I dan baka isaba, isa da kanka

I dan baka isaba, isa da kanka

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from I dan baka isaba, isa da kanka, School Sports Team, kwana hudu layin mai mari, Kano.

Ganin yanda yan uwa mata ke kokarin fadar damuwowinsu privately ana ansamusu a wasu page din,muna gayyatar yan uwa maza ,suma su rubuto mana matsalar su ,zamu turawa yan uwa su basu sha warwari.

15/03/2026
27/09/2025

KARKA AIKATA ALKHAIRI DA ZIMMAR AMAIDA MAKA DA ALKHAIRI; BAI CIKA FARUWA BA

Umar Abdullahi Darmanawa primary Kano | 26-09-2025✍️

Kafin ka aikata kowanne irin Alkhairi ko taimako, ka san da wa'yannan abubuwa bisa yakini ne:

1. Akasarin wadanda Alkhairinka ya shafesu idan s**a tashi maida maka sak**ako, s**an maida sharri;

2. Akasari s**anyi zaton ai wannan Alkhairin da kayi musu damacan hakkin su ne na dole, saboda haka ba wata gwaninta kayi ba;

3. Akasarin jama'a s**an manta Alkhairi bakidayan sa tamkar ba'a taba yi musu shi ba;

4. Da zakayi wa jama'a Alkhairi kaso 99 cikin 100, to duk ranarda ka gaza arana ta 100n to sun manta 99 da kayi acan baya. Kusan dakai da wanda bai taba-yi ba duk daya;

5. Ana samun wadanda kayiwa Alkhairi su juye su koma makiyanka bayyanannu. Kiyayyar takan ninka na Makiyin da baka taba yiwa Alkhairin ba samsam;

6. Koda kasamu jarrabawa irin ta rayuwa (alal misali jinya, karayar-arziki da mak**antansu) akasarin wadanda kayiwa Alkhairi zasu guje ka, kafafuwansu na taba keyar su;

7. Anfi samun rama Alkhairi da Sharri daga wadannan mutane:
🔴 A. Yaron gida ga Ubangida na Kasuwa ko Ofis;
🔴 B. Maraya ga wanda ya raine shi;
🔴 C. Agola ga mijin uwarsa da ya girmar da shi;
🔴 D. Matar Aure da aka auro cikin Talauci, ta ci ta koshi ga Mijinta;
🔴 E. Yaran 'Yan Siyasa da s**a nunawa hanya wuyansu yayi kauri ga Iyayen Gidan;
🔴 F. Yaran Malamai ko Almajirai ga wanda ya soma dora musu baki;
🔴 G. Yaran Mawaka ga wadanda s**a fiddo su a idanun Duniya; da
🔴 H. Wanda ka bashi gida kyauta ya zauna.
Sai kadan cikin al'umma !

Ka lura da kyau ka tambayi kanka: akasarin wadanda kayiwa Alkhairi a rayuwa Alkhairin s**a maida maka ko sharri? 🤔

Ana samun masu maida Alkhairi da Alkhairi amma darussan rayuwa sun nuna sune kadan kwarai kwarai.
Idan ka zauna da manya da s**aga jiya da shekaranjiya zasu tabbatar maka da wannan.

Dan Adam yanada matukar Butulci da Manta Alkhairi musamman idan ya hadu da Hassada, Auratayya, 'Yan uwantaka da Makwabtaka.

Wa

17/09/2025

SHEKARUN FARKOFARKO NA TASHEN BALAGA GA YARANMU, ME YAKAMATA MUYI?

Gudunmowar Umar Abdullahi Darmanawa primary Kano
Kwanan-Wata: 17-09-2025

↪️ Daga lokacin da yara s**a kai matakin tashen balaga wato "Early Adolescence Stage" daga shekaru 12, 13, 15 zuwa 18, to wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga su yaran da iyayensu;

↪️ A lokacin ne yara suke zama Nagari ko Na-banza, masu amfanar da al'umma ko masu cutar da su;

↪️ Yara sun fi tasirantuwa da abokai ko kawaye fiye da malamai ko iyaye;

↪️ Yara suna jin daidai suke da kowa a duniya, kuma zasu iya yin komai k**ar yadda kowa yake yi;

↪️ A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon iyaye akansa. Yana son dakinsa daban, wajen kwanciyarsa daban, abinci daban, sutura daban, su aski da gyaran jiki sai wanda ransa yake so;

↪️ A lokacin ne yake jin karfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa;

