05/05/2026
🏆 | Sha ƙundu Uban tafiya, Rigiji gabji - Uban kofin duk wani kofi na duniya!
Ba’a zuwa inda kake sai an’isa antaka matakai masu yawa, sai ƙungiyar mutum ta cika ta batse!🤤
Sai anyi shekara hudu cirrr za’a kara samun wata ƙungiya ta mallakeka.
Duk yadda ƙungiya takai a wajan kafa tarihi ko daukar kofuna, toh zata iya wayar gari babu ita a cikin tseran daukarka.
Muna sonka muna ji da kai wallahi, kofi daya tilo a duniyar nan!🤗
- Ko Jimina ta rame baza’a taba kiranta da Kaza ba.🤤
- Ko yanzu a soke gudanar da wannan kofin wallahi.🙂
- Ko yanzu kasuwa ta watse dan koli yaci riba.!🤓
Club World Cup💙
Mune Chelsea.
Mune Champoins Club World Cup.💎
✍️✍️
Ismail Attaysir
05/05/2026
🔵 | A wasanmu na jiya da Nottingham ya tara manyan baki kuma shaharru a fadin duniya.
Daga cikin Mahalarta kwallon wasan akwai:
- Shahararren dan kokawannan mai suna Khabib shima yazo.
- Coach din Tottenham na yanzu Roberto De Zerbi & Sam Jewell sun halarta.
- Coach din Portugal mai suna Roberto Martínez shima yana filin jiya.
- Tsohon Coach dinmu Thomas Tuchel da Enzo Maresca duk sun sami halarta.
- Gwarzon dan wasanmu Thiago Silva da kuma Jimmy Floyd Hasselbaink sun zo suma.
05/05/2026
🚨 Chelsea yanzu hanya daya ce tilo da ta rage mana wacca zamu iya samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a season mai zuwa🏆
Hanyar itace kamar haka:👇🏾
1️⃣ Idan ASTON VILLA ta lashe UEFA Europe League.
2️⃣ Bayan ta lashe UEFA Europe League kuma ta kare a matsayi na biyar a gasar Primier league.
3️⃣ Sannan dole ne CHELSEA taci wasanni biyu masu zuwa kuma ta kare a matsayi na shidda a gasar Primier league.
Wannan itace hanya kadai da zamu iya buga Champoins league a kakar wasa mai zuwa.👏
Allah ya bamu sa’a da Nasara.
05/05/2026
🚩 Jamie Carragher:
“Chelsea kulob ne da ya lalace gaba ɗaya. Abin yana da matuƙar ban mamaki, kuma matsalar tana fitowa ne daga sama (shugabanci).
A yau akwai manyan ‘yan wasa guda biyar ko shida a fili, amma duk da haka Nottingham Forest ta doke su da ‘yan ajinta na B.”
“Ƙasa da watanni 12 da s**a wuce, suna murƙushe Paris Saint-Germain.
Yanzu babu haɗin kai tsakanin ‘yan wasa da masu horarwa, haka kuma babu alaƙa tsakanin ‘yan wasa da magoya baya.”
Jamie Yafadi Gaskiya?
Tushe: 🔗 Sky Sports
05/05/2026
A jiya an hangi Enzo Maresca a filin wasa na Stamford bridge.
Maresca yashiga filin ne a matsayin wanda zai kalli wasa ne kawai ba'a matsayin wani babban bako ba
Wannan zuwan nashi me yake nufi kenan
Akwai alamar Enzo Maresca har yanzu yana son aikin horar da Chelsea 🧑🏫
04/05/2026
Dan Allah ku fada mana Gaskiya a hotunannan guda biyu.
Wadannan Bala-balai din duka ancisu, amma abin tambayar a hoton wacca Ball ce Ofside?
Hoton farko ko na biyu?😭
04/05/2026
Dan Allah Liam Delap wanne amfani yayiwa Chelsea?
Akansa aka bada Jackson ga Bayern München sannan da Tyrique George aka bada shi ga Everton.!
Na tabbata da ana sa Marc Guiu a Striker da yayi mana amfani fiye da Delap.
04/05/2026
🔵 | Dukda cewa munyi rashin nasara, amma fah gaskiya João Pedro yaci Ball iyaka Ball.🤯🤾🏽♂️🔥
Ball din da shi kansa bazai taba mantawa da ita ba, kuma maybe ta zama Goal mafi kyau a karshen kakar wasa a kungiyar Chelsea da kuma Primier baki daya (Goal of the season)
04/05/2026
🤦 Wato Akwai Matsala a Chelsea ba kadan kadan ba
04/05/2026
Zaidu Sunusi dan Arewacin Nigeria da Thiago Silva legend din Chelsea sunci lashe gasar Primier ta kasar Portugal tare da kungiyarsu FC Porto.🥳🏆
04/05/2026
| WASAN CHELSEA..
⚽️ FAFATAWA: Chelsea Vs Nottingham forest
🏆 MATSAYIN WASA: Primier League zagaye na 35.
📆 RANAR WASA: Yau Litinin, 4 ga watan May, 2026.
🕓 LOKACI: Karfe 3:00pm na yamma agogon Nigeria 🇳🇬 da Niger 🇳🇪.
🏟 FILIN WASA: Stamford Bridge.
🚩 ALKALIN WASA: Anthony Taylor
Allah ya bamu sa’a
03/05/2026
‼️🎙 John Terry ya yi kira ga Clearlake Capital da ta su sake dawo da Thomas Tuchel aikin Coaching bayan gasar World Cup.
A cikin hirar da akai da legend din yace:
🗣 "Ku saurara, na zauna a wannan Club din na tsawon rayuwata a matsayina na dan wasa kuma Captain, kuma ni babban magoyi ne. Ina gayawa Clearlake Capital kai tsaye: bayan gasar cin kofin duniya a dawo da Thomas Tuchel, babu wata-wata a dawo da mutuminnan kawai.
Tuchel yasan Chelsea, kuma yana son Club dinnan, jagora ne mai nasara. Ya lashe gasar zakarun Turai, kuma ya san ainihin ma'anar wannan bajon, zai shiga dakin sanya tufafi zai fitar da kyawun kowanne dan wasa, matashi ko tsoho, domin yana zabar manyan matsayi ne da kuma sha’awar hakan sosai.
Clearlake, kuna da albarkatu da aiki; yanzu ku nemo mutumin da ya dace, Kwarewa, tsima, da kuma shugabanci mai nasara, Ku dawo da Tuchel, mu dawo da wannan kungiyar zuwa inda ya dace, zuwa sama, abu ne mai sauki."