Labaran wasanni

Labaran wasanni

Share

domin zafafan labaran wasanni kui mana follow da like

05/05/2026

🚨 Rahotanni na cewa wata rubutun koke ko ince korafi (petition) ta yanar gizo da magoya bayan Real Madrid s**a sanya hannu domin a fitar da Kylian Mbappé daga kulob din ta sa samu goyan bayan mutane miliyan daya da dubu dari biyu 1.2.
Amma a kula — irin waɗannan petitions yawanci ba su da tasiri kai tsaye kan shawarar kulob, kuma sau da yawa ana samun su ne daga ɓangaren magoya baya masu fushi bayan sak**ako ko yanayi a wasa.

01/05/2026

✅🗣️ Luis Enrique kocan P.S.G yai magana kan yadda yake ɗaukar Kylian Mbappé k**ar kowane ɗan wasa a dressing room in anje halftime ko bayan an tashi wasa wajen yiwa 'yan wasa fasa lokacin da yake Paris Saint-Germain ⬇️
🗣️ Luis Enrique:
“Ba mu da wata falsafa ta barin Mbappé ya yi duk abin da yake so kawai ba batareda mun masa fada ba in yai kuskure.
A lokacin tsohuwar tsarin PSG, bamuci manyan kofuna ba… Babbar matsalar ‘yan wasa ita ce ana ɗaukar su k**ar wasu sarakuna.
Da zarar ya zura ƙwallaye, babu wanda zai iya masa magana. Sai ka ji ana cewa: ‘bayan Kowa yayi kokari a wasa inaga ba daidai bane ka ware wani tauraro ka fadi iya kokarinsa hakan ze fusata abokan wasansa’.
Taurari dole su zama abin koyi fiye da sauran 'yan wasa, k**ar Kylian. Yana bada misali, amma hakan ba yana nufin ba ya yin kuskure a wasa bane.
Idan ya yi wasa mara kyau, kocinsa zai iya gaya masa — kuma shi kansa ya san hakan.”
📌sun samu sabanine bayan Enrique ya tsawata masa, inda ya umarce shi da ya rika bin ɗan wasan baya na dama na abokan hamayya wato lamba biyu dan karbar kwallo yana temaka ma sauran abokan wasansa. 🔥

27/04/2026

🚨🔥 | Thierry Henry yace ko Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye dubu daya 1000! a tarihin kwallon kafa hakan baze sa ya zama shine wanda yafi kowa a tarihin kwallon kafa ba🤯
🎙️ Thierry Henry ya kara da cewa: “Majed Abdullah ya zura kwallaye dari biyar 500 a gasar Saudiyya, wanda ya fi na Diego Maradona da kuma nawa. amma hakan baya nufin ya fi mu duka dani da Maradona” 👀🔥
📊 Ra’ayi mai tayar da kura a duniyar kwallon kafa a yanzu kenan kar a manta shima messi ya k**a hanyar cin kwallo dubu daya!
Shin yawan kwallaye kadai ne zai sa dan wasa ya zama mafi girma a tarihin kwallon kafa? 🤔⚽

26/04/2026

😆 An cire Marc Guéhi ya fita daga zagaye na uku na FA Cup tare da Crystal Palace a wannan kakar…
Amma duk da haka, har yanzu yana iya taka leda a wasan ƙarshe final tareda Manchester City bayan ya chanja kungiya 🤣 ze buga final! 🤯🔥

26/04/2026

🚨 José Bordalás ya kai “haram ball” wani sabon mataki wato kwallon dirma dirma ko ince tsola tsola… 😳⬇️
Kungiyarsa ta Getafe CF ta zura ƙwallaye Ashirin da takwas 28 kacal a wasanni talatin da biyu 32 a La Liga — amma duk da haka suna matsayi na shida 6 a tebur! 😮🔥
Ga wasu abubuwan mamaki:
▪️ Sun ci wasanni 7 cikin 10 na ƙarshe
▪️ Ba su taɓa zura fiye da ƙwallaye biyu 2 ba a wasa ko ɗaya ba a wannan sizin din
▪️ Sun yi nasara da 1-0 sau huɗu
▪️ Sun sha kashi da 1-0 sau takwas
▪️ Sai Real Oviedo kaɗai ne na ƙasan tebur s**a zura kwallaye ƙasa da su
▪️ Kuma sai Real Madrid da FC Barcelona ne s**a fi su ƙanƙantar yawan ƙwallayen da aka zura musu
⚽️ Duk da ƙarancin ƙwallaye, tsaron su yanada ƙarfi sosai — kuma suna samun sak**ako mekyau sai dai kwallon nasu a ganina batada shaawar kallo tsola kwallo kawai suke ga duka!
Wannan dabara ce ko kuma sa’a? Me kuke tunani shin kwallon nasu tanada kyau kunajin dadin team dinku ta buga wasa da getafe ? ⬇️🔥