↪️ A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga da zafin-kai, ba kan-gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tunaninsa). Idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi da ita;

↪️ A daidai wannan lokacin ne tsananin sha'awar ke sanya yaro ko yarinya su shiga layin Assha da Fasikanci idan ba dagaske akayi da kula da yawaita addu'a ba, musamman daga Iyaye ko masu kula dasu;

↪️ A daidai wannan lokacin, gaasa zata soma shiga ransa yadda zaiso yayi rayuwar jindadi irin ta sa'anninsa. Idan ba'ayi da gaske ba sai ya soma kokarin nemo kudi ta kowanne hali;

↪️ A daidai wannan lokaci, zai soma kokarin watsi da tsoffin abokai ya soma nemo sabbi wa'yanda ra'ayi yazo daya - nagari ko gurbatattu. Zai rage yawan zaman gida, yana yin nesa da unguwa inda aka saba ganinsa akai-akai.

MAFITA DA SHAWARWARI 👇

🔥1. Iyaye su ja 'ya'yansu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi musu gyara da tarbiyya. Su ninninka sanya musu idanu kwarai kwarai;

🔥 2. Sanya yaro ko yarinya a makarantar da ake karantar da boko da addini. Karatun Boko zalla babu na Addini shi yakesa mu cikin fadawa hannun shuwagabanni mar

24/08/2025

KO MUN LURA DA WANNAN? 🤔

Hannunka-Mai-Sanda:

Idan wani ya rasu a unguwarku ko akusa daku, ka lura sosai da yadda mu'amala take sauyawa tsakanin 'ya'yansa da abokansa na-kusa ko akasarin 'yan uwansa na jini cikin dan kankanin lokaci.
Sai kalilan kwarai kwarai cikin al'umma. Kalilan kwarai.

Ka sake sanya hankali da lura, kaga yadda ake janye jiki daga gidan da matarsa ko matansa suke yin takaba, da iyayensa da ake girmamawa lokacin da yake raye, musamman idan mamacin bai bar makudan kudade ba.

Anan zaka kara daukar wani sabon ilimi da darasin rayuwa da dalilan da s**a sa muka tsinci kawunanmu a halin da muke ciki ayanzu.

Har ila yau dai, wannan zai kara ankarar da kai da kake raye wanne mataki yak**ata ka daukarwa 'ya'yanka tun da wuri, inyaso kabarwa Allah sauran aikin kafin naka wa'adin ya cika.

Da akasarin wa'yanda s**a mutu zasu dawo su ga yadda wa'yanda suke kira abokansu s**ayi watsi da iyalinsu, mamaki kadai zai iya sa nantake su koma. Ko kuma akalla ba zasu sake yarda da kowa ba.

Yawayawan iyalan 'yan uwa, abokai da makwabta da s**a rasu, iyalansu suna cikin mawuyacin halin ha'ula'i da kaka-nikayi kuma basu iya roko da maula saboda gudun kada su zubda mutuncin gidansu da mahaifinsu da ya rasu.

Wasu, irin halin da suke shiga cikin dan kankanin lokaci bayan rasuwar mahaifinsu, dalilin juya musu baya da al'umma sukeyi saboda ba'a ganin idanunsa, abin ya munana. Da za'a gayawa mahaifin cewar iyalansa zasu shiga wannan halin bayan rasuwarsa, samsam ba zai yarda ba dalilin yardar da yayiwa abokansa da 'yan uwa.

💥 Daga ranar da wani ya rasu, abokinsa na kut-da-kut ba zai sake waiwayar halin da iyalansa suke ciki ba har abada. Wani, idan kaganshi agidan abokinsa da ya rasu, zawarcin matar abokin yaje.

Iyayen kuwa, ba zasu sake ganin keyar akasarin abokan 'ya:yansu da s**a rasu ba. Wani tun suna tuna shi har su manta k**annin sa.

Ko da mahaifinka bai rasu ba, kasamu zama da wa'yanda mahaifinsu yarasu, suyi maka karin bayani dangane da wannan maudu'in kasha

22/08/2025

INA ANINI?

Lawrence Nomanyagbon Anini ɗan fashin Najeriya ne wanda ya addabi birnin Benin a cikin shekarun 1980s. An k**a shi aka kashe shi saboda laifukan da ya aikata.

Anini ya zama mugun dan fashi da makami da ya addabi birnin Benin a Jihar Bendel (jihar Edo ta yanzu) ya kasance babban dan fashi da ake ganin ya gagari jami'in tsaro.

