10/12/2023
SHAWARA KAUTA GA MATASANMU
Karka ganmu cikin sutura ka dauka siyasace take yimana, aa wallahi kasuwancin mune da addu,ar iyaye sai zagewa da mukai muna neman kudi wurjanjan kawai domin tsira da mutuncinmu
Siyasa muna yintane domin bada gudun mawa ga alumarmu amma ba dan kwadayin tsintar abinda ake yarwa a cikinta ba
Hakanne yasa gaduk wanda yasanmu ko yake rayuwa damu a sabgar siyasa yasan munada namu ra,ayin na kashin kanmu ba komai ake zuwa dashi muke karba ba musamman idan har ya sauka daga tsarin da muke gani akwai kuskure a cikinsa
Hakika ina alfarin da kasantuwata mai koyon siyasa domin na samu ilimi da dama a cikinta wanda koda na barta to zan iya dan bada labarin yadda take kodako kadanne
A karshe ina mai bawa Matasa shawara musamman wadanda suke da ra,ayin koyon siyasa, dasu k**a sana,a da gaske. hakan shine zai basu damar iya rike mutuncinsu ga kowa da iya kawar da kai daga abin hannun wasu yan siyasar, sannan hakan zaisa ka rage jin haushin wasu yan siyasar domin tunanin sunki taimakonka akan wata bukata ta kashin kanka
Sannan hakan shine zaisaka kaucewa makauniyar soyayya ga wasu jagororin siyasa musamman wadanda duniya take musu kallon ba damuwarsu alumma taci gaba ba damuwarsu shine su tsira su tara abin duniya dasu da iyalansu
Ya Allah ka albarkaci nemanmu ka bamu na halal aduk abinda zamuci da wanda zamusha da wanda zamusa a jikinmu
Barkanmu da Safiya โyan uwa๐
17/02/2023
20/11/2022
08/11/2022
29/08/2020
25/05/2020
27/04/2020
10/04/2020
06/01/2020
26/12/2019
16/09/2019