar kasar gwargwadon iko."
© wasan tsakeyar mako