Shugaban Najeriya Janar Babangida lokacin da ya haya hau mulki a ranar 27 ga watan Agusta 1985, gwamnatinsa ta gaji lamarin rikicin Anini wanda gwamnatocin daya gada s**a kasa magancewa.

A safiyar ranar 2 ga watan Disamba 1986, shugaba Babangida yana shan shayi a fadar shugaban kasa da ke Dodan Barak a birnin leges (a lokacin ita ce fadar mulkin kasa). Sai ya tsinci wani labari da jaridar Concord ta buga wanda ke nuna cewa Anini da yaransa sunyi fashi a wani banki a birnin Benin har an kashe yansanda uku da wani ma'aikacin banki guda daya.

Nan take sai Babangida ya fusata, ya dauki wayar tarho ya bugawa Sufeto-Janar na yansanda na lokacin, marigayi Alhaji Muhammadu Gambo jimeta, yace maza maza yazo yana nemansa, yana zuwa sai Babangida yace da shi INA ANINI? Sai Inspector General ya k**a inda-inda. Sai Babangida yace, na baka awa 48 ko naga Anini a hannun jami'anka ko kuma kazo mini da takardar murabus (ajiye aiki) a hannun ka.

A ranar 3 ga Disamba, 1986, kwana daya da bayar da wannan umarnin na shugaban kasa, an k**a Anini a wani gida a cikin garin Benin a titin East Circular Road. A safiyar ranar 4 ga watan Disamba aka kai wa shugaban kasa jaridar The Guardian dauke da labarin an k**a Anini.

Shugaba Janar Ibrahim Babangida, ya bukaci a gaggauta yi masa shari'a. An samu Anini da mafi yawan tuhume-tuhumen da akayi masa, kuma an harbe shi a ranar 29 ga Maris, 1987 a birnin Benin.

08/08/2025

yawa;
👉 Mai wucewa ya soma yiwa wanda ya tarar (yana zaune ko yana tsaye);
👉 Wanda yake bisa abin-hawa - Dabba ko Mota ko mak**antansu, ya soma yiwa wanda yake tafiya da kafa.
Kamar yadda yazo cikin Ingantaccen Hadisi ruwayar Aba-Hurayrah (Allah ya kara yarda dashi):

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: "لِيُسَلِّمِ الصغيرُ على الكبيرِ، والمارُّ على القاعدِ، والقليلُ على الكثيرِ" وفي رواية: "والراكبُ على الماشي

(ii.) Idan kuma akasin haka ne, zabi yana gareka.

14. Ka kaucewa yawan neman rance ko bashi daga makwabcin zaman unguwa;

15. Kada ka bayyana matsalolin iyalinka ga makwabci sai idan ka tabbata mutum ne mai amana da fikira kwarai. Shi din ma sai Idan ya fuskanci hakan ne har yayi maka magana.Yin hakan zai haddasa maka tafiya tsirara koda da kaya a jikinka;

16. Duk iya shegen ka, ka rufawa kanka asiri da tinkarar 'ya'yan makwabta da shashanci. A mafi yawan lokuta asiri yakan tonu, da ba zai tsaya akanka kaikadai ba sai ya shafi martabar iyali, tabawa na har abada;

17. Ka yi taka-tsantsan da zama agidan da mamallakin gidan (Mace ko Namiji, amma musamman kuma Mace)yake zaune acikin gidan tareda kai. Kudi kake biya amma dole zaka zama baawa saboda yawa dokoki da tsari;

18. Idan akwai wakilin maigidan da kake zaune, (caretaker), ka tabbatar kudin hayarka yana isa ga maigida kai-tsaye, ko kuma akalla kake tura masa rasiti ko shaidar biya saboda halin rayuwa. Koda asalin mai gidan yana wata kasa ko wani gari nesa dakai, ka nemi hanyar yin magana da shi kaitsaye don ka kauce wa sharrukan mutumin-yau;

19. Duk tsarkin zuciyarka, ka dena yawan jan yaran mutanen unguwa a jikinka musamman kananan yara saboda gudun zargi;

20. Kakeyin taka-tsantsan wajen yiwa yaran mutanen unguwa fada koda sunyi ba daidai ba. Iyayen yanzu akasari bayin 'ya'yansu ne. Akan yiwa yaron wani fada don ya gyaru, wani har shari'a zakuyi dashi. Gwara a zageka cewar baka yiwa yaran mutane fada. Kaidai ka kula da naka;