26/04/2026

🚨 Michael Olise ba kawai ƙwararren ɗan wasa ba ne a filin wasa, aa har ma yana da ASALI MAI BAN MAMAKI… 🤯🤯⬇️
Olise na da damar wakiltar ƙasashe da dama a ciki:
Akwai▪️ Ingila 🏴 – inda aka haife shi
▪️ Faransa 🇫🇷 – ta bangaren mahaifiyarsa ‘yar Faransa hade da asali a Aljeriya
▪️ Aljeriya 🇩🇿 – daga asalin mahaifiyarsa
▪️ Najeriya 🇳🇬 – ta bangaren mahaifinsa
▪️ Haiti 🇭🇹 – kuma yana da alaƙa ta bangaren mahaifiyarsa
Wato ƙasashe BIYAR da zai iya wakilta a matakin ƙasa! 🌍🔥
🗣️ Thierry Henry:
“Me yasa Michael Olise ya zaɓi Faransa maimakon Ingila? Saboda yana son buga wa Faransa. Wannan SHINE MAFARKINSA.” 🇫🇷✨
Ya taba bugawa Ingila da Faransa wasa a matakin yara, amma lokacin yanke hukuncin buga wa babbar ƙasa wasa ya zaɓi Faransa (Les Bleus). 🇫🇷
Kamar yadda ya zaɓi ƙasa da zuciya ɗaya, haka ma zaɓin kulob dinsa ya nuna BURINSA yake bi. Ya samu tayi daga manyan kulob na Premier League k**ar Manchester United, amma ya zaɓi Bayern Munich — kuma wannan shawara ta yi masa kyau sosai! 🔴🔥
Yanzu haka yana ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Bayern, yana nuna ƙwarewa, hangen nesa da kuma nutsuwa a lokacin matsin lamba. 💎🔥

26/04/2026

Marcus Rashford ya kusa lashe kofin lig nasa na farko a tarihin rayuwar kwallon kafarsa a Barcelona 🤯
Ya taimaka wa FC Barcelona a jiya ta hanyar zura ƙwallo, wanda ya ba su karin maki uku masu muhimmanci a La Liga tazara maki sha daya 11 points tsakaninsu da Na biyu Real Madrid 👏

23/04/2026

Real Madrid sun bazama wajen neman Kocha ya kuke gani in ya kasance sun bukaci sayen Arteta shin kuna ganin Arsenal zasu sayar kuwa 🤔?

22/04/2026

🚨 Antoine Griezmann zai bar Atlético Madrid ba tare da ya taɓa lashe babban kofin gida ba (domestic trophy)… ❌🏆🥺💔⬇️
A cikin shekaru goma 10 da ya yi a Atlético Madrid, Antoine Griezmann bai taɓa lashe manyan kofunan gida a La Liga ba:
❌ 0 La Liga
❌ 0 Copa del Rey
Abin mamaki, bai taɓa lashe kofin lig ba a duk aikinsa! 😳🏆❌
▶ 2019/20: Ya koma FC Barcelona daga Atlético
🏆 2020/21: Atlético Madrid ta lashe La Liga
▶ 2022/23: Ya dawo Atlético daga FC Barcelona
🏆 2022/23: FC Barcelona ta lashe La Liga
Zai bar Turai ba tare da ya taɓa lashe babban kofin lig na ƙasa ba tare da kowace ƙungiya a Turai! ❌🏆
Rashin Rabo! 💔

21/04/2026

🚨 A wani wasa da TSV 1860 Munich a watan Maris 1997, ɗan wasan gaba na VfB Stuttgart, Giovane Élber, ya samu katin gargadi (yellow card) a minti na 26 saboda zagin alkalin wasa. 😳⬇️
bayan an dawo half time, ya fito da bakinsa a rufe, ya manne bakin nasa da jan tape a bakinsa domin kada ya sake yin zagi.
Amma abin mamaki, a minti na 78, Giovane Élber ya bugi wani ɗan wasan Munich da gwiwar hannu, wanda ya sa aka ba shi katin gargadi na biyu (wato jan kati).
🤣🤣🤣

20/04/2026

🚨 A shekarar 1998, wani masoyin Real Sociedad mai suna Aitor Zabaleta ya rasa ransa bayan wasu magoya bayan Atlético Madrid (ultras) sun kai masa hari a wani mashaya a Madrid, yayin da yake ƙoƙarin kare budurwarsa.. 💔😞🕊️🙏⬇️
Bayan Real Sociedad ta doke Atlético Madrid ta lashe Copa del Rey 2026, Mikel Oyarzabal ya girmama shi ta hanyar ɗora riga mai suna Zabaleta a kan kofin da s**a ci athletic Madrid. 🏆💙
Haka kuma, magoya bayan Real Sociedad sun shirya wata tifo ta musamman domin tunawa da shi kafin wasan. 👏
ka tafi, amma ba zamu taɓa mantawa da kai ba! 🤍🕊️

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Nasarawa
Kaduna