21. Ka kauracewa "Ciyayyar Majalisa" kake cin abincinka agida

08/08/2025

MATAKAI 21 NA ZAMA DA MAKWABTAN ZAMANI LAFIYA A NIGERIA

Rubutu: Umar Darmanawa primary Kano
➡️ Kwanan Wata: 08-08-2025
➡️ Maudu'i: Zamantakewa

1. Idan ka koma sabon wuri ko kuma nace sabon matsuguni ko gida, yafi dacewa ka yi hakan da daddare, ba da rana ba. Hakan zai rage kaifin masu sanya idanu kan abinda babu ruwansu akanka. Hakan zaifi rufa sirrukanka saboda baka san hakikanin inda kake ba a matsayinka na bako awajen;

2. Idan kana zaune ne agidan haya, ya kasance kana biyan kudinka akan kari da zarar wa'adi ya cika. Hakan zai kara maka daraja, martaba da kima a idanun mai gida ko wakilansa;

3. Idan ka tare a sabon waje, zakaci karo da sabbin mutane, sabbin fuska. Wasu zasuke shisshige maka don suzama abokanka adaidai wannan lokacin. Kabi ahankali, kayi taka-tsantsan kwarai dasu. Ba'a saurin sakin jiki da mutumin-yau. Akwai korayen macizai cikin korayen ciyayi;

4. Idan mace ce ke, ki nisanci sabawa da gidan kitson cikin unguwa nan-da-nan. Akasari, gidajen kitson cikin unguwanni, nanne majalisar dinkin duniyar gulma da kisisina da munafurci. Anan ake dasa bama-baman dake tarwatsa aurarraki. Anan ake tona sirrukan matan unguwa da bankade-bankade. Sirrinki tsiraicinki. Idan kana da mata, ka gaggauta ja mata kunne akan hakan;

5. Kada ka saki jiki da kowanne makwabci fiye da kima, duk irin siffarsa ta Addini. Ba'a rubuta nagarta a gaban goshi. Ba'a gane gurgu a cikin mota;

6. Ma'aurata a guji tozarta juna a bainan-nasi, cikin jama’a duk yadda rai ya baci. Idan akwai abinda ba'aji dadinsa ba, a daure a tattauna shi cikin sirri ko a tafi caaaan wajen magabata amma ba'a cikin unguwa ba. Kada a tozarta juna agaban jama'ar unguwa daga baya ayi nadama idan zama bai kare ba. Magana zarar-bunu ce, idan har tafito bata komawa;

7. Kayi kaffa-kaffa da taka-tsantsan wajen saurin yarda da masu unguwa, limamai ko wa'yanda ake kira "Dattijan Unguwa" har sai kazama Dan-Gari acikin unguwar tukun. Ba duk abin dake kyalkyali bane zinari;

8. Idan a gidan yawa kuke, ko kuma kai

18/07/2025

WASU MATAKAN ZAMA LAFIYA DA MACE; MUSAMMAN MACE 'YAR AREWA

Rubutawa: Faruq Darmanawa Primary Kano 18-07-2025

1🌹
Tun ranar farko da kuka kasance ma'aurata, ka dauki nauyin rayuwarta yadda zaka iya dorewa da shi. Daga kasa, kakeyin sama, maimakon ka soma daga sama ka fado kasa.
Alal misali: idan kasan karfinka shine ka kashe muku N2K a yini, to kada ka kuskura ka haura N1. Haka abin yake a harkar sutura, muhalli, kayan ado da gyaran jiki da sauransu. Wataran sai a tafi har Miliyan Malala Gashin Tinkiya;

DALILI ⬇️
A dabi'ar akasarin mata, duk abinda kasoma dashi har ka sabar musu dashi s**a ginu akansa, daga ranarda ka dena ko kaja da-baya, a tunaninsu kadena kaunarsu ne kai-tsaye babu wani uzuri kuma komi zai iya faruwa. Maganin kada ayi, kada a fara;
_______

2🌹
Kada ka saba mata da tambayar 'Me K**e So?'
Kawai kake kawo abinda ya sawwaka;

DALILI ⬇️
Duk ranarda baka tambaye ta ba, wai kadena sonta ne kuma k**ar da wasa komi zai iya faruwa.
_______

3🌹
Kada ka kuskura kake musayar yawu da ita (ta fada, ka fada). Shine babban matakin farko na baiwa RAINI kofa har ya girma akasa shawo kansa. Ko kafita gaskiya, idan ka fada kaga alamar zata maida maka martani mara dadi, kayi shiru ka tashi kafita ka bar wajen ko gidan ka bar abin a ranka;
Idan kanason kada tayi maka gardama ko ja-inja, ka bari sai ranar da zata fita unguwa ko gidan biki ka tado da maganar; awannan lokacin duk abinda ka fada babu musu;

DALILI ⬇️
Duk girman yadda mace take da ja akan abu, zata iya Sallama idan zaka barta ta fita unguwa ta sha iskar waje.
_______

4🌹
Kada ka kuskura koda wasa kake bata labarin sabaninka da Iyayenka da sauran 'yan uwanka na jini;

DALILI ⬇️
Billahillazi Laa Ilaaha Illa Huwa k**ar yau ne, watarana sai ta goranta maka cewar Iyayenka da 'yan uwanka ma baka bari ba b***e ita.
_______

5🌹
Ka dena yarda tana yawan kawo maka korafin da ya shafi gidansu. Idan ta baci, cewa zatayi kai kake zuga ta koda baka taba cewa uffan ko ka goya mata baya ba. Idan ka goyi bayan 'yan u

15/07/2025

Alhaji Amadu Chanchangi (mai Cancangi Airlines)

An san Alhaji Amadu chanchangi a matsayin babban mai taimakon jama'a wanda ke sanya murmushi a fuskokin wadanda s**a ci karo da shi. Chanchangi wanda ya shahara wajen kafa kamfanin jirgin sama mai zaman kansa na biyu a Najeriya, wanda ya fito daga karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Kafa Kamfanin Chanchangi Airlines

A ranar 5 ga Janairu, 1994, ɗan kasuwan ya kafa kamfanin jirgin sama na Chanchangi. Kamfanin yana da hedikwatarsa a Kaduna. Ya zuwa Maris 2007, kamfanin jirgin yana da ma'aikata 780. A 2009, yana da jiragen sama shida.

Haka kuma ya samu lambar yabo ta hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayyar Najeriya (FAAN) da kuma lambar yabo ta ‘Corporate Merit Award’ na ‘Best Domestic Airline of the Year’ na shekarar 1998, 1999 da 2000.

Duk da cewa, ya samu nasara sosai, kamfanin jirgin ya fuskanci matsaloli shekaru biyu a wa’adi na biyu na mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

A ranar 10 ga watan Disamba, 2005, gwamnatin Obasanjo ta dakatar da kamfanin saboda rashin tsaro da ayyukansa, amma a ranar 22 ga watan Disamba na wannan shekarar ne kamfanin ya koma aiki. Tsakanin 2005 zuwa 2010, kamfanin jirgin ya rubuta wasu abubuwan da s**a faru da s**a kasance masa kalubale.

A shekarar 2012, kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines ya shigar da karar Chanchangi, inda ya ce yana bin kamfanin bashin biliyoyin nairori domin kula da lafiyar jiragensa. Kamfanin jirgin na Chanchangi ya kasa fitowa ya kare kansa daga tuhumar da ake masa.

Ya zuwa shekarar 2012, lokacin da kamfanin jirgin ya dakatar da aiki, jiragensa biyu ne kawai su ka rage.

Kamfanin jiragen na Chanchangi ya gudanar da zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen Najeriya. Wasu daga cikin abokan huddarsa su ne:

🔹️Majalisar Dinkin Duniya
🔸️Sojojin Najeriya
🔹️Kwamandan Sojoji & Staff College, Jaji
🔸️Makarantar horar da kwallon kafa ta Najeriya

Zargin Boko Haram

A shekarar 2011, wata mujalla ta zargi Chanchangi da daukar nauyin mayak

11/07/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Ibrahim Manaja, Sabiu Musa, Gass Boy, Kasir Abubakar, Mummadu Aliyu, Muhammad Umar, El Jashawēē Been Musa, Inusa Musa

09/07/2025

1. Man Zaitun
2. Mai na shafawa amma Vaseline.

YADDA ZA'A HADA

Da farko zaka debi man Vaseline din kadan a dan wani abu haka,sai ka zuba man Zaitun kadan akai sai ka juya sosai sannan ka shafa shi a gaban ka minti 15 kafin kwanciya.

Zakai uwar gida zatai mamaki kwarai.

LIKE AND SHARE.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kwana Hudu Layin Mai Mari
Kano
1410